DAN 8

Wahayi na Rago da Bunsuru

1 A shekara ta uku ta sarautar Belshazzar, sai ni Daniyel na ga wahayi bayan wancan na fari.

2 A wahayin sai na gani ina a bakin kogin Ulai a Shushan, masarautar lardin Elam.

3 Da na ta da idanuna, sai na ga rago a tsaye a gāɓar kogin. Yana da ƙaho biyu dogaye, amma ɗaya ya ɗara ɗaya tsawo. Wanda ya ɗara tsawon shi ne ya tsiro daga baya.

4 Na ga ragon ya kai karo wajen yamma da wajen kudu, da wajen arewa. Ba wata dabbar da ta iya karawa da shi, ba wanda kuma zai iya kuɓuta daga ikonsa, ya yi yadda ya ga dama, ya ɗaukaka kansa.

5 Sa’ad da nake cikin tunani, sai ga bunsuru ya ɓullo daga wajen yamma, ya ratsa dukan duniya, ba ya ko taɓa ƙasa. Akwai ƙaho na gaske a tsakanin idanunsa.

6 Sai ya zo wurin ragon, mai ƙahoni biyu, wanda na gani a tsaye a gāɓar kogi. Bunsurun kuwa ya tasar masa da fushi mai zafi.

7 Na ga ya zo kusa da ragon, ya husata da shi ƙwarai, sai ya gabza wa ragon karo. Ya kakkarya ƙahonin nan nasa biyu. Ƙarfin ragon ya kāsa, ba ya iya kare kansa daga bunsurun. Bunsurun ya buge shi ƙasa ya tattake shi. Ba wanda ya iya ceton ragon daga bunsurun.

8 Sa’an nan bunsurun ya ɗaukaka kansa ƙwarai, amma sa’ad da ya ƙasaita sai babban ƙahon nan ya karye, a maimakonsa sai waɗansu ƙahoni huɗu na gaske suka tsiro suna fuskantar kusurwa huɗu.

9 Wani ƙaramin ƙaho kuma ya tsiro daga cikin ɗayansu, ya yi girma ya ƙasaita ƙwarai. Ya nuna ikonsa wajen gabas, da wajen kudu, da wajen ƙasa mai albarka.

10 Ya ƙasaita, har ya kai cikin rundunar sama. Ya jawo waɗansu taurari zuwa ƙasa, ya tattake su.

11 Ya ɗaukaka kansa, har ya mai da kansa daidai da shugaban runduna. Ya hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum ga Sarkin sarakuna, ya kuma rushe masa wuri mai tsarki.

12 Saboda zunubi sai aka ba da runduna duk da hadayar ƙonawa ta yau da kullum ga ƙahon. Sai ya yi watsi da gaskiya, ya yi abin da ya ga dama, ya kuwa yi nasara.

13 Sai na ji wani mai tsarki yana magana, wani kuma mai tsarki ya tambayi wancan mai tsarki da ya yi magana, ya ce, “Sai yaushe za a tsai da abubuwan da suke a wahayin nan, wato hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum, da zunubin da yake lalatarwa, da ba da wuri mai tsarki ga rundunar mutane don a tattake?”

14 Ya ce mini, “Sai an yi kwana dubu biyu da ɗari uku, sa’an nan za a mai da wuri mai tsarki daidai da yadda yake a dā.”

Jibra’ilu Ya Fasarta Wahayin

15 Sa’ad da ni Daniyel, na ga wahayin, ina so in gane, sai ga wani kamar mutum ya tsaya a gabana.

16 Na kuma ji muryar mutum a gāɓar Ulai ta ce, “Jibra’ilu, ka sa wannan mutum ya gane wahayin.”

17 Don haka sai ya zo kusa da inda nake tsaye. Da ya zo sai na firgita, na faɗi rubda ciki.

Amma ya ce mini, “Ɗan mutum, wannan wahayi yana a kan lokaci na ƙarshe ne.”

18 Sa’ad da yake magana da ni, sai barci mai nauyi ya kwashe ni da nake kwance rubda ciki, amma sai ya taɓa ni, ya tashe ni tsaye.

19 Ya ce mini, “Zan sanar da kai abubuwan banhaushi, da za su faru nan gaba, gama wahayin ya shafi ƙayyadadden lokaci na ƙarshe.

20 “Ragon nan mai ƙaho biyu da ka gani, sarakunan Mediya ne da na Farisa.

21 Bunsurun kuwa Sarkin Hellas ne. Babban ƙahon nan da yake tsakanin idanunsa shi ne sarki na farko.

22 Ƙahoni huɗu da suka tsiro bayan karyewar na farin, sarakuna huɗu ne da za su fito daga cikin al’ummarsa, amma ba za su sami iko irin nasa ba.

23 “A wajen ƙarshen mulkinsu, sa’ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai izgili, mayaudari, zai fito.

24 Zai ƙasaita, amma ba ta wurin ikon kansa ba. Zai yi mummunar hallakarwa. Zai hallaka manyan mutane, da tsarkaka. Zai yi nasara cikin abin da zai yi.

25 Ta wurin mugun wayonsa zai sa cin hanci ya haɓaka. Zai ɗaukaka kansa a ransa. Zai hallaka mutane da yawa, ba zato ba tsammani, har ma zai tasar wa Sarkin sarakuna, amma za a hallaka shi ba ta hannun mutum ba.

26 Wannan wahayi na kwanaki wanda aka nuna maka gaskiya ne, asiri ne kuma, kada ka faɗa, gama zai daɗe kafin a yi.”

27 Ni Daniyel kuwa na siƙe, na yi ciwo, har na kwanta ‘yan kwanaki, sa’an nan na tashi na ci gaba da aikin sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ban gane shi ba.