1 KOR 3

Abokan Aiki na Allah

1 Amma ni, ‘yan’uwa, ban iya yi muku jawabi ba, kamar yadda nake yi wa mutanen da suke na ruhu, sai dai kamar yadda nake yi wa masu halin mutuntaka, kamar jarirai a cikin bin Almasihu.

2 Nono ne na shayar da ku, ba abinci mai tauri na ba ku ba, don ba ku isa ci ba a lokacin, ko a yanzu ma ba ku isa ba,

3 don har a yanzu ku masu halin mutuntaka ne. Muddin akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe, ku ba masu halin mutuntaka ba ne, kuna kuma aikata halin mutuntaka?

4 Don in wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afolos ne,” ashe, ba aikata halin mutuntaka kuke yi ba?

5 To, wane ne Afolos? wane ne Bulus kuma? Ashe, ba bayi ne kawai ba, waɗanda kuka ba da gaskiya ta wurinsu, ko wannensu kuwa gwargwadon abin da Ubangiji ya ba shi?

6 Ni na yi shuka, Afolos ya yi banruwa, amma Allah ne ya girmar.

7 Don haka da mai shukar, da mai banruwan, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, shi da ya girmar.

8 Da mai shukar, da mai banruwan, duk daidai suke, sai dai ko wanne zai sami tasa ladar gwargwadon wahalarsa,

9 gama mu abokan aiki ne na Allah, ku kuwa gona ce ta Allah, ginin Allah kuma.

10 Kamar gwanin magini, haka na sa harsashin gini, gwargwadon baiwar alherin da Allah ya yi mini, wani kuma yana ɗora gini a kai. Sai dai kowane mutum, yă lura da irin ginin da yake ɗorawa a kai.

11 Harsashin kam, ba wanda yake iya sa wani dabam da wanda aka riga aka sa, wato, Yesu Almasihu.

12 To, kowa ya yi ɗori da zinariya a kan harsashin nan, ko da azurfa, ko da duwatsun alfarma, ko da itace, ko da shuci, ko da kara,

13 ai, aikin kowane mutum zai bayyana, domin ranar nan za ta tona shi, gama za a bayyana ta da wuta, wutar kuwa za ta gwada aikin kowa a san irinsa.

14 In aikin da kowane mutum ya ɗora a kan harsashin nan ya tsira, to, zai sami sakamako.

15 In kuwa aikin wani ya ƙone, to, sai yă yi hasara, ko da yake shi da kansa zai tsira, amma kamar ya bi ta wuta ne.

16 Ashe, ba ku sani ku Haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma yana zaune a zuciyarku?

17 In wani ya ɓāta Haikalin Allah, Allah zai ɓāta shi. Gama Haikalin Allah tsattsarka ne, ku kanku Haikalinsa ne.

18 Kada kowa yă ruɗi kansa. In waninku ya zaci shi mai hikima ne, yadda duniya ta ɗauki hikima, sai yă mai da kansa marar hikima, domin ya sami zama mai hikima.

19 Gama hikimar duniyar nan wauta ce a gun Allah, domin a rubuce yake, “Yakan kama masu hikima da makircinsu.”

20 Har wa yau, “Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne.”

21 Saboda haka kada kowa yă yi fariya da ‘yan adam. Don kuwa kome naku ne,

22 ko Bulus, ko Afolos, ko Kefas, ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwan yanzu, ko da na gaba, ai, duk naku ne.

23 Ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne.