Yaƙin Jihadi da Madayanawa
1 Ubangiji ya ce wa Musa,
2 “Ka ɗaukar wa Isra’ilawa fansa a kan Madayanawa. Bayan ka yi wannan za ka mutu.”
3 Musa kuwa ya ce wa jama’a, “Ku sa mazajen da suke cikinku su yi shiri, su yi ɗamarar yaƙi, don su tafi su yi yaƙi da Madayanawa, su ɗaukar wa ubangiji fansa a kansu.
4 Sai ku aiki mutum dubu ɗaya daga kowace kabilar Isra’ila zuwa wurin yaƙi.”
5 Aka samo mutum dubu goma sha biyu (12,000) shiryayyu don yaƙi, daga cikin dubban Isra’ilawa, mutum dubu ɗaya daga kowace kabila.
6 Musa ya aike su zuwa yaƙi tare da Finehas, ɗan Ele’azara firist, da akwatin alkawari, da ƙahonin kiran yaƙi a hannun Finehas.
7 Suka yi yaƙi da Madayanawa suka kashe musu kowane namiji, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
8 Suka kashe har da sarakuna biyar na Madayanawa, da Ewi, da Rekem, da Zur, da Hur, da Reba. Suka kuma kashe Bal’amu ɗan Beyor.
9 Isra’ilawa suka kwashi mata da yaran Madayanawa bayi. Suka washe shanunsu, da tumakinsu da dukan dukiyarsu ganima.
10 Suka kuma ƙone dukan biranen zamansu da dukan san saninsu da wuta.
11 Da mutum da dabba sun kwashe su ganima.
12 Suka kawo bayin da ganimar a wurin Musa, da Ele’azara firist, da taron jama’ar Isra’ila a zango a filayen Mowab a Kogin Urdun daura da Yariko.
Sojoji Sun Komo
13 Sai Musa da Ele’azara firist, da shugabannin taron jama’ar Isra’ila suka fita zango su tarye su.
14 Musa kuwa ya husata da shugabannin sojoji waɗanda suke shugabannin dubu dubu da shugabannin ɗari ɗari, waɗanda suka dawo daga wurin yaƙi.
15 Ya tambaye su ya ce, “Don me kuka bar dukan mata da rai?
16 Ku tuna fa, su ne, ta wurin shawarar Bal’amu, suka yaudari Isra’ilawa, suka saɓi Ubangiji cikin maƙidar Feyor, har annoba ta fasu a jama’ar Ubangiji.
17 Yanzu, sai ku kashe dukan yara maza da kowace mace wadda ta san namiji.
18 Amma dukan ‘yan mata da ba su san maza ba, sai ku bar wa kanku.
19 A cikinku duk wanda ya kashe mutum ko ya taɓa gawa, sai ya zauna a bayan zango kwana bakwai don ya tsarkake kansa tare da bayin a rana ta uku da ta bakwai.
20 Za ku tsarkake kowace riga, da kowane abu da aka yi da fata, da kowane kaya da aka yi da gashin awaki, da kowane abu da aka yi da itace.”
21 Ele’azara firist kuwa, ya ce wa sojojin da suka tafi yaƙi, “Waɗannan su ne ka’idodin da Ubangiji ya ba Musa.
22 Zinariya, da azurfa, da tagulla, da baƙin ƙarfe, da kuza, da darma,
23 da dukan abin da wuta ba ta ci ba, su ne za ku tsarkake su da wutar tsarkakewa, duk da haka za a kuma tsarkake shi da ruwa. Amma abin da wuta takan ci, sai a tsarkake shi da ruwa kawai.
24 Ku wanke tufafinku a rana ta bakwai don ku tsarkaka, bayan haka ku shiga zangon.”
Raba Ganima
25 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,
26 “Da kai, da Ele’azara firist, da shugabannin gidajen kakannin taron jama’a, ku lasafta yawan mutane, da dabbobin da aka kwaso ganima.
