YUSH 2

Ubangiji Yana Ƙaunar Mutanensa Marasa Aminci

1 “Ka ce wa ‘yan’uwanka maza, ‘Ku mutanena ne,’ ka kuma ce wa ‘yar’uwarka, ‘Kin sami jinƙai!’

2 Ku roƙi uwarku,

Gama ita ba matata ba ce,

Ni kuma ba mijinta ba ne.

Ku roƙe ta ta daina karuwancinta,

Ta rabu da masu rungumar mamanta.

3 In ba haka ba, sai in yi mata tsiraici,

In bar ta kamar ran da aka haife ta.

In maishe ta kamar jeji,

In bar ta kamar busasshiyar ƙasa,

In kashe ta da ƙishi.

4 Ba zan yi wa ‘ya’yanta jinƙai ba,

Domin su ‘ya’yan karuwanci ne

5 Gama uwarsu ta yi karuwanci.

Ita wadda ta haife su ta yi abin kunya.

Gama ta ce, ‘Zan bi samarina

Waɗanda suke ba ni ci da sha,

Da ulu, da lilin, da mai, da ruwan inabi.’

6 “Don haka zan shinge hanyarta da ƙaya,

Zan gina mata garu don kada ta sami hanyar fita.

7 Za ta bi samarinta, amma ba za ta tarar da su ba.

Za ta neme su, amma ba za ta same su ba.

Sa’an nan za ta ce, ‘Zan koma wurin mijina na fari,

Gama zamana na dā ya fi na yanzu!’

8 “Amma ba ta sani ni nake ba ta hatsi, da ruwan inabi, da mai,

Da azurfa, da zinariya da yawa

Waɗanda suka bauta wa gunkin nan Ba’al da su ba.

9 Don haka zan hana mata hatsi a kakarsa,

Da ruwan inabi a kakarsa, da kuma ulu da lilin

Waɗanda suka zama abin rufe tsiraicinta.

10 Yanzu zan buɗe tsiraicinta

A idon samarinta,

Ba kuwa wanda zai cece ta daga hannuna.

11 Zan sa ta daina farin cikinta,

Da idodinta, da kiyaye lokatan amaryar wata,

Da hutawar ranar Asabar,

Da ƙayyadaddun idodinta.

12 Zan ɓata inabinta da itatuwan ɓaure

Waɗanda take cewa, ‘Waɗannan su ne hakkina

Wanda samarina suka ba ni.’

Zan sa su zama kurmi,

Namomin jeji su cinye su.

13 Zan hukunta ta saboda kwanakin idodin gunkin nan Ba’al.

A kwanakin nan takan ƙona musu turare,

Ta yi ado da zobe da lu’ulu’ai,

Ta bi samarinta, amma ta manta da ni.”

In ji Ubangiji.

14 “Don haka, ga shi, zan rarrashe ta,

In kai ta cikin jeji,

In ba ta magana.

15 Can zan ba ta gonar inabi,

In mai da kwarin Akor, wato wahala, ƙofar bege.

A can za ta amsa mini kamar a kwanakin ƙuruciyarta,

Kamar lokacin da ta fito daga ƙasar Masar.

16 Ni Ubangiji na ce, a waccan rana

Za ta ce da ni,

‘Mijina,’ ba za ta ƙara ce da ni Ba’al ba.

17 Zan kawar da sunayen Ba’al daga bakinta.

Ba za a ƙara kiransu da sunayensu ba.

18 “A waccan rana zan yi alkawari

Da namomin jeji, da tsuntsaye,

Da abubuwa masu rarrafe saboda Isra’ila.

Zan kuma kakkarya baka da takobi,

In kuma sa yaƙi ya ƙare a ƙasar,

Sa’an nan za su yi zamansu lami lafiya.

19 Zan ɗaura auren da yake cikin adalci,

Da bisa kan ka’ida, da ƙauna.

20 Zan ɗaura auren da yake cikin aminci,

Za ki kuwa sani, ni ne Ubangiji.

21 “A waccan rana, zan amsa wa sammai,

Su kuma za su amsa wa ƙasa.

22 Ƙasa kuma za ta amsa wa hatsi, da ruwan inabi, da mai,

Su ma za su amsa wa Yezreyel.

23 Zan dasa ta a ƙasa domin kaina.

Zan kuma yi wa ‘Ba-jinƙai,’ jinƙai,

In kuma ce wa ‘Ba-mutanena ba,’ ‘Mutanena!’

Su ma za su ce, ‘Kai ne Allahna!’ ”