Musa Ya Jaddada wa Isra’ilawa Alkawarin Ubangiji a Horeb
1 Waɗannan su ne zantuttukan da Musa ya faɗa wa dukan Isra’ilawa a hayin Urdun cikin jejin Araba daura da Suf, tsakanin Faran, da Tofel, da Laban, da Hazerot, da Dizahab.
2 Tafiyar kwana goma sha ɗaya ne daga Horeb zuwa Kadesh-barneya, ta hanyar Dutsen Seyir.
3 A shekara ta arba’in, a rana ta fari ga watan goma sha ɗaya, Musa ya faɗa wa Isra’ilawa dukan abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa musu.
4 A lokacin kuwa ya riga ya ci Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda yake zaune a Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, wanda yake zaune a Ashtarot, da Edirai.
5 A hayin Urdun, cikin ƙasar Mowab, Musa ya yi niyya ya fassara waɗannan dokoki.
Ya ce,
6 “Ubangiji Allahnmu ya faɗa mana a Horeb, ya ce, ‘Daɗewarku a wannan dutse ta isa.
7 Ku tashi, ku yi gaba zuwa ƙasar duwatsun Amoriyawa, da dukan maƙwabtansu waɗanda suke a Araba. Ku shiga tuddai, da kwaruruka, da Negeb, da bakin bahar, da ƙasar Kan’aniyawa, da Lebanon, har zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis.
8 Duba, na sa ƙasar a gabanku, sai ku shiga ku mallake ta, ƙasa wadda na rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, cewa zan ba su, su da zuriyarsu a bayansu.’ ”
Sa shugabanni
9 “A wancan lokaci ne na yi magana, na ce, ‘Ba zan iya ɗaukar nawayarku ba,
10 gama Ubangiji ya riɓaɓɓanya ku, har yawanku ya kai kamar taurarin sama.
11 Ubangiji Allah na kakanninku ya riɓa yawanku har sau dubu, ya sa muku albarka yadda ya alkawarta muku!
12 Ƙaƙa ni kaɗai zan iya ɗaukar nawayarku da wahalarku da kuma faɗace-faɗacenku?
13 Ku zaɓi masu hikima, da masu ganewa daga cikin kabilanku, waɗanda suka saba da zaman jama’a, ni kuwa in sa su zama shugabanninku!’
14 Kuka amsa mini, kuka ce, ‘I, daidai ne kuwa mu bi shawaran nan da ka kawo mana.’
15 Don haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma’amala da jama’a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu dubu, waɗansu a kan ɗari ɗari, waɗansu a kan hamsin hamsin, waɗansu kuma a kan goma goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku.
16 “A wannan lokaci kuma na umarci shugabanninku na ce, ‘Ku yi adalci cikin shari’a tsakanin ‘yan’uwanku, tsakanin mutum da ɗan’uwansa, ko kuma da baren da yake zaune tare da shi.
17 Kada ku nuna bambanci cikin shari’a, ko babban mutum ne ko talaka, duka biyu za ku ji su. Kada ku ji tsoron fuskar mutum, gama shari’a ta Allah ce. In kuwa shari’a ta fi ƙarfinku, sai ku kawo ta wurina, ni kuwa zan yanke ta.’
18 A wancan lokaci na umarce ku da dukan abin da ya kamata ku yi.”
An Aiki ‘Yan Leƙen Asirin Ƙasa
19 “Sai muka tashi daga Horeb, muka ratsa babban jejin nan mai bantsoro wanda kuka gani a hanyarmu zuwa ƙasar tuddai ta Amoriyawa, kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, muka zo Kadesh-barneya.
20 Sa’an nan na faɗa muku cewa, ‘Kun iso ƙasar tuddai ta Amoriyawa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu.
21 Ga ƙasar a gabanku wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku haura ku mallake ta yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya faɗa muku. Kada ku ji tsoro ko ku firgita.’
22 “Sa’an nan sai dukanku kuka zo wurina, kuka ce, ‘Bari mu aika da mutane, su je su leƙo mana asirin ƙasar tukuna, domin su shawarce mu ta hanyar da za mu bi, da kuma irin biranen da za mu shiga.’
23 “Na ga al’amarin ya gamshe ni, saboda haka na ɗauki mutum goma sha biyu daga cikinku, mutum guda daga kowace kabila.
