A.M. 10

Bitrus da Karniliyas

1 An yi wani mutum a Kaisariya, mai suna Karniliyas, wani jarumi ne na ƙungiyar soja da ake kira Ƙungiyar Italiya.

2 Shi kuwa mutum ne mai ibada, yana tsoron Allah shi da iyalinsa duka, yana yana ba jama’a sadaka hanu sake, yana kuma addu’a ga Allah a kai a kai.

3 Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma, ya ga wani mala’ikan Allah a fili cikin wahayi, ya shigo, ya ce masa, “Ya Karniliyas.”

4 Shi kuwa ya zura masa ido a tsorace, ya ce, “Ya Ubangiji, mene ne?” Mala’ikan kuma ya ce masa, “Addu’arka da sadakarka sun kai har a gaban Allah, abubuwan tunawa ne kuma a gare shi.

5 To, yanzu, sai ka aiki mutane Yafa su kirawo Saminu, wanda ake kira Bitrus,

6 ya sauka a gun Saminu majemi, wanda gidansa yake a bakin bahar.”

7 Da mala’ikan da ya yi masa magana ya tafi, ya kira barorinsa biyu, da kuma wani soja mai ibada daga cikin waɗanda suke yi masa hidima kullum.

8 Da ya ba su labarin kome, ya aike su Yafa.

9 Kashegari suna cikin tafiya, sun zo kusa da gari ke nan, sai Bitrus ya hau kan soro yin addu’a, wajen rana tsaka.

10 Yunwa ta kama shi, har ya so ya ci wani abu. Ana cikin shirya abincin, sai wahayi ya zo masa,

11 ya ga sama ta dare, wani abu kuma yana saukowa kamar babban mayafi, ana zuro shi ƙasa ta kusurwoyinsa huɗu.

12 Cikinsa akwai kowace irin dabba, da masu jan ciki, da tsuntsaye.

13 Sai ya ji wata murya ta ce masa, “Bitrus, tashi, ka yanka ka ci.”

14 Amma Bitrus ya ce, “A’a, ya Ubangiji, don ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko mai ƙazanta ba.”

15 Sai ya sāke jin murya, ji na biyu, ta ce, “Abin da Allah ya tsarkake, kada ka ce da shi marar tsarki.”

16 Da an yi wannan sau uku, nan da nan aka yi sama da abin.

17 Bitrus na a cikin damuwa ƙwarai a kan ko mece ce ma’anar wahayin da aka yi masa, sai ga mutanen da Karniliyas ya aiko tsaye a ƙofar zaure, sun riga sun tambayi gidan Saminu,

18 suna sallama, suna tambaya ko Saminu da ake kira Bitrus a nan ya sauka.

19 Tun Bitrus yana bibiya wahayin nan, Ruhu ya ce masa, “Ga mutum uku nan suna nemanka.

20 Tashi, ka sauka, ku tafi tare, ba da wata shakka ba, domin ni ne na aiko su.”

21 Sai Bitrus ya sauka wurin mutanen, ya ce musu, “Ga ni, ni ne kuke nema. Wace magana yake tafe da ku?”

22 Sai suka ce, “Wani jarumi ne, wai shi Karniliyas, mutumin kirki, mai tsoron Allah, wanda duk jama’ar Yahudawa suke yabo, shi ne wani tsattsarkan mala’ika ya umarce shi, ya aiko ka je gidansa, ya ji maganarka.”

23 Sai Bitrus ya shigo da su, ya sauke su.

Kashegari ya tashi suka tafi tare, waɗansu ‘yan’uwa kuma daga Yafa suka raka shi.

