GAL 2

Sauran Manzanni Sun Karɓi Bulus

1 Bayan shekara goma sha huɗu na sāke komawa Urushalima tare da Barnaba, na kuma ɗauki Titus.

2 Da umarnin wahayi ne na tafi, har na rattaba musu bisharar da nake yi a cikin al’ummai, amma a keɓance a gaban waɗansu shugabannin ikkilisiya, kada himmar da nake yi, ko wadda na riga na yi, ta zamana ta banza ce.

3 Kai, ko Titus ma da yake a tare da ni, ba a tilasta masa yin kaciya ba, ko da yake shi Bahelene ne.

4 Maganar nan ta tashi saboda ‘yan’uwan ƙaryar nan ne, da aka shigo da su a asirce, waɗanda suka saɗaɗo su yi ganganen ‘yancinmu da muke da shi ta wurin Almasihu Yesu, don dai su sa mu bauta.

5 Amma ko kaɗan ba mu sakar musu ba, ko da taƙi, domin gaskiyar bishara tă zaune muku.

6 Waɗanda kuma aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne (ko su wane ne, ai, duk ɗaya ne a guna, domin Allah ba ya tāra), ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙare ni da kome ba.

7 Amma da suka ga an amince mini in yi wa marasa kaciya bishara, kamar yadda aka amince wa Bitrus ya yi wa masu kaciya bishara,

8 (domin shi da ya yi aiki a zuciyar Bitrus ya sa shi manzo ga masu kaciya, shi ne kuma ya yi aiki a zuciyata, ya sa ni manzo ga al’ummai),

9 sai Yakubu da Kefas da Yahaya, su da suke shahararrun ginshiƙan ikkilisiya, da suka ga alherin da Allah ya yi mini, sai suka karɓe mu, ni da Barnaba, hannu biyu biyu, domin mu mu je wurin al’ummai, su kuwa gun masu kaciya.

10 Sai dai kuma suna so mu tuna matalauta, wannan kuwa ko dā ma ina da himmar yi ƙwarai.

Bulus ya Tsawata wa Bitrus a Antakiya

11 Amma da Kefas ya zo Antakiya, sai na tsaya masa fuska da fuska don laifinsa a fili yake.

12 Don kafin waɗansu su zo daga wurin Yakubu, yakan ci abinci da al’ummai. Amma da suka zo, ya janye jiki ya ware kansa, yana tsoron ɗariƙar masu kaciyar nan.

13 Haka ma sauran Yahudawa masu bi suka nuna fuska biyu kamarsa, ko da Barnaba ma sai da suka ciwo kansa da munafuncinsu.

14 Amma da na ga dai ba sa bin gaskiyar bishara sosai, na ce wa Kefas a gaban idon kowa, “Kai da kake Bayahude, in ka bi al’adar al’ummai ba ta Yahudawa ba, yaya kake tilasta wa al’ummai su bi al’adar Yahudawa?

Ceton Yahudawa duk da Al’ummai ta wurin Bangaskiya

15 “Mu da aka haifa Yahudawa, ba al’ummai masu zunubi ba,

16 da yake mun sani mutum ba ya samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari’a, sai dai ta wurin gaskatawa ga Yesu Almasihu kaɗai, mu ma mun gaskata da Almasihu Yesu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya ga Almasihu, ba ta wurin bin Shari’a ba, don ba ɗan adam ɗin da zai sami kuɓuta ga Allah ta hanyar bin Shari’a.

17 In kuwa ya zamana, sa’ad da muke neman kuɓuta ga Allah ta wurin Almasihu, an tarar har mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, Almasihu yana hidimar zunubi ne? A’a, ko kusa!

18 Amma in na sāke ginin abin da dā na rushe, na tabbata mai laifi ke nan.

19 Gama ni ta wurin Shari’a matacce ne ga Shari’a domin in rayu ga Allah.

20 An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma nake a raye ba, Almasihu ne yake a raye a cikina. Rayuwar nan kuma da nake yi ta jiki, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina.

21 Ba na tozarta alherin Allah. Don da ta wurin bin Shari’a ake samun adalcin Allah, ashe, da Almasihu ya mutu a banza ke nan.”