A.M. 27

Bulus Ya Shiga Jirgi zuwa Roma

1 Da aka shirya mu tashin jirgin ruwa zuwa ƙasar Italiya, sai suka danƙa Bulus da waɗansu ‘yan sarƙa a hannun wani jarumi, mai suna Yuliyas, na ƙungiyar Augustas.

2 Da muka shiga wani jirgi na Adaramitiya, mai shirin tashi zuwa waɗansu garuruwan da suke gaɓar Asiya, muka fara tafiya. Aristarkus kuwa, wani mutumin Tasalonika ta ƙasar Makidoniya, na tare da mu.

3 Kashegari ga mu a Sidon. Yuliyas kuwa ya yi wa Bulus alheri, ya ba shi izini ya je ya gano abokansa, su yi masa taimako.

4 Da muka tashi daga nan a jirgin ruwa sai muka zaga ta bayan tsibirin Kubrus, saboda iska tana gāba da mu.

5 Bayan da muka haye bahar ɗin da yake kusa da kasar Kilikiya da ta Bamfiliya, muka isa Mira ta ƙasar Likiya.

6 A nan jarumin ya sami wani jirgin Iskandariya mai zuwa ƙasar Italiya, ya sa mu a ciki.

7 Muka yi kwana da kwanaki muna tafiya kaɗan kaɗan, har da ƙyar muka kai kusa da Kinidas. Da dai iska ta hana mu ci gaba, muka zaga ta bayan tsibirin Karita kusa da Salmoni.

8 Muna bin gefen gaɓarsa da ƙyar, har muka isa wani wuri mai suna Amintacciyar Mafaka, wadda take kusa da birnin Lasiya.

9 Da yake an ɓata lokaci mai yawa, tafiyar ma ta riga ta zama mai hatsari, lokacin azumi kuwa ya wuce, sai Bulus ya gargaɗe su,

10 ya ce musu, “Ya ku jama’a, na dai ga tafiyar nan za ta zamanto da masifa da hasara mai yawa, ba wai ta kaya da jirgi kawai ba, har ma ta rayukanmu.”

11 Amma jarumin soja, ya fi mai da hankali ga maganar mai tuƙin jirgin da kuma ta mai jirgin, a kan abin da Bulus ya faɗa.

12 Da yake mafakar nan ba ta kamaci jirage su ci damuna a ciki ba, sai yawanci suka kawo shawara a tashi daga nan, ko ta ƙaƙa su iya kaiwa Finikiya, wata mafakar tsibirin Karita, mai duban gabas maso arewa da kuma gabas maso kudu, su ci damuna a can.

Hadiri a Teku

13 Da iska ta buso daga kudu sannu sannu, a tsammaninsu muradinsu ya biya ke nan, sai suka janye anka suka bi ta gefen tsibirin Karita gab da gaci.

14 Ba da jimawa ba kuwa sai ga wata gawurtacciyar iska da ake kira Yurokilidon ta bugo daga tsibirin.

15 Da iskar ta bugo jirgin, har ya kasa fuskantarta, sai muka sallama mata, ta yi ta kora mu.

16 Da muka bi ta jikin wani ɗan tsibiri wai shi Kauda muka samu muka yi iko da ƙaramin jirginmu da ƙyar.

17 Bayan suka jawo ƙaramin jirgi ɗin a cikin babban jirgi, sai suka yi dabara suka ɗaɗɗaura igiyoyi ta gindin babban jirgin, suka rage shi. Don kuma gudun kada a fyaɗa su a yashin nan na Sirtis mai haɗiye kome, suka sauke filafilai, aka kora jirgin haka.

18 Saboda hadiri yana sa mu tangaɗi ƙwarai da gaske, kashegari sai suka fara watsar da kayan da jirgin ya ɗauko, a ruwa.

19 A rana ta uku kuma, su da kansu suka jefar da kayan aikin jirgin.

20 Da dai muka yi kwana da kwanaki ba mu ga rana ko taurari ba, gawurtacciyar iskar hadiri kuma ta yi ta bugunmu, sai muka fid da zuciya da tsira.

