DAN 11

1 A shekara ta fari ta sarautar Dariyus Bamediye, na tashi na tabbatar da shi, na kuma ƙarfafa shi.”

Sarkin Kudu da Sarkin Arewa

2 “Yanzu zan faɗa maka gaskiya. Za a ƙara samun sarakuna uku a Farisa, amma na huɗun zai fi dukansu dukiya. Sa’ad da ya ƙasaita saboda dukiyarsa, zai kuta dukan daularsa ta yi gaba da mulkin Hellas.

3 “Sa’an nan wani sarki babba zai taso wanda zai yi mulki da babban iko yadda ya ga dama.

4 Sa’ad da ya ƙasaita mulkinsa zai faɗi, a rarraba shi kashi huɗu a ba waɗansu waɗanda ba zuriyarsa ba, amma ba za su yi mulki da iko kamar yadda ya yi ba, gama za a tumɓuki mulkinsa saboda waɗansu.

5 “Sarkin kudu zai yi ƙarfi, amma ɗaya daga cikin jarumawansa zai ƙasaita fiye da shi, mulkinsa kuma zai zama babba.

6 Bayan waɗansu shekaru za su ƙulla zumunci. Sarkin kudu zai aurar wa sarkin arewa da ‘yarsa don sāda zumunci, amma ba za ta sami iko ba. Shi da zuriyarsa ba za su amince da ita ba. Za a yi watsi da ita, ita da masu yi mata hidima, da mahaifinta, da waliyyinta.

7 Ba za a daɗe ba, wani daga cikin danginta zai tasar wa sojojin sarkin arewa da yaƙi, ya shiga kagararsu, ya ci su da yaƙi.

8 Zai kwashe gumakansu ganima, da siffofinsu na zubi, ya kai Masar, tare da tasoshinsu na azurfa da na zinariya masu daraja. Zai yi shekaru bai kai wa sarkin arewa yaƙi ba.

9 Bayan wannan sarkin arewa zai kai wa sarkin kudu yaƙi, amma tilas zai janye, ya koma ƙasarsa.

10 “’Ya’yansa maza za su tara babbar rundunar yaƙi. Ɗayansu zai mamaye kamar rigyawa, har ya kai kagara wurin da abokan gāba suke.

11 Sarkin kudu zai husata ya kai wa sarkin arewa yaƙi, za a ba da rundunar sojojin sarkin arewa a hannunsa.

12 Ganin ya kashe sojoji masu ɗumbun yawa, sai ya yi girmankai, amma nasararsa ba mai ɗorewa ba ce.

13 Sarkin arewa kuwa zai tara babbar rundunar soja fiye da ta dā. Bayan waɗansu shekaru kuwa zai kama hanya da babbar rundunar soja, da kayan faɗa masu yawan gaske.

14 “A waɗannan kwanaki mutane da yawa za su tashi gāba da sarkin kudu. Amma waɗansu ‘yan kama-karya za su taso daga jama’arka da niyya su cika abin da wahayin ya ce, amma za a fatattaka su.

15 Sa’an nan sarkin arewa zai zo ya gina mahaurai a jikin garun birni don ya ci birnin da yaƙi. Sojojin kudu kuwa ba za su iya tsayawa ba, ko zaɓaɓɓun jarumawansa ma, gama za su rasa ƙarfin tsayawa.

16 Amma wanda ya kawo masa yaƙin zai yi yadda ya ga dama, ba wanda zai iya ja da shi. Zai tsaya a ƙasa mai albarka, ya mallake ta duka.

17 Zai yunƙuro da dukan ƙarfin mulkinsa, zai zo ya gabatar da shawarar salama, ya aikata ta. Zai aurar masa da ‘yarsa don ta lalatar da mulkin abokin gabansa, amma wannan dabara ba za ta ci ba.

18 Daga nan zai yunƙura zuwa ƙasashen gaɓar teku, ya ci da yawa daga cikinsu, amma wani jarumi zai kawo ƙarshen fāɗin ransa. Zai sa fāɗin ransa ya koma masa.

19 Sa’an nan zai juya, ya nufi kagarar ƙasarsa, amma zai yi tuntuɓe, ya fāɗi, ba za a ƙara ganinsa ba.”

Mugun Sarki

20 “Wani sarki zai ɗauki matsayinsa, zai aiki mai karɓar haraji cikin daularsa, amma ba da daɗewa ba za a kashe shi, ba cikin hargitsin yaƙi ba.

21 “Wani kuma rainanne zai maye gurbin wancan, shi kuwa ba ɗan jinin sarauta ba ne. Zai taso ba zato ba tsammani, ya ƙwace sarautar ta hanyar zamba.

