IRM 17

Zunubin Yahuza Ya Yi Kanta

1 Ubangiji ya ce, “An rubuta zunubin mutanen Yahuza da alƙalamin ƙarfe, mai bakin yakutu. An zana shi a allon zuciyarsu da a zankayen bagadansu.

2 Idan sun tuna da ‘ya’yansu haka sun tuna da bagadansu da Ashtarot ɗinsu a gindin itatuwa masu duhuwa da kan tuddai masu tsayi.

3 Ku mazauna a tsaunuka da cikin saura, zan ba da dukiyarku da wadatarku ganima saboda dukan zunuban da kuka yi a dukan ƙasar.

4 Za ku rasa abin da yake hannunku daga cikin gādon da na ba ku. Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama da fushina wuta ta kama wadda za ta yi ta ci har abada.”

5 Ubangiji ya ce,

“La’ananne ne mutumin da yake

dogara ga mutum,

Wanda jiki ne makaminsa,

Wanda ya juya wa Ubangiji baya,

6 Gama yana kama da sagagi a

hamada,

Ba zai ga wani abu mai kyau yana

zuwa ba.

Zai zauna a busassun wuraren

hamada,

A ƙasar gishiri, inda ba kowa.

7 “Mai albarka ne mutumin da yake

dogara ga Ubangiji,

Wanda Ubangiji ne madogararsa.

8 Shi kamar itace ne wanda ake dasa a

bakin rafi

Wanda yake miƙa saiwoyinsa zuwa

cikin rafin,

Ba zai ji tsoron rani ba,

Kullum ganyensa kore ne,

Ba zai damu a lokacin fari ba,

Ba zai ko fasa yin ‘ya’ya ba.

9 “Zuciya ta fi kome rikici,

Cuta gare ta matuƙa,

Wa zai san kanta?

10 Ni Ubangiji nakan bincike tunani,

In gwada zuciya,

Domin in sāka wa kowane mutum

gwargwadon al’amuransa,

Da kuma gwargwadon ayyukansa.

11 “Kamar makwarwar da ta kwanta

kan ƙwan da ba ita ta nasa ba,

Haka yake ga wanda ya sami dukiyar

haram,

Yana gaɓar ƙarfinsa, za ta rabu da

shi,

A ƙarshe zai zama wawa.”

12 Kursiyi mai daraja,

Da aka sa a bisa tun daga farko,

Wurin ke nan inda Haikalinmu

yake.

13 Ya Ubangiji, begen Isra’ila,

Duk waɗanda suka rabu da kai, za su

sha kunya.

Waɗanda suka ba ka baya a duniya

za a rubuta su

Domin sun rabu da Ubangiji,

maɓuɓɓugar ruwan rai.

Irmiya Ya Roƙi Ubangiji ya Kiyaye Shi

14 Ubangiji, ka warkar da ni, zan kuwa

warke,

Ka cece ni, zan kuwa cetu,

Gama kai ne abin yabona.

15 Ga shi, suna ce mini,

“Ina maganar Ubangiji take?

Ta zo mana!”

16 Amma ni ban yi gudun zaman

makiyayi a gabanka ba,

Ban kuma so zuwan ranar bala’i ba,

Ka kuwa sani.

Abin da ya fito daga bakina kuwa,

A bayyane yake gare ka.

17 Kada ka zamar mini abin razana,

Kai ne mafakata cikin ranar masifa,

18 Bari waɗanda suka tsananta mini su

sha kunya,

Amma kada ka bar ni in kunyata.

Bari su tsorata,

Amma kada ka bar ni in tsorata.

Ka aukar musu da ranar masifa,

Ka hallaka su riɓi biyu!

A kan Kiyaye Ranar Asabar

19 Haka Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi ka tsaya a ƙofar Biliyaminu, wadda sarakunan Yahuza suke shiga da fita ta cikinta, ka kuma tafi dukan ƙofofin Urushalima.

20 Ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuza, da dukan Yahuza, da dukan mazaunan Urushalima, waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi.

21 Haka Ubangiji ya ce, ku yi hankali saboda rayukanku, kada ku ɗauki kaya a ranar Asabar, ko ku shigar da kowane abu ta ƙofofin Urushalima.

22 Kada ku ɗauki kaya, ku fita da shi daga gidajenku a ranar, ko ku yi kowane irin aiki, amma ku kiyaye ranar Asabar da tsarki, kamar yadda na umarci kakanninku.’

23 Amma duk da haka ba su kasa kunne, ko su mai da hankali ba. Amma suka taurare don kada su ji, su karɓi koyarwa.

24 “ ‘Amma idan kun kasa kunne gare ni,’ in ji Ubangiji, ‘ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofin wannan birni a ranar Asabar ba, amma kuka kiyaye ranar Asabar da tsarki, ba ku yi aiki a cikinta ba,

25 sa’an nan ne sarakuna waɗanda za su zauna a kan gadon sarautar Dawuda, za su shiga ta ƙofofin wannan birni, suna hawan karusai, da dawakai, su da sarakunansu, da jama’ar Yahuza da mazaunan Urushalima. Za a zauna a wannan birni har abada.

26 Mutane za su zo daga biranen Yahuza da wuraren da yake kewaye da Urushalima, daga ƙasar Biliyaminu, da ta Shefela, da ta ƙasar tuddai, da kuma ta Negeb, suna kawo hadayu na ƙonawa da sadakoki, da hadayu na sha, da na turare, za su kuma kawo hadayu na godiya a Haikalin Ubangiji.

27 Amma idan ba ku kasa kunne gare ni ba, ba ku kuwa kiyaye ranar Asabar da tsarki ba, kun kuma ɗauki kaya kun shiga ta ƙofofin Urushalima a ranar Asabar, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wuta. Za ta kuwa cinye fādodin Urushalima, ba kuwa za ta kasu ba.’ ”