1 TAS 5

Ku Zauna a Faɗake don Zuwan Ubangiji

1 Amma ga zancen ainihin lokaci ko rana, ba lalle sai an rubuto muku kome ba.

2 Domin ku da kanku kun sani sarai, ranar Ubangiji za ta zo ne kamar ɓarawo da dare.

3 Lokacin da mutane suke cewa, “Muna zaman salama da zaman lafiya,” wuf; sai halaka ta auko musu, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba kuwa hanyar tsira.

4 Amma, ai, ba a cikin duhu kuke ba, ‘yan’uwa, har da ranar nan za ta mamaye ku kamar ɓarawo.

5 Domin duk mutanen haske kuke, na rana kuma. Mu ba na dare ko na duhu ba ne.

6 Ashe, saboda haka kada mu yi barci yadda waɗansu suke yi, sai dai mu zauna a faɗake, da natsuwa.

7 Don masu barci da daddare suke barci, masu sha su bugu ma da daddare suke sha su bugu.

8 Amma da yake mu na rana ne, sai mu natsu, muna saye da sulken bangaskiya da ƙauna, muna begen samun ceto, shi ne kuma kwalkwakinmu.

9 Allah bai ƙaddara mu ga fushinsa ba, sai dai ga samun ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu,

10 wanda ya mutu saboda mu, domin ko muna a raye, ko muna barci, mu zama muna tare da shi.

11 Saboda haka, sai ku ƙarfafa wa juna zuciya, kuna riƙa inganta juna, kamar dai yadda kuke yi.

Gargaɗi da kuma Gaisuwa

12 Amma muna roƙonku ‘yan’uwa, ku girmama masu fama da aiki a cikinku, wato waɗanda suke shugabanninku cikin Ubangiji, suke kuma yi muku gargaɗi.

13 Ku riƙe su da mutunci ƙwarai game da ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.

14 Muna kuma yi muku gargaɗi, ‘yan’uwa, ku tsawata wa malalata, ku ƙarfafa masu rarraunar zuciya, ku taimaki marasa tsayayyiyar zuciya, ku yi haƙuri da kowa da kowa.

15 Ku lura fa, kada kowa ya rama mugunta da mugunta. Sai dai kullum ku nace yi wa juna aiki nagari, da kuma dukkan mutane.

16 Ku riƙa yin farin ciki a kullum.

17 Ku riƙa yin addu’a ba fāsawa.

18 Ku godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu.

19 Kada ku danne maganar Ruhu.

20 Kada ku raina annabci,

21 sai dai ku jarraba kome, ku riƙi abin da yake nagari kankan.

22 Ku yi nesa da kowace irin mugunta.

23 Allah kansa, mai zartar da salama, yă tsarkake ku sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku ƙalau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

24 Wanda yake kiranku ɗin nan mai alkawari ne, zai kuwa zartar.

25 Ya ku ‘yan’uwa, ku yi mana addu’a.

26 Ku gai da dukkan ‘yan’uwa da tsattsarkar sumba.

27 Na gama ku da Ubangiji, a karanta wa dukkan ‘yan’uwa wasiƙar nan.

28 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.