21 Da yake an daɗe ba cin abinci, sai Bulus ya miƙe a tsaye a tsakiyarsu, ya ce, “Ya ku jama’a, da kun ji maganata, da ba ku taso daga tsibirin Karita kun fāɗa wannan masifa da hasara ba.

22 To, a yanzu, ina yi muku gargaɗi ku yi ƙarfin hali, don ba wanda zai yi hasarar ransa a cikinku, sai dai a yi hasarar jirgin.

23 Don a daren jiya wani mala’ikan Allah wanda ni nasa ne, nake kuma bauta masa, ya tsaya kusa da ni,

24 ya ce, ‘Kada ka ji tsoro Bulus, lalle za ka tsaya a gaban Kaisar, ga shi kuma, Allah ya amsa ya yardar maka duk abokan tafiyarka su tsira.’

25 Saboda haka, sai ku yi ƙarfin hali, ya ku jama’a, domin na gaskata Allah a kan cewa, yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka za a yi.

26 Amma fa lalle ne a fyaɗa mu a wani tsibirin.”

27 A dare na goma sha huɗu, ana ta kora mu sakaka a bahar Adariya, wajen tsakar dare sai masu tuƙi suka zaci mun yi kusa da ƙasa.

28 Sai suka gwada zurfin ruwan, suka sami gaba ashirin, da muka ci gaba kaɗan, sai suka sāke gwadawa, suka sami gaba goma sha biyar.

29 Don gudun kada a fyaɗa mu a kan duwatsu, sai suka saki anka guda huɗu na bayan jirgin, suka ƙagauta gari ya waye.

30 Masu tuƙi suna neman gudu daga jirgin ke nan, har sun zura ƙaramin jirgi a cikin ruwa, wai don a ga kamar za su ja su anka ɗin ne daga goshin jirgin su sake su,

31 sai Bulus ya ce da jarumin yaki da kuma sojan. “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba yadda za a yi ku tsira.”

32 Sai sojan suka yayyanke igiyoyin ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa.

33 Da gari ya yi kusan wayewa sai Bulus ya roƙe su su taɓa ɗan abinci, ya ce, “Yau fa kwana goma sha huɗu ke nan kuke zaman jira, ba wani abin da kuka ci.

34 Saboda haka, ina roƙonku ku ci abinci, don lafiyarku, tun da yake ba wanda ko gashin kansa zai yi ciwo a cikinku.”

35 Da ya faɗi haka, ya ɗauki curin gurasa, ya yi godiya ga Allah a gabansu duka, sa’an nan ya gutsuttsura ya fara ci.

36 Sai duk suka farfado, su ma kansu suka ci abinci.

37 Mu duka a cikin jirgin kuwa mutum metan da saba’in da shida ne.

38 Da suka ci suka ƙoshi, sai suka riƙa rage wa jirgin nauyi, suka yi ta zub da alkama a cikin ruwa.

Ragargajewar Jirgi

39 Da gari ya waye ba su shaida ƙasar ba, amma dai sun lura da wani lungu da gaci mai yashi, sai kuma suka yi shawara cewa in mai yiwuwa ne su kai jirgin kan yashin.

40 Sai suka daddatse su anka duka, suka bar su a ruwa, suna kuma ɓalle maɗaurin abin juyar da jirgin a lokacin, sa’an nan kuma suka ta da filafilan goshin jirgin daidai iska, suka doshi gaci.

41 Amma da muka isa wata mahaɗar ruwa, sai suka tura jirgin ya dunguri yashi, har goshinsa ya cije ya kasa motsi, ƙarshensa kuma ya fara ragargejewa saboda haukan raƙuman ruwa.

42 Sai sojan suka yi niyya su kashe ‘yan sarka, don kada wani ya yi ninƙaya ya tsira.

43 Amma jarumin da ya so ya ceci Bulus, ya hana i da nufinsu, ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci,

44 sauran kuwa waɗansu suka hau katako, waɗansu kuma suka hau tarkacen jirgin. Da haka duk suka kai gaci lafiya.