2 KOR 11

Bulus da Manzannin Ƙarya

1 Da ma a ce ku jure ‘yar wautata. Ku dai yi haƙuri da ni!

2 Ina kishi a kanku saboda Allah. Gama na bashe ku ga Almasihu, domin in miƙa ku kamar amarya tsattsarka ga makaɗaicin mijinta.

3 Amma ina tsoro kada yă zamana, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Almasihu.

4 Don in wani ya zo yana wa’azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa’azi, ko kuma in kun sami wani ruhu dabam da Ruhun da kuka samu, ko wata bishara dabam da wadda kuka yi na’am da ita, ashe, har kuna saurin yin na’am da irinsu ke nan!

5 A ganina ban kasa mafifitan manzannin nan da kome ba.

6 Ko da yake ni bāmi ne a wajen yin magana, a wajen sani kam, ba haka ba ne, mun kuwa bayyana wannan sarai ta kowace hanya a cikin dukan sha’aninmu da ku.

7 Ashe, laifi na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaukaka ku, wato, saboda na yi muku bisharar Allah a kyauta?

8 Waɗansu ikilisiyoyi na biyan hakkina, sai ka ce ina yi musu ƙwace domin in yi muku hidima.

9 Sa’ad da nake a wurinku kuma nake zaman rashi, ban nauyaya wa kowa ba, domin ‘yan’uwan da suka zo daga Makidoniya su ne suka biya mini bukata. Saboda haka, na ƙi nauyaya muku ta kowace hanya, ba kuwa zan nauyaya muku ba.

10 Albarkacin gaskiyar Almasihu da yake tare da ni, ba mai hana ni fahariyar nan tawa a lardin Akaya.

11 To, don me? Domin ba na ƙaunarku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku.

12 Abin da nake yi kuwa, shi zan riƙa yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su.

13 Irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, mayaudaran ma’aikata, suna mai da kansu kamar su manzannin Almasihu ne.

14 Ba abin mamaki ba ne kuwa, domin ko Shaiɗan ma da kansa, yakan mai da kansa kamar shi mala’ikan haske ne.

15 Don haka, ba abin mamaki ba ne in bayinsa ma sun mai da kansu kamar su bayi ne na aikin adalci. A ƙarshe za a saka musu gwargwadon ayyukansu.

Wahalar Bulus saboda Manzanci

16 Ina sāke faɗa, kada wani ya zaci ni wawa ne. In kuwa kun zaci haka nake, to, ku ji ni wawa ne, don ni ma in samu in taɓa ‘yar taƙama kaɗan.

17 Abin nan da nake faɗa fa, ba bisa ga umarnin Ubangiji nake faɗa ba, sai dai magana ce irin ta wawa, wadda yake yi gabagaɗi, yana fariya,

18 da yake mutane da yawa suna fariya irin ta ‘yan adam kawai, ni ma zan yi.

19 Ai, ku kam, hikimarku har ta kai ga jure wa wawaye da murna!

20 Don in wani ya sa ku bauta, kukan jure masa, ko ya yi muku ƙwace, ko ya more ku, ko ya nuna muka isa, ko kuwa ya mare ku.

21 Mu kam, saboda rauninmu, wane mu da yin haka!

Amma ta ko yaya wani yake ƙarfin halin yin fariya, ina magana a kan ni wawa ne fa! to, ni ma sai in yi.

22 In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra’ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka.

23 In su bayin Almasihu ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan ɗauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri iri.

24 Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu.

25 Sau uku aka bulale ni da tsumagu, sau ɗaya har aka jejjefe ni da dutse. Sau uku jirgi ya ragargaje ina ciki, na kwana na yini ruwan bahar yana tafiya da ni.

26 Na yi tafifiya da yawa, na sha hatsari a koguna , na sha hatsarin ‘yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a bahar, na kuma sha hatsarin ‘yan’uwa na ƙarya.

27 Na sha fama, na sha wuya, na sha rashin barci, na sha yunwa da ƙishirwa, sau da yawa na rasa abinci, na sha sanyi da huntanci.

28 Banda waɗansu abubuwa dabam kuma, kowace rana ina a matse da matsananciyar kula saboda dukan ikilisiyoyi.

29 Wane ne ya raunana da ban raunana ba? Wane ne aka sa tuntuɓe, ban ji zafin ba?

30 In ma lalle ne in yi gadara, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suke nuna raunanata.

31 Allahn Ubangiji Yesu, wato Ubansa, wanda ya yabo ya tabbata a gare shi har abada, ya sani ba ƙarya nake yi ba.

32 A Dimashƙu gwamnan da yake ƙarƙashin sarki Aretis ya tsare ƙofofin birnin Dimashƙu don ya kama ni,

33 amma sai aka zura ni a cikin babban kwando ta tagar garu, na kuɓuce masa.