IRM 19

Fasasshen Tulu

1 Ubangiji ya ce mini, “Tafi ka sayo tulu a wurin maginin tukwane. Sa’an nan kuma ka ɗauki waɗansu daga cikin dattawan jama’a, da waɗansu manyan firistoci,

2 ku tafi kwarin ɗan Hinnom na mashigin Ƙofar Kasko, ka yi shelar maganar da zan faɗa maka a can.

3 Za ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ya ku sarakunan Yahuza da mazaunan Urushalima, Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce, zan kawo wata irin masifa a wannan wuri, wanda duk ya ji, kunnuwansa za su kaɗa.

4 Ga shi, mutanen nan sun rabu da ni, sun ƙazantar da wannan wuri sun ƙona wa gumaka turare, waɗanda su, ko kakanninsu, ko sarakunan Yahuza, ba su san su ba. Sun cika wannan wuri da jinin marasa laifi.

5 Sun gina wa Ba’al masujadai don su miƙa masa ‘ya’yansu maza hadayar ƙonawa, abin da ban umarta ba, ban kuma ba da izni ba, ban ma yi tunanin haka ba.

6 Saboda haka rana tana zuwa da ba za a ƙara ce da wannan wuri Tofet, ko kwarin ɗan Hinnom ba, amma za a ce da shi Kwarin Kisa.

7 A wannan wuri zan wofinta dabarun Yahuza da na Urushalima, zan sa a kashe jama’arsu da takobi, a gaban abokan gābansu, ta hannun waɗanda suke neman ransu. Zan ba da gawawwakinsu su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.

8 Zan mai da wannan birni abin ƙyama, abin raini, dukan wanda ya wuce wurin zai yi mamaki, ya yi tsaki saboda dukan masifun da suka auka wa birnin.

9 Zan sa su ci naman ‘ya’yansu mata da maza. Kowa zai ci naman maƙwabcinsa cikin damuwa a lokacin da za a kewaye su da yaƙi, zai sha wahala daga wurin abokan gābansa da waɗanda suke neman ransa.’

10 “Sa’an nan sai ka fasa tulun a gaban mutanen da suka tafi tare da kai,

11 ka kuwa ce musu, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, haka zai farfasa jama’a, da wannan birni kamar yadda aka fashe tulun maginin tukwanen, ba kuwa zai gyaru ba. Za a binne mutane a Tofet domin za a rasa makabartar da za a binne su.

12 Haka zai yi wa wurin nan da mazauna cikinsa, ya mai da birnin nan kamar Tofet.

13 Gidajen Urushalima da gidajen sarakunan Yahuza da dukan gidaje waɗanda a kan rufinsu aka ƙona wa rundunar sararin sama turare, aka zuba wa gumaka hadayu na sha, za su ƙazantu kamar Tofet.’ ”

14 Sa’an nan Irmiya ya komo daga Tofet, inda Ubangiji ya aike shi don ya yi annabci, sai ya tsaya a fili na Haikalin Ubangiji, ya ce wa dukan jama’a,

15 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Ga shi, ina aukar wa wannan birni da dukan garuruwansa dukan masifu da na ambata a kansa, domin sun taurare zukatansu, sun ƙi jin maganata.’ ”