22 Zai shafe rundunonin sojoji har da rantsattsen shugaba.

23 Daga lokacin da aka ƙulla yarjejeniya da shi, zai yi munafunci. Zai sami iko ta wurin goyon bayan mutane kima.

24 Ba zato ba tsammani zai kai wa lardi mafi arziki hari. Zai aikata abin da kakanninsa ba su taɓa yi ba. Zai rarraba wa mabiyansa kwason yaƙi, da ganima, da dukiya. Zai kuma yi shiri ya kai wa kagara hari amma domin ɗan lokaci ne kawai.

25 “Zai iza kansa ya yi ƙarfin hali ya kai wa sarkin kudu yaƙi da babbar rundunar soja. Sarkin kudu zai haɗa babbar rundunar soja mai ƙarfi don yaƙin, amma ba zai iya karo da shi ba, domin za a shirya masa maƙarƙashiya.

26 Waɗanda suke na jikinsa, su ne za su zama sanadin faɗuwarsa. Za a kashe rundunar sojojinsa, a shafe su duk.

27 Sarakunan nan biyu sun sa mugunta a ransu. Za su zauna a tebur guda su yi ta shara wa juna ƙarya, amma a banza, gama lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna.

28 “Sarkin arewa zai koma gida da dukiya mai ɗumbun yawa. Zuciyarsa za ta yi gāba da tsattsarkan alkawari. Zai yi yadda ya ga dama sa’an nan ya koma ƙasarsa.

29 “A ƙayyadadden lokaci kuma zai koma kudu, amma a wannan karo abin ba zai zama kamar dā ba,

30 gama jiragen ruwa na Kittim za su tasar masa, shi kuwa zai ji tsoro, ya janye.

“Zai koma ya huce fushinsa a kan tsattsarkan alkawari. Zai kula da waɗanda suka yi banza da tsattsarkan alkawarin.

31 Sojojinsa za su ɓata tsattsarkan wuri da kagararsa. Za su kuma hana yin hadayu na yau da kullum, su kafa abin banƙyama da suke lalatarwa.

32 Waɗanda suka ta da alkawarin kuma, sarki zai ƙara dulmuyar da su ta wurin daɗin bakinsa. Amma waɗanda suka san Allahnsu za su tsaya da ƙarfi su yi wani abu.

33 Waɗansu daga cikin mutane waɗanda suke da hikima, za su wayar da kan mutane da yawa. Amma duk da haka za a kashe su da takobi, waɗansu da wuta, a washe waɗansu a kai su bauta.

34 Sa’ad da suka fāɗi ba za su sami wani taimakon kirki ba, mutane da yawa za su haɗa kai da su, amma da munafunci.

35 Waɗanda suke da hikima, za a kāshe su, don a tsabtace su, a tsarkake su, su yi tsab tsab, har matuƙar da aka ƙayyade ta yi.

36 “Sa’an nan sarki zai yi yadda ya ga dama. Zai ɗaukaka kansa, ya aza ya fi kowane allah. Zai kuma yi maganganu na saɓo a kan Allahn alloli, zai yi nasara, sai lokacin da aka huce haushi, gama abin da aka ƙaddara zai cika.

37 Ba zai kula da gumakan kakanninsa ba, ko begen da mata suke yi. Ba kuwa zai kula da kowane irin gunki ba, domin zai aza kansa ya fi su duka.

38 A maimakon haka zai girmama gunkin kagarai, gunkin da kakanninsa ba su ko sani ba, shi ne zai miƙa masa zinariya, da azurfa, da duwatsu masu daraja, da abubuwa masu tamani.

39 Zai tasar wa kagara mafi ƙarfi da taimakon baƙon gunki. Waɗanda suka yarda da shi, zai ba su girma, ya kuma shugabantar da su a kan mutane da yawa, zai raba musu ƙasa ta zama ladansu.

40 “A lokaci na ƙarshe sarkin kudu zai tasar masa, sarkin arewa kuwa zai tunzura, ya tasar masa da karusai da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, ya ci su da yaƙi, ya wuce.

41 Zai shiga kyakkyawar ƙasa ya kashe dubban mutane. Amma ƙasar Edom, da ta Mowab, da yawancin ƙasar Ammonawa za su kuɓuta daga hannunsa.

42 Zai kai wa waɗansu ƙasashe yaƙi, ƙasar Masar kuwa ba za ta kuɓuta ba.

43 Zai mallaki dukiyoyi na zinariya, da na azurfa, da dukan abubuwa masu tamani na Masar. Zai kuma ci Libiyawa da Habasha da yaƙi.

44 Labarin da zai zo masa daga gabas da arewa zai firgita shi, shi kuwa zai ci gaba da yin yaƙi da zafi, ya karkashe mutane da yawa, ya shafe su.

45 Zai kafa manyan alfarwai na sarauta a tsakanin teku da tsattsarkan dutse. Amma zai mutu ba kuwa wanda zai taimake shi.”