AFI 6

Biyayya da Ƙauna

1 Ku ‘ya’ya, ku yi wa iyayenku biyayya tsakani da Ubangiji, domin wannan shi ne daidai.

2 Wannan shi ne umarnin farko mai alkawari, cewa, “ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,

3 don al’amarinka ya kyautatu, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”

4 Ku ubanni, kada ku sa ‘ya’yanku su yi fushi, sai dai ku goye su da tarbiyya, da kuma gargaɗi ta hanyar Ubangiji.

5 Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya, da hali bangirma tare da matsananciyar kula da zuciya ɗaya, Almasihu kuke yi wa ke nan,

6 ba aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai kamar bayin Almasihu masu aikata abin da Allah yake so, da zuciya ɗaya,

7 kuna bauta da kyakkyawar niyya domin Ubangiji kuke yi wa, ba mutane ba.

8 Kun sani, kowane alherin da mutum ya yi, ko shi ɗa ne ko bawa, Ubangiji zai sāka masa shi.

9 Ku iyayengiji, ku ma ku yi musu haka, ku bar tsorata su, ku sani, shi wanda yake Ubangijinsu da ku duka, yana Sama, shi kuwa ba ya zaɓe.

Makaman Allah Duka

10 A ƙarshe kuma, ku ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa.

11 Ku yi ɗamara da dukan makamai na Allah, don ku iya dagewa gāba da kissoshin Iblis.

12 Ai, famarmu ba da ‘yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama, masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu take hannunsu.

13 Saboda haka, sai ku ɗauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa a muguwar ranar nan, bayan kuma kun gama kome duka, ku dage.

14 Saboda haka fa ku dage, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci ya zama sulkenku,

15 shirin kai bisharar salama ya zama kamar takalmi a ƙafafunku.

16 Banda waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kiban wutar Mugun nan da ita.

17 Ku kuma ɗauki kwalkwalin ceto, da takobin Ruhu, wato Maganar Allah,

18 a koyaushe kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fāsawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matuƙar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu’a.

19 Ni ma ku yi mini, domin in sami baiwar yin hurci, in yi magana gabagaɗi, in sanar da asirin bishara,

20 wadda ni jakadanta ne, ɗaurarre. Ku dai yi mini addu’a, duk sa’ad da nake yin bisharar, in bayyana ta gabagaɗi, kamar yadda ya kamata in yi.

Gaisuwa

21 A yanzu kuwa, don ku ma ku san lafiyata, da kuma halin da nake a ciki, ga Tikikus, ƙaunataccen ɗan’uwa, amintaccen mai hidimar Ubangiji, zai sanar da ku kome.

22 Na aiko shi gare ku musamman domin ku san yadda muke, ya kuma ƙarfafa muku zuciya.

23 Salamar Allah Uba da ta Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata ga ‘yan’uwa, tare da ƙauna game da bangaskiya.

24 Alheri yă tabbata ga dukkan masu ƙaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu da ƙauna marar ƙarewa.