YUSH 1

Matar Yusha’u wadda Ta Ci Amanarsa da ‘Ya’yanta

1 Ubangiji kuwa ya yi magana da Yusha’u ɗan Beyeri a zamanin mulkin Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, sarakunan Yahuza, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yehowash, Sarkin Isra’ila.

2 Sa’ad da Ubangiji ya fara yin magana da Yusha’u ya ce masa, “Tafi ka auro karuwa, ka haifi ‘ya’yan karuwanci, gama ƙasar tana yin fasikanci sosai, wato ta bar bin Ubangiji.”

3 Sai ya tafi ya auri Gomer, ‘yar Diblayim. Ta yi ciki, ta haifi masa ɗa namiji.

4 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Yezreyel, gama ba da daɗewa ba zan ziyarci gidan Yehu da hukunci saboda jinin da ya zubar a Yezreyel. Zan sa mulkin Isra’ila ya ƙare.

5 A wannan rana zan karya bakan Isra’ila a kwarin Yezreyel.”

6 Gomer ta kuma ɗauki ciki, ta haifi ‘ya mace. Ubangiji kuma ya ce wa Yusha’u, “Ka raɗa mata suna Bajinƙai, gama ba zan ƙara yi wa jama’ar Isra’ila jinƙai ba, har da zan gafarta mata.

7 Amma zan yi wa mutanen Yahuza jinƙai. Ni kaina zan cece su ba da baka ba, ba kuwa da takobi, ko da yaƙi, ka da dawakai, ko da sojojin dawakai ba.”

8 Sa’ad da ta yaye Ba-jinƙai, ta sāke ɗaukar ciki, ta haifi ɗa namiji.

9 Ubangiji kuma ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Ba-mutanena-ba-ne, gama ku ba mutanena ba ne,ni kuma ba Allahnku ba ne.

10 “Duk da haka yawan mutanen Isra’ila

Zai zama kamar yashi a bakin teku,

Wanda ba za a iya aunawa ko ƙidayawa ba.

Maimakon kuma a ce, ‘Ku ba mutanena ba ne,’

Za a ce, ‘Ku mutanen Allah ne mai rai.’

11 Mutanen Yahuza da mutanen Isra’ila za su haɗu su zama ɗaya,

Za su zaɓa wa kansu shugaba ɗaya.

Za su shugabanci ƙasar

Gama ranar Yezreyel babba ce.”