1 KOR 11

1 Ku yi koyi da ni kamar yadda nake koyi da Almasihu.

Mata su Rufe Kansu

2 Ina yaba muku ne don kuna tunawa da ni a cikin kowace harka, kuna kuma riƙe ka’idodin nan da kyau, daidai yadda na ba ku.

3 Amma fa ina so ku fahimci cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace kuwa mijinta ne, shugaban Almasihu kuma Allah ne.

4 Duk mutumin da ya yi addu’a ko ya yi annabci kansa a rufe, ya wulakanta shugabansa ke nan.

5 Amma duk matar da ta yi addu’a, ko ta yi annabci da kanta a buɗe, ta wulakanta shugabanta ke nan, duk ɗaya ne da an aske kanta ma.

6 In mace ta ƙi rufe kanta, to, sai ta sausaye gashinta. In kuwa abin kunya ne a yi wa mace sausaye ko kundumi, to, sai ta rufe kanta.

7 Namiji kam, bai kamata yă rufe kansa ba, tun da yake shi kamannin Allah ne, abin alfahari ga Allah kuma. Amma mace abar taƙamar namiji ce.

8 (Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba, amma matar daga jikin namiji take.

9 Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.)

10 Shi ya sa ya kamata mace ta rufe kanta, wato, alamar ikon namiji, saboda mala’iku.

11 Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba.

12 Wato, kamar yadda mace take daga namiji, haka namiji kuma haihuwar mace ne. Amma dukkan abubuwa daga Allah suke.

13 Ku kanku ku duba fa ku gani. Ya dace da mace ke nan ta yi addu’a ga Allah da kanta a buɗe?

14 Ashe, ko ɗabi’a ma ba ta nuna muku cewa namiji ya yi gizo, abin kunya ne ba?

15 In kuwa mace tana da gashi, ba alfarmarta ce ba? Gama don rufin kai ne aka yi mata gashin.

16 In kuwa wani yana da niyyar gardama, to, mu dai ba mu san wata al’ada ba, ikilisiyoyin Allah kuma haka.

Ƙasƙantar da Cin Jibin Ubangiji

17 A game da umarnin nan kuwa, ban yaba muku ba, taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin kirki ce.

18 To, da farko dai sa’ad da kuka taru, taron ikkilisiya, na ji har akwai rarrabuwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen.

19 Don lalle ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda suke amintattu a cikinku.

20 Ashe kuwa, in kun taru gu ɗaya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba!

21 Domin a wajen cin abinci, kowa yakan dukufa a kan akushinsa, ga wani yana jin yunwa, ga wani kuwa ya sha ya bugu.

22 A! Ba ku da gidajen da za ku ci ku sha a ciki ne? Ko kuwa kuna raina Ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma muzanta waɗanda ba su da kome? To, me zan ce muku? Yaba muku zan yi a kan wannan matsala? A’a, ba zan yaba muku ba.

Cin Jibin Ubangiji

23 Abin nan kuwa da na karɓa a gun Ubangiji, shi ne na ba ku, cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki gurasa,

24 bayan da ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya gutsuttsura, ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake saboda ku. Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni.”

25 Haka kuma bayan jibin, sai ya ɗauki ƙoƙo, ya ce, “Ƙoƙon nan na Sabon Alkawari ne, da aka tabbatar da shi da jinina. Ku yi haka duk a sa’ad da kuke sha, domin tunawa da ni.”

26 Wato, duk sa’ad da kuke cin gurasar nan, kuke kuma sha a ƙoƙon nan, kuma ayyana mutuwar Ubangiji ke nan, har sai ya dawo.

Cin Jibin Ubangiji da Rashin Cancanta

27 Saboda haka duk wanda ya ci gurasar nan, ko ya sha a ƙoƙon nan na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulakanta jikin Ubangiji da jininsa ke nan.

28 Sai dai kowa ya auna kansa, sa’an nan ya ci gurasar, ya kuma sha a ƙoƙon.

29 Kowa ya ci, ya kuma sha, ba tare da faɗaka da jikin Ubangiji ba, ya jawo wa kansa hukunci ke nan, ta wurin ci da sha da ya yi.

30 Shi ya sa da yawa daga cikinku suke da rashin lafiya da rashin ƙarfi, har ma waɗansu da dama suka yi barci.

31 Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za a hukunta mu ba.

32 In kuwa Ubangiji ne yake hukunta mu, to, muna horuwa ke nan, don kada a yanke mana hukunci tare da sauran duniya.

33 Saboda haka, ya ‘yan’uwana, in kuka taru don cin abinci, sai ku jiraci juna.

34 In kuwa wani yana jin yunwa, sai yă ci a gida, kada yă zamana taronku ya jawo muku hukunci. Batun sauran abubuwa kuwa, zan ba da umarni a kai sa’ad da na zo.