DAN 6

Daniyel a Kogon Zakoki

1 Dariyus ya ga ya yi kyau ya naɗa muƙaddas guda ɗari da ashirin a dukan mulkinsa.

2 Sai ya naɗa Daniyel da waɗansu mutum biyu su zama shugabannin muƙaddasan nan. Su muƙaddasan kuwa za su riƙa ba shugabannin labarin aikinsu, don kada sarki ya yi hasarar kome.

3 Sai Daniyel ya shahara fiye da sauran shugabannin, da su muƙaddasan, domin yana da nagarin ruhu a cikinsa. Sarki kuwa ya shirya ya gabatar da shi kan dukan mulkin.

4 Sai shugabannin, da su muƙaddasan suka nemi Daniyel da laifi game da ayyukan mulki, amma ba su sami laifin da za su tuhume shi da shi ba, domin shi amintacce ne, ba shi da kuskure ko ha’inci.

5 Sai mutanen nan suka ce, “Ba za mu sami Daniyel da laifin da za mu kama shi da shi ba, sai dai ko mu neme shi da laifi wajen dokokin Allahnsa.”

6 Sa’an nan waɗannan shugabanni da muƙaddasai suka ƙulla shawara, suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Ran sarki Dariyus ya daɗe!

7 Dukan shugabannin ƙasar da masu mulki da muƙaddasai, da ‘yan majalisa, da wakilai, sun tsai da shawara, cewa ya kamata sarki ya kafa doka, ya yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu’a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, sai a tura shi cikin kogon zakoki.

8 Yanzu, ya sarki, sai ka tabbatar da dokar, ka sa hannu, don kada a sāke ta, gama dokar Mediya da Farisa ba a soke ta.”

9 Sai sarki Dariyus ya sa hannu a dokar.

10 Sa’ad da Daniyel ya sani an sa hannu a dokar, sai ya tafi gidansa. Ya buɗe tagogin benensa waɗanda suke fuskantar Urushalima. Sau uku kowace rana yakan durƙusa ya yi addu’a, yana gode wa Allahnsa kamar yadda ya saba.

11 Sai mutanen nan suka tafi, suka iske Daniyel yana kai koke-kokensa da roƙonsa ga Allahnsa.

12 Sai suka taho wurin sarki, suka yi magana a kan dokar sarki, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ashe, ba ka sa hannu a dokar ba, cewa cikin kwana talatin nan gaba kada kowa ya yi addu’a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, sai a jefa shi a kogon zakoki?”

Sai sarki ya amsa, ya ce, “Dokar tabbatacciya ce, gama dokar Mediya da Farisa, ba ta sokuwa.”

13 Sa’an nan suka amsa wa sarki cewa, “Ya sarki, Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga ƙasar Yahuza, bai kula da kai ba, balle fa dokar da ka kafa, amma yana ta yin addu’a sau uku kowace rana.”

14 Sa’ad da sarki ya ji wannan magana, sai ransa ya ɓaci ƙwarai, sai ya shiga tunani ta yadda zai yi ya kuɓutar da Daniyel. Ya yi ta fama har faɗuwar rana yadda zai yi ya kuɓutar da shi.

15 Sai waɗannan mutane suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Ka sani fa ya sarki, doka ce ta Mediya da Farisa, cewa ba dama a soke doka ko umarni wanda sarki ya kafa.”

16 Sarki kuwa ya umarta a kawo Daniyel, a tura shi cikin kogon zakoki. Sarki kuma ya ce wa Daniyel, “Ina fata Allahn nan wanda kake bauta masa kullum zai cece ka.”

17 Sai aka kawo dutse aka rufe bakin kogon, sarki kuwa ya hatimce shi da hatiminsa, da hatimin fādawansa, don kada a sāke kome game da Daniyel.

18 Sarki ya koma fādarsa, ya kwana yana azumi, bai ci abinci ba, ya kuma kāsa yin barci.

19 Gari na wayewa, sai sarki ya tashi, ya tafi da gaggawa wurin kogon zakoki.

20 Da ya zo kusa da kogon da Daniyel yake, sai ya ta da murya ya yi kira da damuwa, ya ce wa Daniyel, “Ya Daniyel, bawan Allah mai rai, ko Allahn nan naka wanda kake bauta masa kullum, yana da ikon cetonka daga zakoki?”

21 Sai Daniyel ya ce wa sarki, “Ran sarki ya daɗe!

22 Allahna ya aiko mala’ikansa ya rufe bakunan zakoki, ba su iya yi mini lahani ba, domin ban yi wa Allah laifi ba, ban kuma yi maka ba.”

23 Sarki ya cika da murna ƙwarai, ya umarta a fito da Daniyel daga kogon. Sai aka fito da Daniyel daga kogon, aka ga ba wani lahani a jikinsa saboda ya dogara ga Allahnsa.

24 Sai sarki ya umarta a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da ‘ya’yansu, da matansu cikin kogon zakoki. Tun ba su kai ƙurewar kogon ba, sai zakoki suka hallaka su, suka kakkarye ƙasusuwansu gutsi-gutsi.

25 Dariyus sarki kuwa ya rubuta wa dukan jama’a da al’ummai, waɗanda suke zaune a duniya duka, ya ce, “Salama ta yalwata a gare ku.

26 Ina umartar mutanen da suke cikin mulkina su yi rawar jiki, su ji tsoron Allah na Daniyel,

Gama shi Allah ne mai rai, Madawwami,

Sarautarsa ba ta tuɓuwa,

Mulkinsa kuma madawwami ne.

27 Yakan yi ceto, yakan kuma kuɓutar,

Yana aikata alamu da mu’ujizai a sama da duniya.

Shi ne wanda ya ceci Daniyel daga bakin zakoki.”

28 Daniyel kuwa ya bunƙasa a zamanin mulkin Dariyus da na Sairus mutumin Farisa.