24 Kashegari kuma suka shiga Kaisariya. Dā ma Karniliyas na tsammaninsu, har ya gayyato ‘yan’uwansa da aminansa.

25 Bitrus na shiga gidan ke nan sai Karniliyas ya tarye shi, ya fāɗi a gabansa, ya yi masa sujada.

26 Amma Bitrus ya tashe shi, ya ce, “Tashi, ai, ni ma ɗan adam ne.”

27 Bitrus na zance da shi, ya shiga ya tarar mutane da yawa sun taru.

28 Ya ce musu, “Ku da kanku kun sani, bai halatta Bayahude ya cuɗanya, ko ya ziyarci wani na wata kabila dabam ba. Amma Allah ya nuna mini kada in ce da kowa marar tsarki, ko mai ƙazanta.

29 Saboda haka da aka neme ni, na zo, ban ce a’a ba. To, yanzu ina so in ji abin da ya sa kuka kira ni.”

30 Sai Karniliyas ya ce, “Yau kwana uku ke nan, wajen war haka, ina addu’ar ƙarfe uku na yamma a gidana, sai ga wani mutum tsaye a gabana, yana saye da tufafi masu ɗaukar ido,

31 ya ce, ‘Ya Karniliyas, an amsa addu’arka sadakarka kuma ta zama abar tunawa ga Allah.

32 Saboda haka sai ka aika Yafa a kirawo Saminu, wanda ake kira Bitrus, yă sauka a gidan Saminu majemi a bakin bahar.’

33 Nan da nan kuwa na aika maka, ka kuma kyauta da ka zo. To, yanzu ga mu duk mun hallara a gaban Allah, domin mu ji duk irin abin da Ubangiji ya umarce ka.”

Bitrus Ya Yi Jawabi a Gidan Karniliyas

34 Sai Bitrus ya kāda baki ya ce, “Hakika na gane lalle Allah ba ya tara,

35 amma a kowace al’umma duk mai tsoronsa, mai kuma aikata adalci, abin karɓuwa ne a gare shi.

36 Allah ya aiko wa Isra’ilawa maganarsa, ana yi musu bisharar salama ta wurin Yesu Almasihu, shi ne kuwa Ubangijin kowa.

37 Kun dai san labarin nan da ya bazu a duk ƙasar Yahudiya, an fara tun daga ƙasar Galili, bayan baftismar da Yahaya ya yi wa’azi,

38 wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da yadda ya riƙa zagawa na aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, domin Allah yana tare da shi.

39 Mu kuwa shaidu ne ga duk abin da ya yi a ƙasar Yahudawa da Urushalima. Shi ne kuma suka kashe ta wurin kafa shi a jikin gungume.

40 Shi ne Allah ya tasa a rana ta uku, ya kuma yarda ya bayyana,

41 ba ga dukan jama’a ba, sai dai ga shaidun nan da Allah ya zaɓa tun dā, wato mu ke nan, da muka ci muka sha tare da shi, bayan ya tashi daga matattu.

42 Ya kuma umarce mu mu yi wa mutane wa’azi, mu kuma tabbatar cewa shi ne wanda Allah ya sa mai hukunta rayayyu da matattu.

43 Shi ne duk annabawa suka yi wa shaida, cewa albarkacin sunansa duk mai gaskatawa da shi zai sami gafarar zunubai.”

An Ba Al’ummai Ruhu Mai Tsarki

44 Bitrus na a cikin wannan magana, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauko wa dukan masu jinta.

45 Sai Yahudawa masu bi, ɗaukacin waɗanda suka zo tare da Bitrus, suka yi mamakin ganin har al’ummai ma an zubo musu baiwar Ruhu Mai Tsarki.

46 Domin sun ji suna magana da waɗansu harsuna, suna ta ɗaukaka Allah. Sa’an nan Bitrus ya ce,

47 “Akwai mai iya hana ruwan da za a yi wa mutanen nan baftisma, waɗanda suka sami Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda mu ma muka samu?”

48 Sai ya yi umarni a yi musu baftisma da sunan Yesu Almasihu. Sa’an nan suka roƙe shi ya ƙara ‘yan kwanaki a gunsu.