Dokoki Goma
1 Musa ya kirawo Isra’ilawa duka, ya ce musu, “Ya ku Isra’ilawa, ku ji dokoki da farillai waɗanda nake muku shelarsu a yau! Sai ku koye su, ku aikata su sosai.
2 Ubangiji Allahnmu ya yi alkawari da mu a Horeb.
3 Ba da kakanninmu ne Ubangiji ya yi wannan alkawari ba, amma da mu ne, mu duka waɗanda suke da rai a yau.
4 Ubangiji ya yi muku magana fuska da fuska bisa dutsen ta tsakiyar wuta.
5 Ni ne na tsaya a tsakanin Ubangiji da ku a lokacin don in faɗa muku maganar Ubangiji, gama kun ji tsoro saboda wutar, ba ku kuma hau dutsen ba.
“Ubangiji ya ce,
6 ‘Ni ne Ubangiji Allahnka wanda ya fisshe ka daga ƙasar Masar daga gidan bauta.
7 “ ‘Kada ka kasance da waɗansu gumaka, sai ni.
8 “ ‘Kada ka yi wa kanka gunki, ko wata siffar abin da yake a sama a bisa, ko siffar abin da yake a duniya a ƙasa, ko siffar abin da yake a cikin ruwa a ƙarƙashin ƙasa.
9 Kada ka yi musu sujada, ko ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, Allah mai kishi ne, nakan hukunta ‘ya’ya, da jikoki saboda laifin iyaye waɗanda suka ƙi ni.
10 Amma nakan nuna ƙauna ga dubbai waɗanda suke ƙaunata, suna kiyaye umarnaina.
11 “ ‘Kada ka rantse da sunan Ubangiji Allahnka a kan ƙarya, gama Ubangiji ba zai kuɓutar da wanda yake rantsewa da sunansa a kan ƙarya ba.
12 “ ‘Ka kiyaye ranar Asabar, ka riƙe ta da tsarki yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka.
13 Kwana shida za ka yi aikinka duka.
14 Amma rana ta bakwai ranar hutu ce ta Ubangiji Allahnka. A cikinta ba za ka yi kowane irin aiki ba, kai da ɗanka, da baranka, da baranyarka, da sanka, da jakinka, da kowace dabbar da kake da ita, da baƙon da yake zaune tare da kai, don barorinka mata da maza su ma su huta kamarka.
15 Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnka ya fisshe ka da dantse mai iko, mai ƙarfi. Domin haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabar.
16 “ ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka domin ka yi tsawon rai, ka sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
17 “ ‘Kada ka yi kisankai.
18 “ ‘Kada ka yi zina.
19 “ ‘Kada ka yi sata.
20 “ ‘Kada ka yi shaidar zur a kan maƙwabcinka.
21 “ ‘Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko barorinsa mata ko maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abu da yake na maƙwabcinka.’
22 “Ubangiji ya faɗa wa taron jama’arku waɗannan dokoki da murya mai ƙarfi ta tsakiyar wuta, da girgije, da duhu baƙi ƙirin. Ya rubuta su a bisa alluna biyu na dutse, ya ba ni, ba abin da ya ƙara.”
Mutane Suka Ji Tsoro
23 “Sa’ad da kuka ji murya tana fitowa daga duhu, harshen wuta kuma tana ci a bisa dutse, sai shugabannin kabilanku da dattawanku suka zo wurina,
24 suka ce, ‘Ga shi, Ubangiji Allahnmu ya bayyana mana ɗaukakarsa da girmansa, mun kuma ji muryarsa a tsakiyar wutar. Yau mun ga Allah ya yi magana da mutum, duk da haka ya rayu.
25 Don me za mu mutu yanzu? Gama wannan babbar wuta za ta cinye mu. Idan muka ci gaba da jin muryar Ubangiji Allahnmu, za mu mutu.
26 Akwai wani ɗan adam wanda ya taɓa jin muryar Allah, Allah Mai Rai yana magana ta tsakiyar wuta yadda muka ji, har ya rayu?
27 Kai, ka matsa kusa, ka ji dukan abin da Ubangiji Allahnmu zai faɗa, sa’an nan ka mayar mana da dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya faɗa maka. Za mu ji, mu kuma aikata.’
28 “Ubangiji kuwa ya ji maganarku wadda kuka yi mini, sai ya ce, ‘Na ji maganar da jama’an nan suka yi maka, abin da suka faɗa daidai ne.
29 Da ma kullum suna da irin wannan zuciya ta tsorona, da za su kiyaye dukan umarnaina, zai zama fa’ida gare su da ‘ya’yansu har abada.
30 Tafi, ka faɗa musu su koma cikin alfarwansu.
31 Amma kai ka tsaya nan a wurina don in faɗa maka dukan umarnai, da dokoki, da farillai, waɗanda za ka koya musu su kiyaye a ƙasar da nake ba su, su mallake ta.’
32 “Sai ku lura ku yi daidai bisa ga abin da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, kada ku kauce dama ko hagu.
33 Sai ku bi hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku don ku rayu, ku zauna lafiya, ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku mallaka.”