DAN 12

Lokaci na Ƙarshe

1 “A wannan lokaci Mika’ilu babban shugaba wanda yake lura da jama’arka zai bayyana. A lokacin za a yi tashin hankali irin wanda ba a taɓa yi ba, tun da aka yi duniya. Amma a lokacin za a ceci jama’arka waɗanda aka rubuta sunayensu cikin littafi.

2 Waɗanda suka rasu za su tashi, waɗansu zuwa rai madawwami, waɗansu kuwa zuwa kunya da madawwamin ƙasƙanci.

3 Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar sararin sama, waɗanda kuma suka juyar da mutane da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.

4 “Amma kai, Daniyel, sai ka rufe maganar, ka kuma kulle littafin, har zuwa ƙarshen lokaci. Mutane da yawa za su yi ta kai da kawowa, ilimi kuma zai ƙaru.”

5 Sa’an nan ni Daniyel na duba, sai ga waɗansu biyu a tsaye, ɗaya a wannan gāɓa ɗayan kuma a waccan gāɓar kogin.

6 Dayansu ya ce wa mutumin da yake sāye da rigar lilin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin, “Sai yaushe waɗannan abubuwan banmamaki za su ƙare?”

7 Sai mutumin da yake sāye da rigar lilin ɗin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin ya ɗaga hannuwansa sama, sa’an nan ya rantse da wanda yake rayayye har abada, ya ce, “Za a yi shekara uku da rabi. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa’ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”

8 Na ji, amma ban gane ba. Sai na ce, “Ya shugabana, mene ne ƙarshen waɗannan abubuwa?”

9 Sai ya ce, “Yi tafiyarka, Daniyel, gama an rufe wannan magana, an kuma kulle ta har ƙarshen lokaci.

10 Mutane da yawa za su tsarkake kansu, su zama masu tsabta tsab tsab, amma mugaye ba za su gane ba, za su yi ta muguntarsu, amma masu hikima za su gane.

11 “Tun daga lokacin da za a hana miƙa hadayar ƙonawa ta yau da kullum, a kafa abin banƙyama, wanda yake lalatarwa, za a yi kwana dubu da ɗari biyu da tasa’in.

12 Masu farin ciki ne waɗanda suka daure, har suka kai ƙarshen kwana dubu da ɗari uku da talatin da biyar.

13 “Ka yi tafiyarka ka huta, a ƙarshen kwanaki za ka tashi ka karɓi naka rabo.”