2 TIM 4

1 Na gama ka da Allah, da kuma Almasihu Yesu, wanɗa zai yi wa rayayyu da matattu shari’a, na kuma gargaɗe ka saboda bayyanarsa da kuma mulkinsa,

2 ka yi wa’azin Maganar Allah, ka dimanta a kai ko da yaushe, kana shawo kan mutane, kana tsawatarwa, kana ƙarfafa zukata, a game da matuƙar haƙuri da kuma koyarwa.

3 Don lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu yana ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu.

4 Za su toshe kunnensu ga jin tatsuniyoyi.

5 Kai kuwa, sai ka natsu a cikin kowane hali, ka jure wa shan wuya, kana aikin mai bishara, ka cika hidimarka.

6 Ni fa tsiyaye ni ake yi kamar hadaya, lokacin ƙauracewata kuma ya gabato.

7 Na sha fama, famar gaske, na gama tseren, na riƙe bangaskiya.

8 Saura kuwa, sai sakamakon nan na aikin adalci, da aka tanadar mini, wanda Ubangiji, mahukunci mai adalci, zai ba ni a ranar nan, ba kuwa ni kaɗai ba, har da duk waɗanda suke ɗokin ganin bayyanarsa.

Waɗansu Umarnai

9 Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo wurina da hanzari,

10 domin Dimas, saboda ƙaunar duniyar nan, ya yashe ni, ya tafi Tasalonika. Karaska ya tafi ƙasar Galatiya, Titus kuma ya tafi ƙasar Dalmatiya.

11 Luka ne kaɗai yake tare da ni. Ka ɗauko Markus ku zo tare, gama yana da amfani a gare ni a wajen yi mini hidima.

12 Tikikus kuwa na aike shi Afisa.

13 Sa’ad da za ka taho, ka zo da alkyabbar nan da na bari a wurin Karbus a Taruwasa, da kuma littattafan nan, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba.

14 Iskandari maƙerin farfarun nan ya yi mini mugunta ƙwarai, Ubangiji zai yi masa sakayyar aikinsa.

15 Kai ma, ka mai da hankali da shi, gama ya hauri maganarmu, mummunan hauri.

16 A lokacin da na ba da hanzarina na farko, ba wanda ya goyi bayana, sai duk suka yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba.

17 Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya ba ni ƙarfin sanar da bishara sosai da sosai, domin duk al’ummai su ji, aka kuwa cece ni daga bakin zaki.

18 Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun abu, ya kuma kiyaye ni, ya kai ni ga Mulkinsa na Sama. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!

Gaisuwa

19 Ka gayar mini da Bilkisu da Akila, da mutanen gidan Onisifaras.

20 Aratas ya dakata a Koranti. Tarofimas kuwa na bar shi a Militas, ba shi da lafiya.

21 Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo kafin damuna. Aubulus yana gaishe ka, da Budis, da Linas, da Kalaudiya, da kuma dukkan ‘yan’uwa.

22 Ubangiji yă kasance a zuciyarka. alheri yă tabbata a gare ku.