M. SH 6

Babban Umarni

1 “Waɗannan su ne umarnai, da dokoki, da farillai waɗanda Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku domin ku kiyaye su a ƙasar da kuke hayewa zuwa ciki don ku mallake ta,

2 don ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku da ‘ya’yanku da jikokinku, ku kuma kiyaye dukan dokokinsa da umarnansa, waɗanda nake umartarku dukan kwanakinku don ku yi tsawon rai.

3 Don haka, ku ji, ya Isra’ilawa, ku lura, ku kiyaye su domin zaman lafiyarku, domin kuma ku riɓaɓɓanya ƙwarai a ƙasar da take mai yalwar abinci yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya alkawarta muku.

4 “Ku ji, ya Isra’ilawa, Ubangiji shi ne Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.

5 Sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya, da dukan ranku, da dukan ƙarfinku.

6 Waɗannan kalmomi da na umarce ku da su a yau, za su zauna a zuciyarku.

7 Sai ku koya wa ‘ya’yanku su da himma. Za ku haddace su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, da sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

8 Za ku ɗaura su a hannunku da goshinku don alama.

9 Za ku kuma rubuta su a madogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.”

Faɗakarwa a kan Rashin Biyayya

10 “Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da ya rantse wa kakanninku Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zai ba ku manyan birane masu kyau waɗanda ba ku ne kuka gina ba,

11 da gidaje cike da abubuwa masu kyau waɗanda ba ku ne kuka cika su ba, da rijiyoyi waɗanda ba ku ne kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun waɗanda ba ku ne kuka dasa ba. Sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi,

12 to, kada ku manta da Ubangiji wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.

13 Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Shi ne za ku bauta masa, ku rantse da sunansa.

14 Kada ku bi waɗansu alloli na al’umman da suke kewaye da ku,

15 gama Ubangiji Allahnku wanda yake zaune a tsakiyarku, mai kishi ne, don kada Ubangiji Allahnku ya husata, ya shafe ku daga duniya.

16 “Kada ku gwada Ubangiji Allahnku kamar yadda kuka yi a Masaha.

17 Sai ku himmantu ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, da farillansa, da dokokinsa waɗanda ya umarce ku da su.

18 Sai ku yi abin da yake daidai, da abin da yake mai kyau a gaban Ubangiji saboda lafiyarku, domin kuma ku shiga ku mallaki ƙasa mai kyau wadda Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku.

19 Zai kuwa kori maƙiyanku a gabanku kamar yadda ya alkawarta.

20 “Idan nan gaba ‘ya’yanku suka tambaye ku ma’anar maganarsa, da dokoki, da farillai, waɗanda Ubangiji Allahnmu ya umarce ku da su,

21 sai ku amsa wa ‘ya’yanku, ku ce, ‘Dā mu bayin Fir’auna ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji ya fisshe mu daga Masar da dantse mai iko.

22 A idonmu Ubangiji ya aikata manyan alamu masu banmamaki, da mu’ujizai gāba da Masarawa, da Fir’auna, da dukan gidansa.

23 Ya fisshe mu daga wurin, ya bi da mu zuwa ƙasar da ya alkawarta wa kakanninmu zai ba mu.

24 Ubangiji kuwa ya umarce mu mu kiyaye dukan waɗannan umarnai, mu kuma ji tsoron Ubangiji Allahnmu domin amfanin kanmu kullum, domin kuma mu wanzu kamar yadda muke a yau.

25 Idan mun lura, muka kiyaye waɗannan umarnai, muka aikata su kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, zai zama adalci a gare mu.’ ”