HAG 1

An Zuga Mutane Su Gina Haikali

1 A rana ta fari ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar sarki Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Haggai, cewa ya yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.

2 Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Mutanen nan suna cewa lokaci bai yi ba tukuna da za a sāke gina Haikalin Ubangiji.”

3 Ubangiji kuwa ya yi magana da annabi Haggai ya ce,

4 “Ashe, lokaci ya yi da za ku zauna a ɗakunan da kuka yi wa rufin katako, amma Haikalin nan yana zaman kufai?

5 Yanzu, ni Ubangiji Mai Runduna na ce, ku lura da al’amuranku!

6 Kun yi shuka da yawa, kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha ruwa, amma bai kashe muku ƙishi ba. Kun sa tufafi, amma ba wanda ya ji ɗumi. Wanda yake karɓar albashi kuwa, sai ka ce yana sawa a huɗajjen aljihu.”

7 Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ku lura da al’amuranku!

8 Ku haura zuwa kan tuddai, ku kawo itace don ku gina Haikalina, in ji daɗinsa, a kuma ɗaukaka ni.

9 “Kun sa zuciya za ku sami da yawa, sai kuka sami kaɗan. Sa’ad da kuma kuka kawo shi gida, sai na hurar da shi. Me ya sa haka? Saboda Haikalina da yake zaman kufai, amma ko wannenku yana fama da ginin gidansa.

10 Domin haka sama ta ƙi saukar da raɓa, ƙasa kuma ta ƙi ba da amfani.

11 Na kawo fari a kan ƙasa, da kan tuddai, da kan hatsi, da kan ‘ya’yan inabi, da kan ‘ya’yan zaitun, da kan dukan abin da yake tsirowa daga ƙasa, da kan mutane, da kan dabbobi, da kan ayyukansu.”

12 Zarubabel ɗan Sheyaltiyel kuwa, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu, suka kuma yi biyayya da maganar annabi Haggai, kamar yadda Ubangiji Allahnsu ya faɗa masa. Mutane kuwa suka yi tsoron Ubangiji.

13 Sai Haggai, manzon Ubangiji, ya faɗa wa mutane maganar Ubangiji, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Ni Ubangiji ina tare da ku.’ ”

14 Ubangiji kuwa ya zuga zuciyar Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da zuciyar Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da zuciyar dukan sauran mutane. Suka zo, suka fara aikin Haikalin Ubangiji Allahnsu Mai Runduna

15 a ranar ashirin da huɗu ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus.