1 TIM 2

Gargaɗi a kan Addu’a

1 Da farko dai ina gargaɗi, cewa a yi ta roƙon Allah, ana addu’a, ana godo, ana gode wa Allah saboda dukkan mutane,

2 da sarakuna da kuma duk waɗanda suke a manyan maƙamai, don mu zauna lafiya, rai a kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa.

3 Wannan kyakkyawan abu ne, kuma abin karɓa ne a gun Allah Mai Cetonmu,

4 wanda yake son dukkan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.

5 Domin Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya ne, a tsakanin Allah da mutane, Almasihu Yesu, mutum,

6 wanda ya ba da kansa fansa saboda kowa da kowa. An kuwa yi shaidar wannan a daidai lokacinsa.

7 Don haka ne aka sa ni mai wa’azi, da manzo kuma (gasikya nake faɗa, ba ƙarya ba), mai koya wa al’ummai al’amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.

8 Saboda haka, a kowane wuri ina so maza su yi addu’a, suna ɗaga hannuwa tsarkakakku, ba tare da fushi ko jayayya ba.

9 Mata kuma su riƙa sa tufafin da suka dace da su saboda kunya da kamunkai, ba adon kitso, ko kayan zinariya, ko lu’ulu’u, ko tufafi masu tsada ba,

10 sai dai su yi aiki nagari, yadda ya dace da mata masu bayyana shaidar ibadarsu.

11 Mace ta riƙa koyo da kawaici da matuƙar biyayya.

12 Ban yarda mace ta koyar, ko kuma ta yi iko da maza ba, sai dai ta zama shiru.

13 Ai, Adamu aka fara halitta, sa’an nan Hawwa’u.

14 Ba kuma Adamu aka yaudara ba, amma matar ce aka yaudara, har ta keta umarni.

15 Duk da haka kuwa, ta wurin haifar ‘ya’ya sai ta kai ga kammala, muddin ta nace wa bangaskiya, da ƙauna, da zama a tsarkake, da kuma kamunkai.