24 Mutanen kuwa suka kama hanya, suka tafi tuddai, suka kuma isa kwarin Eshkol, suka leƙo asirin ƙasar.
25 Da hannunsu suka ɗebo daga cikin amfanin ƙasar, suka gangaro mana da shi. Suka kuma faɗa mana cewa ƙasa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu, mai kyau ce.
26 “Amma kuka ƙi ku haura, kuka ƙi bin umarnin Ubangiji Allahnku.
27 Sai kuka yi ta gunaguni cikin alfarwanku, kuna cewa, ‘Ai, saboda Ubangiji ya ƙi mu, shi ya sa ya fisshe mu daga ƙasar Masar, don ya bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallaka mu.
28 Ta ƙaƙa za mu hau? Gama ‘yan’uwanmu sun narkar da zuciyarmu da cewa, mutanen sun fi mu girma, sun kuma fi mu ƙarfi. Biranensu kuma manya manya ne, da gine-gine masu tsayi ƙwarai. Har ma sun ga Anakawa a wurin.’
29 “Sai na ce muku, ‘Kada ku ji tsoronsu ko ku firgita.
30 Ubangiji Allahnku wanda yake tafiya tare da ku, shi kansa zai yi yaƙi dominku kamar yadda ya yi muku a Masar a kan idonku.
31 Kun ma ga yadda Ubangiji ya bi da ku cikin jeji kamar yadda mutum yakan bi da ɗansa, a dukan tafiyarku har zuwa wannan wuri.’
32 Amma ko da yake ya yi muku haka duk da haka ba ku dogara ga Ubangiji Allahnku ba.
33 Shi wanda ya bishe ku, ya nuna muku inda za ku yi zango. Da dare yakan nuna muku hanya da wuta, da rana kuma yakan bi da ku da girgije.”
Hukuncin Allah a kan Isra’ilawa
34 “Ubangiji kuwa ya ji maganganunku, sai ya yi fushi, ya rantse, ya ce,
35 ‘Daga cikin mutanen wannan muguwar tsara ba wanda zai ga ƙasan nan mai albarka wadda na rantse zan ba kakanninku,
36 sai dai Kalibu ɗan Yefunne, shi kaɗai ne zai gan ta. Zan ba shi da ‘ya’yansa ƙasar da ƙafarsa ta taka, gama shi ne ya bi Ubangiji sosai.’
37 Ubangiji ma ya yi fushi da ni sabili da ku, ya ce, ‘Har kai ma ba za ka shiga ba.
38 Baranka, Joshuwa ɗan Nun, shi ne zai shiga. Sai ka ƙarfafa masa zuciya gama shi ne zai bi da Isra’ilawa, har su amshi ƙasar, su gaje ta.’
39 “Sa’an nan Ubangiji ya ce wa dukanmu, ‘Amma ‘ya’yanku ƙanana waɗanda ba su san mugunta ko nagarta ba, waɗanda kuke tsammani za a kwashe su ganima, su ne za su shiga ƙasar. Ni Ubangiji zan ba su su mallake ta.
40 Amma ku, sai ku koma cikin jeji ta hanyar Bahar Maliya.’ ”
An Ci Isra’ilawa da Yaƙi a Horma
41 “Sa’an nan kuka amsa mini, kuka ce, ‘Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi. Za mu tafi mu yi yaƙi bisa ga faɗar Ubangiji Allahnmu.’ Sai kowannenku ya yi ɗamara ya ɗauki makaman yaƙinsa, kuka yi tsammani abu mai sauƙi ne ku shiga ƙasar tuddai.
42 “Amma Ubangiji ya ce mini in faɗa muku, kada ku tafi kada kuma ku yi yaƙi, gama ba ya tare da ku. Maƙiyanku za su kore ku.
43 Haka kuwa na faɗa muku, amma ba ku kasa kunne ba, kuka ƙi yin biyayya da umarnin Ubangiji. Sai kuka yi izgili, kuka hau cikin ƙasar tuddai.
44 Sai Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai suka fito da yawa kamar ƙudan zuma, suka taru a kanku suka bi ku, suka fatattaka ku a Seyir, har zuwa Horma.
45 Sai kuka koma, kuka yi kuka ga Ubangiji, amma Ubangiji bai ji kukanku ba, bai kuma kula da ku ba.
46 Kun kuwa zauna cikin Kadesh kwana da kwanaki, kamar dai yadda kuka yi.”