DAN 7

Dabbobi Huɗu da Daniyel Ya Gani cikin Wahayi

1 A shekara ta farko ta sarautar Belshazzar Sarkin Babila, Daniyel ya yi mafarki, ya kuma ga wahayi sa’ad da yake kwance a gadonsa. Sai ya rubuta mafarkin. Ga abin da ya faɗa.

2 Daniyel ya ce, “A wahayi da dare na ga iskar samaniya daga kusurwa huɗu tana gurɓata babbar teku.

3 Sai manyan dabbobi huɗu iri dabam dabam suka fito daga cikin tekun.

4 Kamannin dabba ta fari irin ta zaki ce, amma tana da fikafikan gaggafa. Ina kallo, sai aka fige fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum.

5 “Sai kuma ga dabba ta biyu mai kama da beyar. Gefe guda na jikinta ya ɗara ɗaya. Tana riƙe da haƙarƙari uku a haƙoranta! Sai aka ce mata, ‘Tashi ki cika cikinki da nama.’

6 “Bayan wannan kuma, sai ga wata dabba mai kama da damisa tana da fikafikai huɗu irin na tsuntsu a bayanta, tana kuma da kai huɗu. Sai aka ba ta mulki.

7 “Bayan wannan kuma a wahayi na dare na ga dabba ta huɗu mai ƙarfi ƙwarai, mai bantsoro da banrazana. Tana da haƙoran ƙarfe, zaga-zaga. Ta cinye, ta ragargaza, sa’an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. Dabam take da sauran dabbobin da suka riga ta. Tana kuma da ƙaho goma.

8 Ina duban ƙahonin, sai ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙane, ya ɓullo a tsakiyarsu. Sai aka tumɓuke ƙaho uku na fari daga cikinsu. Wannan ƙaramin ƙaho yana da idanu kamar na mutum, yana kuma da baki, yana hurta maganganu na fariya.”

Wahayi na Wanda Ya Dawwama har Adaba

9 “Ina dubawa sai na ga an ajiye gadajen sarauta,

Sai wani wanda yake Tun Fil Azal ya zauna kursiyinsa.

Rigarsa fara fat kamar dusar ƙanƙara,

Gashin kansa kamar ulu ne tsantsa,

Kursiyinsa harshen wuta ne,

Ƙafafun kursiyin masu kamar karusa, wuta ne.

10 Kogin wuta yana gudu daga gabansa.

Dubun dubbai suna ta yi masa hidima,

Dubu goma sau dubu goma suka tsaya a gabansa,

Aka kafa shari’a, aka buɗe littattafai.

11 “Na yi ta dubawa saboda manya manyan maganganun fariya da ƙahon yake hurtawa, sai na ga an kashe dabbar, an jefar da gawar cikin wuta don ta ƙone.

12 Sauran dabbobi kuwa aka karɓe mulkinsu, amma aka bar su da rai har wani ƙayyadadden lokaci.

13 “A cikin wahayi na dare, na ga wani kamar Ɗan Mutum.

Yana zuwa cikin gizagizai,

Ya zo wurin wanda yake Tun Fil Azal,

Aka kai shi gabansa.

14 Aka kuwa danƙa masa mulki, da ɗaukaka, da sarauta,

Domin dukan jama’a, da al’ummai, da harsuna su bauta masa.

Mulkinsa, madawwamin mulki ne,

Wanda ba zai ƙare ba.

Sarautarsa ba ta tuɓuwa.”

Ma’anar Wahayin

15 “Amma ni Daniyel raina ya damu, wahayin da na gani ya tsorata ni.

16 Sai na matsa kusa da ɗaya daga cikin waɗanda suke tsaye a wurin, na tambaye shi ma’anar waɗannan abubuwa duka. Sai ya bayyana mini, ya kuma ganar da ni ma’anar waɗannan abubuwa.

17 Waɗannan manyan dabbobi guda huɗu, sarakuna ne huɗu waɗanda za su taso a duniya.

18 Amma tsarkaka na Maɗaukaki za su karɓi mulki, su kuwa riƙe mulkin har abada abadin.

19 “Sai na nemi in san ainihin ma’anar dabba ta huɗu, wadda ta bambanta da sauran. Tana da bantsoro ƙwarai, tana kuma da haƙoran baƙin ƙarfe da faratan tagulla. Ta cinye, ta ragargaje, sa’an nan ta tattake sauran da ƙafafunta.

20 Na kuma so in san ma’anar ƙahoninta goma, da ɗaya ƙahon wanda ya tsiro, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa. Ƙahon nan yake da idanu da bakin da yake hurta manyan maganganun fariya, wanda girmansa ya fi na sauran.

21 “Ina dubawa ke nan sai ga wannan ƙaho yana yaƙi da tsarkaka har ya rinjaye su,

22 sai da Tun Fil Azal ya zo ya yanke shari’a, aka ba tsarkaka na Maɗaukaki gaskiya. Da lokaci ya yi aka ba tsarkaka mulkin.

23 “Ga abin da ya ce, ‘Dabba ta huɗu za ta zama mulki na huɗu a duniya, wanda zai bambanta da sauran mulkokin. Zai cinye duniya duka, ya ragargaje ta, ya tattake ta.

24 Ƙahonin nan goma kuwa, sarakuna goma ne waɗanda za su taso daga cikin mulkin. Sa’an nan wani sarki zai taso a bayansu wanda zai bambanta da sauran da suka fara tasowa, zai kā da sarakuna uku.

25 Zai yi maganganun saɓo a kan Maɗaukaki, zai tsananta wa tsarkaka na Maɗaukaki, zai yi ƙoƙari ya sāke lokatai, da shari’a, za a kuwa bashe su a hannunsu, har shekara uku da rabi.

26 Amma majalisa za ta zauna ta yanke shari’a, za a karɓe mulkinsa, a hallaka shi har abada.

27 Sa’an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki. Mulkinsa madawwamin mulki ne. Dukan sarakunan duniya za su bauta masa, su kuma yi masa biyayya.’

28 “Ni Daniyel na firgita ƙwarai, fuskata ta yi yaushi. Amma na riƙe al’amarin duka a zuciyata.”