2 TIM 2

Amintaccen Sojan Almasihu

1 Saboda haka, ya kai ɗana, sai ka ƙarfafa da alherin da yake ga Almasihu Yesu.

2 Abin da ka ji a guna a gaban shaidu masu yawa kuwa, sai ka danƙa wa amintattun mutane, waɗanda su ma za su koya wa waɗansu.

3 Kai kuma ka jure wa shan wuya, kana amintaccen sojan Almasihu Yesu.

4 Ai, ba sojan da yake a bakin dāga da ransa zai sarƙafe da sha’anin duniya, tun da yake burinsa shi ne yă faranta wa wanda ya ɗauke shi soja.

5 Mai wasan guje-guje da tsalle-tsalle, ba zai sami ɗaukaka ba, sai ko ya bi dokokin wasan.

6 Ma’aikaci, ai, shi ya kamata yă fara cin amfanin gonar.

7 Ka yi tunani a kan abin da nake faɗa, Ubangiji kuwa zai ba ka fahimtar kome.

8 Ka tuna da Yesu Almasihu fa, shi da aka tashe shi daga matattu, na zuriyar Dawuda bisa ga bisharata,

9 wadda nake shan wuya saboda ita, har nake ɗaure kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a ɗaure take ba.

10 Don haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton nan da yake samuwa ta wurin Almasihu, a game da madawwamiyar ɗaukaka.

11 Maganar nan tabbatacciya ce,

“In mun mutu tare da shi, za mu rayu ma tare da shi,

12 In mun jure, za mu yi mulki ma tare da shi,

In mun yi musun saninsa, shi ma zai yi musun saninmu,

13 In ba mu da aminci, shi kam ya tabbata mai aminci,

Domin ba zai yi musun kansa ba.”

Yardajjen Ma’aikaci

14 Ka riƙa tuna musu da haka, ka kuma gama su da Ubangiji, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi.

15 Ka himmantu, ka miƙa kanka yardajje ga Allah, ma’aikaci wanda ba hanya ya kunyata, mai kuma fassara Maganar gaskiya daidai.

16 Ka yi nesa da masu maganganun banza na sāɓo. Sai daɗa jan mutane zuwa ga rashin bin Allah suke yi,

17 maganarsu takan haɓaka kamar gyambo. A cikinsu har da Himinayas da Filitas,

18 waɗanda suka bauɗe wa gaskiya suna cewa tashin matattu ya riga ya wuce, suna jirkitar da bangaskiyar waɗansu.

19 Duk da haka, ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikata mugunta.”

20 A babban gida, ba kayan zinariya da na azurfa ne kawai ba, har ma da na itace da na yumɓu, waɗansu don aikin ɗaukaka, waɗansu kuwa don ƙasƙantaccen aiki.

21 Kowa yă tsarkake kansa daga ayyukan nan ƙasƙantattu, zai zama ma’aikaci mai daraja, tsarkakakke, mai amfani ga Ubangiji, shiryayye ga kowane kyakkyawan aiki.

22 Don haka, sai ka guje wa mugayen sha’awace-sha’awacen ƙuruciya, ka dimanci aikin adalci, da bangaskiya, da ƙauna, da kuma salama, tare da waɗanda suke roƙon Ubangiji da zuciya tsarkakakkiya.

23 Ka ƙi gardandamin banza marasa ma’ana, ka san lalle suna jawo husuma.

24 Bawan Ubangiji kuwa lalle ba zai zama mai husuma ba, sai dai ya zama salihi ga kowa, gwanin koyarwa, mai haƙuri,

25 mai sa abokan hamayyarsa a kan hanya da tawali’u, ko Allah zai sa su tuba, su kai ga sanin gaskiya,

26 su kuɓuce wa tarkon Iblis, su bi nufin Allah, bayan da Iblis ya tsare su.