A.M. 19

Bulus a Afisa

1 To, lokacin da Afolos yake Koranti, Bulus ya zazzaga ƙasar ta kan tudu, ya gangara zuwa Afisa. A can ya tarar da waɗansu masu bi,

2 sai ya ce musu, “Kun sami Ruhu Mai Tsarki sa’ad da kuka ba da gaskiya?” Suka ce masa, “Ba mu ma ji zuwan Ruhu Mai Tsarki ba.”

3 Sai ya ce, “To, wace baftisma ke nan aka yi muku?” Suka ce, “Irin ta Yahaya ce.”

4 Bulus ya ce, “Ai, Yahaya baftisma ya yi a tuba, yana faɗa wa mutane su gaskata da mai zuwa bayansa, wato Yesu.”

5 Da suka ji haka, aka yi musu baftisma da sunan Ubangiji Yesu.

6 Da Bulus ya ɗora musu hannu, Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu, suka kuwa yi magana da waɗansu harsuna, suna annabci.

7 Su wajen sha biyu ne duka duka.

8 Sai ya shiga majami’a yana wa’azi gabagaɗi, ya kuma yi wata uku yana muhawwara da su, yana kuma rinjayarsu a kan al’amarin Mulkin Allah.

9 Amma da waɗansu suka taurare, suka ƙi ba da gaskiya, suna kushen wannan hanya gaban jama’a, sai ya rabu da su, ya keɓe masu bi, yana ta muhawwara da su a kowace rana makarantar Tiranas.

10 Shekara biyu ana wannan, har dukan mazaunan ƙasar Asiya suka ji Maganar Ubangiji, Yahudawa da al’ummai duka.

‘Ya’yan Siba

11 Ta hannun Bulus kuma Allah ya yi waɗansu mu’ujizai da ba a saba gani ba,

12 har akan kai wa marasa lafiya adikansa, ko tufafinsa da yake sawa yana aiki, sun kuwa warke daga cuce-cucensu, baƙaƙen aljannu kuma sun rabu da su.

13 Sai waɗansu Yahudawa masu yawo gari gari, matsubbata, suka yi ƙoƙarin kama sunan Ubangiji Yesu ga masu baƙaƙen aljannu, suna cewa, “Mun umarce ku da sunan Yesun nan da Bulus yake wa’azi.”

14 To, akwai ‘ya’ya bakwai maza, na wani babban firist na Yahudawa, mai suna Siba, duk suna yin wannan abu.

15 Amma aljanin ya amsa musu ya ce, “Yesu dai na san shi, na kuma san Bulus, to, ku kuma ku wane ne?”

16 Mutumin nan mai aljanin sai ya daka tsalle, ya fāɗa musu, ya fi ƙarfinsu dukkansu, ya ci ɗunguminsu, har suka fita daga gidan a guje, a tuɓe, suna masu rauni.

17 Wannan abu fa ya sanu ga dukan mazaunan Afisa, Yahudawa da al’ummai duka, duka kuma tsoro ya kama su, aka kuwa ɗaukaka sunan Ubangiji Yesu.

18 Da yawa kuma daga cikin waɗanda suka ba da gaskiya suka zo, suna bayyana ayyukansu a fili.

19 Mutane da yawa kuwa masu yin sihiri, suka tattaro littattafansu suka ƙone a gaban jama’a duka. Da suka yi wa littattafan nan kima, sai suka ga sun kai kuɗi azurfa dubu hamsin.

20 Sai kuma Maganar Ubangiji ta ƙara haɓaka, ta kuma fifita ƙwarai.

Hargitsi a Afisa

21 Bayan waɗannan al’amura Bulus ya ƙudura a ransa, cewa in ya zazzaga ƙasar Makidoniya da ta Akaya, za shi Urushalima, ya kuma ce, “Bayan na je can, lalle ne kuma in je in ga birnin Roma.”

22 Da ya aiki mataimakansa biyu Makidoniya, wato Timoti da Arastas, shi kuwa ya ɗan dakata a ƙasar Asiya.

23 A lokacin nan kuwa ba ƙaramin hargitsi aka yi game da wannan hanya ba.

24 Domin akwai wani maƙerin farfaru, mai suna Dimitiriyas, mai ƙera surorin haikalin Artimas da azurfa, ba kuwa ƙaramar riba yake jawo wa masu yin wannan sana’a ba.

25 Sai ya tara su da duk ma’aikatan irin wannan sana’a, ya ce, “Ya ku jama’a, kun sani fa da sana’ar nan muke arziki.

26 Kuna kuwa ji, kuna gani, ba a nan Afisa kawai ba, kusan ma a duk ƙasar Asiya, Bulus ɗin nan ya rinjayi mutane masu yawan gaske, ya juyar da su, yana cewa, allolin da mutum ya ƙera ba alloli ba ne.

27 Ga shi kuma, akwai hatsari, ba wai cinikinmu kawai ne zai zama wulakantacce ba, har ma haikalin nan na uwargijiya Artimas mai girma zai zama ba a bakin kome ba, har kuma a raba ta da darajarta, ita da duk ƙasar Asiya, kai, har duniya ma duka suke bauta wa.”

28 Da suka ji haka suka hasala ƙwarai, suka kuma ɗaga murya gaba ɗaya suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!”

29 Sai garin duk ya ruɗe, jama’a suka ruga zuwa dandali da nufi ɗaya, suna jan Gayus da Aristarkus, mutanen Makidoniya, abokan tafiyar Bulus.

30 Bulus ya so shiga taron nan, amma masu bi suka hana shi.

31 Waɗansu zaɓaɓɓun mutanen ƙasar Asiya, waɗanda suke abokansa, su ma suka aika masa, suka roƙe shi kada ya kuskura ya shiga dandalin nan.

32 Taron kuwa, waɗansu suka ta da murya su ce kaza, waɗansu su ce kaza, don duk taron a ruɗe yake, yawancinsu ma ba su san dalilin da ya sa suka taru ba.

33 Da Yahudawa suka gabatar da Iskandari, waɗansu suka ɗauka a kan shi ne sanadin abin. Iskandari kuwa ya ɗaga hannu a yi shiru, don ya kawo musu hanzari,

34 amma da suka fahimci, cewa shi Bayahude ne, suka ɗaga murya gaba ɗaya har wajen sa’a biyu, suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!”

35 To, da magatakardan garin ya kwantar da hankalin jama’a, ya ce, “Ku mutanen Afisa! Wane mutum ne bai san cewa musamman birnin Afisawa ne suke kula da haikalin mai girma Artimas ba, da kuma dutsen nan da ya faɗo daga sama?

36 To, da yake ba dama a yi musun waɗannan abubuwa, ai, ya kamata ku natsu, kada ku yi kome da garaje.

37 Ga shi, kun kawo mutanen nan, su kuwa ba su yi sata a ɗakin uwargijiya ba, ba su kuma saɓi uwargijiyarmu ba.

38 To, in Dimitiriyas da abokan sana’arsa suna da wata magana a game da wani, ai, ga ɗakin shari’a a buɗe, ga kuma mahukunta, sai su kai ƙara.

39 Amma in wani abu kuke nema dabam, to, ai, sai a daidaita a majalisa ke nan.

40 Hakika muna cikin hatsarin amsa ƙara a kan tawaye saboda al’amarin nan na yau, tun da yake ba za mu iya ba da wani hanzari game da taron hargitsin nan ba.”

41 Da ya faɗi haka ya sallami taron.