1 KOR 14

Harsuna da Annabci

1 Ku nace wa ƙauna, ku kuma himmantu ga neman bayebaye na ruhu, tun ba ma na yin annabci ba.

2 Duk wanda yake magana da wani harshe, ba da mutane yake magana ba, da Allah yake yi, ba kuwa wanda yake fahimtarsa, domin asirtattun al’amura yake ambato ta wurin Ruhu.

3 Wanda kuwa yake yin annabci, mutane yake yi wa magana domin yă inganta su, ya ƙarfafa su, yă ta’azantar da su.

4 Duk wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ingantawa. Mai yin annabci kuwa, ikkilisiya yake ingantawa.

5 To, ina so dukanku ku yi magana da waɗansu harsuna dabam, amma na fi so ku yi annabci. Wanda yake yin annabci, ya fi mai magana da waɗansu harsuna, sai ko in wani ya yi masa fassara, domin a inganta ikkilisiya.

6 To, ‘yan’uwa, in na zo muku ina magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani, ko ilimi, ko annabci, ko koyar da Maganar Allah ba?

7 In abubuwan nan marasa rai, kamar su sarewa da molo, muryarsu ba ta fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa?

8 In ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi?

9 Haka ma yake a gare ku. In kun yi magana da wani harshe, wanda ba a fahimta ba, yaya wani zai san abin da ake faɗa? Kun yi magana a banza ke nan!

10 Hakika akwai harsuna iri iri a duniya, ba kuwa wanda ba shi da ma’ana.

11 In kuwa ba na jin harshen, sai in zama bare ga mai maganar, mai maganar kuma ya zama bare a gare ni.

12 Haka ma yake a gare ku. Tun da yake kun ɗokanta da samun bayebaye na Ruhu, sai ku himmantu ku ba da ƙarfinku ga inganta ikkilisiya.

13 Saboda haka duk mai magana da wani harshe, sai yă yi addu’a a yi masa baiwar fassara.

14 In na yi addu’a da wani harshe, ruhuna ne yake addu’a, amma tunanina bai amfana kowa ba.

15 To, ƙaƙa ke nan? Zan yi addu’a da ruhuna, zan kuma yi a game da tunanina. Zan yi waƙar yabon Allah da ruhuna, zan yi a game da tunanina.

16 In ba haka ba, in ka gode wa Allah da ruhu kawai, ta yaya wanda yake jahili zai ce, “Amin,” a kan godiyar da kake yi, in bai san abin da kake faɗa ba?

17 Ko da yake ka gode wa Allah sosai, ai, ɗan’uwanka bai ƙaru da kome ba.

18 Na gode Allah ina magana da waɗansu harsuna fiye da ku duka.

19 Duk da haka dai a taron ikkilisiya na gwammace in faɗi kalmomi biyar a game da tunanina, domin in karantar da waɗansu, da in faɗi kalmomi dubu goma da wani harshe.

20 Ya ku ‘yan’uwa, kada ku yi hankali irin na yara, sai dai a wajen mugunta, ku yi halin jarirai, amma a wajen hankali ku yi dattako.

21 A rubuce yake a cikin littattafai masu tsarki cewa, “Zan yi magana da jama’an nan ta wurin mutane masu baƙin harsuna, da kuma ta harshen baƙi, duk da haka kuwa ba za su saurare ni ba, in ji Ubangiji.”

22 Wato, ashe, harsuna a kan alamu suke, ba ga masu ba da gaskiya ba, sai dai ga marasa ba da gaskiya. Annabci kuwa domin masu ba da gaskiya ne, ba don marasa ba da gaskiya ba.

23 Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da wani harshe dabam, waɗansu jahilai kuma ko marasa ba da gaskiya suka shigo, ashe, ba sai su ce kun ruɗe ba?

24 In kuwa kowa yana yin annabci, wani kuma marar ba da gaskiya ko jahili ya shigo, sai maganar kowa ta ratsa shi, ya kamu a ransa ta maganar kowa,

25 asiran zuciyarsa kuma su tonu. Ta haka sai ya fāɗi ya yi wa Allah sujada, yana cewa lalle Allah na cikinku.

A Yi Kome yadda Ya Dace, a Shirye

26 To, ƙaƙa abin yake ne, ‘yan’uwa? Duk sa’ad da kuka taru, wani yakan yi waƙar yabon Allah, wani kuma koyar da Maganar Allah, wani bayani, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Sai dai a yi kome don ingantawa.

27 In kuwa waɗansu za su yi magana da wani harshe, kada su fi mutum biyu, matuƙa uku, su ma kuwa bi da bi, wani kuma yă yi fassara.

28 In kuwa ba mai fassara, sai kowannensu yă yi shiru a cikin taron Ikkilisiya, yă yi wa Allah magana a zuci.

29 Masu yin annabci kuma, sai dai biyu ko uku su yi magana, saura kuwa su auna maganar.

30 In kuwa an yi wa wani wanda yake zaune wani bayani, sai na farkon nan mai magana yă yi shiru.

31 Dukanku kuna iya yin annabci da ɗaya ɗaya, har kowa yă koya, yă koma sami ƙarfafawa.

32 Annabawa suna sarrafa ruhohinsu na annabci,

33 domin Allah ba Allahn ruɗu ba ne, na salama ne.

Haka yake kuwa a duk ikilisyoyin tsarkaka.

34 Sai mata su yi shiru a cikin taron ikkilisiya, don ba a ba su izinin yin magana ba, sai dai su bi, kamar dai yadda Attaura ma ta ce.

35 In akwai wani abin da suke so su sani, to, sai su tambayi mazansu a gida, don abin kunya ne mace ta yi magana a cikin taron ikkilisiya.

36 A kanku ne maganar Allah ta fara, ko kuwa a gare ku kaɗai ta isa?

37 In wani yana zato shi annabi ne, ko kuwa mai wata baiwa ta ruhu, to, sai yă fahimta, abin nan da nake rubuto muku umarni ne na Ubangiji.

38 In kuwa wani ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi.

39 Saboda haka, ‘yan’uwa, sai ku himmantu ga samun baiwar yin annabci, kada kuma ku hana yin magana da waɗansu harsuna.

40 Sai dai a yi kome ta hanyar da ta dace, a shirye kuma.