A.M. 12

An Kashe Yakubu, an Kulle Bitrus

1 A lokacin nan kuwa sarki Hirudus ya fara gwada wa waɗansu ‘yan Ikkilisiya tasku,

2 har ma ya sare Yakubu ɗan’uwan Yahaya da takobi.

3 Da ya ga abin ya ƙayatar da Yahudawa, har wa yau kuma ya kama Bitrus, shi ma. Kwanakin idin abinci marar yisti ne kuwa.

4 Da ya kama shi, ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, su yi tsaronsa, da niyyar kawo shi a gaban jama’a bayan idin.

5 Sai aka tsare Bitrus a kurkuku, Ikkilisiya kuwa ta himmantu ga roƙon Allah saboda shi.

An Ceci Bitrus daga Kurkuku

6 A daren da in gari ya waye Hirudus yake da niyyar fito da shi a yi masa hukunci, Bitrus kuwa na barci a tsakanin soja biyu, ɗaure da sarƙa biyu, masu tsaro kuma suna bakin ƙofa suna tsaron kurkukun,

7 sai ga mala’ikan Ubangiji tsaye kusa da shi, wani haske kuma ya haskaka ɗakin, sa’an nan mala’ikan ya bugi Bitrus a kwiɓi, ya tashe shi, ya ce, “Maza, ka tashi.” Sai kuwa sarƙar ta zube daga hannunsa.

8 Mala’ikan ya ce masa, “Yi ɗamara, ka sa takalminka.” Sai ya yi. Sai ya ce masa, “Yafa mayafinka, ka biyo ni.”

9 Sai ya fito ya bi shi, bai san abin da mala’ikan nan ya yi hakika ne ba, cewa yake wahayi ake yi masa.

10 Da suka wuce masu tsaron farko da na biyu, suka isa ƙyauren ƙarfe na ƙofar shiga gari, ƙyauren kuwa ya buɗe musu don kansa. Sai suka fita. Sun ƙure wani titi ke nan, nan da nan sai mala’ikan ya bar shi.

11 Da Bitrus ya koma cikin hankalinsa, ya ce, “Yanzu kam na tabbata, Ubangiji ne ya aiko mala’ikansa, ya cece ni daga hannun Hirudus, da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.”

12 Da ya gane haka, ya je gidan Maryamu, uwar Yahaya wanda ake kira Markus, inda aka taru da yawa, ana addu’a.

13 Da ya ƙwanƙwasa ƙofar zauren, wata baranya mai suna Roda ta zo ji ko wane ne.

14 Da ta shaida muryar Bitrus, ba ta buɗe ƙofar ba don murna, sai ta koma ciki a guje, ta ce Bitrus na tsaye a ƙofar zaure.

15 Sai suka ce mata, “Ke dai akwai ruɗaɗɗiya.” Ita kuwa ta nace a kan shi ne. Su kuwa suka ce, “To, mala’ikansa ne!”

16 Bitrus dai ya yi ƙwanƙwasawa, da suka buɗe suka gan shi, suka yi ta al’ajabi.

17 Shi kuwa ya ɗaga musu hannu su yi shiru, ya kuma bayyana musu yadda Ubangiji ya fito da shi daga kurkuku. Ya kuma ce, “Ku faɗa wa Yakubu da ‘yan’uwa waɗannan abubuwa.” Sa’an nan ya tashi ya tafi wani wuri.

18 Da gari ya waye kuwa ba ƙaramar rigima ce ta tashi tsakanin sojan nan ba, kan abin da ya sami Bitrus.

19 Da Hirudus ya neme shi bai same shi ba, ya yi ta tuhumar masu tsaron, ya kuma yi umarni a kashe su. Sa’an nan ya tashi daga ƙasar Yahudiya ya tafi Kaisariya, ya yi ‘yan kwanaki a can.

Mutuwar Hirudus

20 To, Hirudus ya yi fushi ƙwarai da mutanen Taya da na Sidon. Suka zo wurinsa da nufi ɗaya. Bayan sun rinjayi Bilastasa, sarkin fāda, suka nemi zaman lafiya, domin ga ƙasar sarkin nan suka dogara saboda abincinsu.

21 Ana nan a wata rana da aka shirya, Hirudus ya yi shigar sarauta, ya zauna a gadon sarauta, ya yi musu jawabi.

22 Taron mutane kuwa suka ɗauki sowa, suna cewa, “Kai! ka ji muryar wani Allah, ba ta mutum ba!”

23 Nan take sai mala’ikan Ubangiji ya buge shi don bai ɗaukaka Allah ba. Sai tsutsotsi suka yi ta cinsa har ya mutu.

Barnaba da Shawulu

24 Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, tana yaɗuwa.

25 Sai Barnaba da Shawulu suka komo daga Urushalima, bayan sun cika aiken da aka yi musu, suka kuma zo da Yahaya wanda ake kira Markus.