Tafe-tafe daga Masar zuwa Mowab
1 Waɗannan su ne wuraren da Isra’ilawa suka yi zango sa’ad da suka fita runduna runduna daga ƙasar Masar ta hannun Musa da Haruna.
2 Bisa ga faɗar Ubangiji, Musa ya rubuta wuraren tashinsu da wuraren saukarsu. Wuraren saukarsu da na tashinsu ke nan.
3 Sun tashi daga Ramases a rana ta goma sha biyar ga watan fari. A kashegarin Idin Ƙetarewa ne suka fita gabagaɗi a gaban dukan Masarawa.
4 Masarawa suna ta binne gawawwakin ‘ya’yan farinsu da Ubangiji ya karkashe musu. Banda ‘ya’yan farinsu kuma Ubangiji ya hukunta wa allolinsu.
5 Isra’ilawa kuwa suka tashi daga Ramases suka sauka a Sukkot.
6 Suka tashi daga Sukkot suka sauka a Etam wadda take a gefen jejin.
7 Da suka tashi daga Etam, sai suka juya zuwa Fi-hahirot wadda take gaban Ba’al-zefon suka sauka a gaban Migdol.
8 Da suka tashi daga gaban Fi-hahirot sai suka haye teku zuwa cikin jejin. Suka yi tafiya kwana uku a jejin Etam, suka sauka a Mara.
9 Suka tashi daga Mara suka zo Elim inda akwai maɓuɓɓugan ruwa guda goma sha biyu da itacen dabino guda saba’in. Sai suka sauka a can.
10 Suka tashi daga Elim, suka sauka a gefen Bahar Maliya.
11 Da suka tashi daga Bahar Maliya suka sauka a jejin Sin.
12 Suka tashi daga jejin Sin, suka sauka a Dofka.
13 Daga Dofka suka tafi Alush.
14 Suka tashi daga Alush suka sauka a Refidim inda mutane suka rasa ruwan sha.
15 Suka tashi daga Refidim suka sauka a jejin Sinai.
16 Da suka tashi daga jejin Sinai, sai suka sauka a Kibrot-hata’awa.
17 Suka tashi daga Kibrot-hata’awa suka sauka a Hazerot.
18 Da suka tashi daga Hazerot, sai suka sauka a Ritma.
19 Suka tashi daga Ritma suka sauka a Rimmon-farez.
20 Suka tashi daga Rimmon-farez, suka sauka a Libna.
21 Da suka tashi daga Libna, sai suka sauka a Rissa.
22 Da suka tashi daga Rissa, suka sauka a Kehelata.
23 Suka tashi daga Kehelata suka sauka a Dutsen Shifer.
24 Suka tashi daga Dutsen Shifer suka sauka a Harada.
25 Da suka tashi daga Harada, suka sauka a Makelot.
26 Suka tashi daga Makelot suka sauka a Tahat.
27 Suka tashi daga Tahat suka sauka a Tara.
28 Suka kama hanya daga Tara suka sauka a Mitka.
29 Suka kuma kama hanya daga Mitka suka sauka a Hashmona.
30 Daga Hashmona suka sauka a Moserot.
31 Da suka tashi daga Moserot suka sauka a Bene-ya’akan.
32 Suka tashi daga Bene-ya’akan suka sauka a Hor-hagidgad.
33 Da suka tashi daga Hor-hagidgad suka sauka a Yotbata.
34 Suka kama hanya daga Yotbata suka sauka a Abrona.
35 Da suka tashi daga Abrona, sai suka sauka a Eziyon-geber.
36 Suka tashi daga Eziyon-geber suka sauka a jejin Zin, wato Kadesh.
37 Da suka kama hanya daga Kadesh suka sauka a Dutsen Hor a kan iyakar ƙasar Edom.
38 Bisa ga umarnin Ubangiji, Haruna firist ya hau Dutsen Hor inda ya rasu a rana ta fari ga watan biyar a shekara ta arba’in ta fitowar jama’ar Isra’ila daga ƙasar Masar.
39 Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku sa’ad da ya rasu a Dutsen Hor.
40 Sai Sarkin Arad, Bakan’ane wanda yake zaune a Negeb, a ƙasar Kan’ana, ya ji zuwan Isra’ilawa.
41 Isra’ilawa kuma suka tashi daga Dutsen Hor, suka sauka a Zalmona.
42 Daga Zalamona suka sauka a Funon.
43 Da suka tashi daga Funon, sai suka sauka a Obot.
44 Suka kuma kama hanya daga Obot suka sauka a Abarim a karkarar Mowab.
45 Suka tashi daga nan suka sauka a Dibon-gad.
46 Suka tashi daga Dibon-gad suka sauka a Almon-diblatayim.
47 Da suka tashi daga Almon-diblatayim, suka sauka a duwatsun Abarim a gaban Nebo.
48 Daga duwatsun Abarim suka sauka a filayen Mowab kusa da Urdun daura da Yariko.
49 Suka sauka kusa da Urdun, suka kakkafa alfarwansu tun daga Betyeshimot har zuwa Abel-shittim, a filayen Mowab.
Umarni kafin su Haye Urdun
50 Sai Ubangiji ya yi magana da Musa a filayen Mowab kusa da Urdun, daura da Yariko, ya ce
51 ya faɗa wa jama’ar Isra’ila, “Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa ƙasar Kan’ana,
52 sai ku kori dukan mazaunan ƙasar daga gabanku ku rurrushe sassaƙaƙƙun duwatsunsu, da siffofinsu na zubi, da masujadansu.
53 Sa’an nan ku mallaki ƙasar, ku zauna a ciki,gama na ba ku ƙasar, ku mallake ta.
54 Za ku rarraba wa kanku gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar jefar kuri’a. Za ku ba babbar kabila babban rabo, ƙaramar kabila kuwa ku ba ta ƙaramin rabo. Inda duk kuri’a ta fāɗa wa mutum, nan ne zai zama wurinsa. Bisa ga kabilan kakanninku za ku gāji ƙasar.
55 Amma idan ba ku kori mazaunan ƙasar daga gabanku ba, to, waɗannan da kuka bari cikinta za su zama haki a idanunku, da ƙayayuwa a kwiyaɓunku. Za su yi ta wahalshe ku da yaƙi.
56 Idan ba ku kore su ba, zan lalatar daku kamar yadda na shirya lalatar da su.”