27 Ku kasa ganima kashi biyu, ku ba sojojin da suka tafi yaƙi kashi ɗaya, kashi ɗayan kuwa ku ba taron jama’ar.
28 Sai ka karɓi na Ubangiji daga cikin kashin ganimar da aka baiwa sojojin da suka tafi yaƙi. Ka ɗauki ɗaya daga cikin mutum ɗari biyar, da shanu ɗari biyar, da jakai ɗari biyar, da tumaki ɗari biyar.
29 Ka ba Ele’azara firist. Wannan hadaya ta ɗagawa ce ga Ubangiji.
30 Daga cikin rabin ganimar da aka ba Isra’ilawa, sai ka ɗauki ɗaya ɗaya daga cikin mutum hamsin, da shanu hamsin,da jakai hamsin, da tumaki hamsin, da dukan dabbobin. Ka ba da su ga Lawiyawa waɗanda suke lura da alfarwar sujada ta Ubangiji.”
31 Musa da Ele’azara firist, suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.
32 Yawan ganimar da sojoji suka kawo ke nan, tumaki dubu ɗari shida da dubu saba’in da dubu biyar (675,000),
33 shanu dubu saba’in da dubu biyu (72,000),
34 jakai dubu sittin da dubu ɗaya (61,000),
35 ‘yan mata dubu talatin da dubu biyu (32,000) waɗanda ba su san namiji ba.
36 Kashin da aka ba sojoji waɗanda suka tafi yaƙi ne nan, tumaki dubu ɗari uku da talatin da bakwai da ɗari biyar (337,500).
37 Daga ciki aka fitar da tumaki ɗari shida da saba’in da biyar domin Ubangiji.
38 Shanu kuma dubu talatin da dubu shida (36,000), daga ciki aka fitar da shanu saba’in da biyu domin Ubangiji.
39 Jakai dubu talatin da ɗari biyar (30,500), daga ciki aka fitar da jakai sittin da ɗaya domin Ubangiji.
40 ‘Yan mata dubu goma sha shida (16,000), daga ciki aka fitar da ‘yan mata talatin da biyu domin Ubangiji.
41 Sai Musa ya ba Ele’azara firist rabon Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
42 Wannan shi ne kashin da aka ba jama’ar Isra’ila cikin kashin da aka ware daga na waɗanda suka tafi yaƙin.
43 Tumaki dubu ɗari uku da talatin da bakwai da ɗari bayar (337,500),
44 shanu dubu talatin da dubu shida (36,000),
45 jakai dubu talatin da ɗari biyar (30,500),
46 ‘yan mata dubu goma sha shida (16,000).
47 Daga rabin kashi na jama’ar Isra’ila, Musa ya ɗauki ɗaya daga cikin hamsin na ‘yan mata, da na dabbobi, ya ba Lawiyawan da suke lura da alfarwar sujada ta Ubangiji kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
48 Sai shugabannin da suka shugabanci rundunar yaƙin, suka zo wurin Musa.
49 Suka ce masa, “Mu barorinka mun ƙidaya mayaƙan da suke ƙarƙashin ikonmu, ba wanda ya ɓace daga cikinmu.
50 Mun kuwa kawo wa Ubangiji hadaya daga cikin abubuwan da kowannenmu ya samu, kayan ado na zinariya, da mundaye, da ƙawane da ‘yan kunne, da duwatsun wuya, don yi wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.”
51 Musa da Ele’azara firist, suka karɓi zinariya da kayan adon duka.
52 Dukan zinariya da shugabanni suka bayar hadaya ga Ubangiji, nauyinta ya kai shekel dubu goma sha shida da ɗari bakwai da hamsin (16,750).
53 Kowane soja ya kwashi ganimarsa.
54 Musa da Ele’azara firist kuwa, suka karɓi zinariya da shugabanni suka bayar, suka kai su cikin alfarwa ta sujada don ta zama abin tunawa da jama’ar Isra’ila a gaban Ubangiji.