2 TAS 2

Sarkin Tawaye

1 To, a game da komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma taruwarmu mu sadu da shi, muna roƙonku ‘yan’uwa,

2 kada ku yi saurin jijiguwa a zukatanku, ko kuwa hankalinku yă tashi, saboda faɗar wani ruhu, ko wani jawabi, ko wata wasiƙa a kan cewa daga gare mu suke, cewa ranar Ubangiji ta zo.

3 Kada ku yarda kowa yă yaudare ku ko ta halin ƙaƙa, domin wannan rana ba za ta zo ba, sai an yi fanɗarewar nan, sarkin tawaye kuma ya bayyana, wato, hallakakken nan.

4 Shi ne magabci, mai ɗaukaka kansa, yana gāba da duk abin da ya shafi sunan Allah, ko kuma wanda ake yi wa ibada. Har ma yakan zauna a Haikalin Allah, yana cewa, shi ne Allah.

5 Ashe, ba ku tuna ba, nakan gaya muku haka tun muna tare?

6 To, a yanzu dai kun san abin da yake tare shi, don kada ya bayyana kafin lokacinsa.

7 Ko a yanzu ma tawayen nan, wanda ba shi fahimtuwa, an fara shi, amma farawar abin da zai faru, sai an ɗauke wanda yake hana shi tukuna.

8 A sa’an nan ne fa sarkin tawayen zai bayyana, Ubangiji Yesu kuwa zai hallaka shi da hucin bakinsa, ya kuma shafe shi da bayyanarsa a ranar komowarsa.

9 Mai tawayen nan kuwa, zai zo ne bisa ga ikon Shaiɗan, yana aikata abubuwan al’ajabi, da alamu, da aikin dabo na ƙarya iri iri,

10 yana kuma yaudarar waɗanda suke a hanyar hallaka, muguwar yaudara, domin sun ƙi ƙaunar gaskiya har yadda za su sami ceto.

11 Saboda haka, Allah zai auko musu da wata babbar ɓatan basira don su gaskata ƙarya,

12 don duk a hukunta waɗanda suka ƙi gaskata gaskiya, suke kuma jin daɗin mugunta.

Ya Zaɓe Ku Ku Sami Ceto

13 Ya ku ‘yan’uwa, ƙaunatattun Ubangiji, lalle ne kullum mu gode wa Allah saboda ku, domin Allah ya zaɓe ku, don ku fara samun ceto ta wurin tsarkakewar Ruhu, da kuma amincewarku da gasikya.

14 Domin wannan maƙasudi ya kira ku, ta wurin bishararmu, domin ku sami ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

15 Saboda haka, ‘yan’uwa, sai ku dage, ku kuma riƙi ka’idodin da muka koya muku kankan, ko da baka ko ta wurin wasiƙa.

16 To, Ubangijinmu Yesu Almasihu kansa, da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu, ya kuma ba mu madawwamiyar ta’aziyya da kyakkyawan bege ta wurin alherinsa,

17 yă ta’azantar da ku, ya kuma ƙarfafa ku ga yin kowane kyakkyawan aiki da magana.