1 BIT 5

Ku Yi Kiwon Garken Allah

1 Don haka, ku dattawan ikkilisiya da suke cikinku, ni da nike dattijon ikkilisiya, ɗan’uwanku, mashaidin shan wuyar Almasihu, mai samun rabo kuma a cikin ɗaukakar da za a bayyana, ina yi muku gargaɗi,

2 ku yi kiwon garken Allah da yake tare da ku, ba a kan tilas ba, sai dai a kan yarda, ba ma don neman ribar banza ba, sai dai da himma.

3 Kada ku nuna wa waɗanda suke hannunku iko, sai dai ku zama abin koyi ga garken nan.

4 Sa’ad da kuma Sarkin Makiyaya ya bayyana, za ku sami kambin ɗaukaka marar dusashewa.

5 Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali’u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali’u alheri.”

6 Don haka, sai dai ku ƙasƙantar da kanku ga maɗaukakin ikon Allah, domin ya ɗaukakaku a kan kari.

7 Ku jibga masa dukan taraddadinku, domin yana kula da ku.

8 Ku natsu, ku kuma zauna a faɗake. Magabcinku Iblis yana zazzāgawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lanƙwame.

9 Ku yi tsayayya da shi, kuna dagewa a kan bangaskiyarku, da yake kun san ‘yan’uwanku a duniya duka an ɗora musu irin wannan shan wuya.

10 Bayan kun sha wuya kuma ta ɗan lokaci kaɗan, Allah mai alheri duka, wanda ya kira ku ga samun madawwamiyar ɗaukakarsa a cikin Almasihu, shi kansa zai kammala ku, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku.

11 Mulki yā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!

Gaisuwa

12 Na rubuto muku wasiƙar nan a taƙaice ta hannun Sila, ɗan’uwa mai aminci, a yadda na ɗauke shi, domin in yi muku gargaɗi, in kuma sanar da ku, cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske, ku tsaya a gare shi da ƙarfi.

13 Ita da take a Babila, wadda ita ma zaɓaɓɓiya ce, ta aiko muku da gaisuwa. Haka kuma, ɗana, Markus.

14 Ku gai da juna da sumbar ƙauna.

Salama tă tabbata a gare ku duka, ku na Almasihu.