IRM 27

Irmiya Ya Ɗaura Karkiyar Shanu a Wuyansa

1 A farkon sarautar Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi wa Irmiya magana.

2 Ya ce ya yi wa kansa karkiyar itace da maɗaurai na fata ya ɗaura su a wuyansa,

3 ya aika da magana zuwa ga Sarkin Edom, da Sarkin Mowab, da Sarkin Ammon, da Sarkin Taya, da Sarkin Sidon ta hannun manzannin da suka zo Urushalima wurin Zadakiya Sarkin Yahuza.

4 Ubangiji ya ce wa Irmiya ya umarce su, su tafi, su faɗa wa iyayengijinsu cewa, “In ji Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ga abin da za ku faɗa wa iyayengijinku,

5 ‘Ni ne da ikona da ƙarfina na yi duniya, da mutane, da dabbobi waɗanda suke cikinta. Nakan ba da ita ga wanda na ga dama.

6 Yanzu fa na ba bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila, dukan ƙasashen nan, na kuma ba shi namomin jeji su bauta masa.

7 Dukan ƙasashe za su bauta masa, da shi da ɗansa, da jikansa, har lokacin da na sa ƙasar ta fāɗi, sa’an nan al’ummai masu yawa da manyan sarakuna za su bautar da shi.

8 “ ‘Amma idan wata al’umma ko wani mulki bai yarda ya bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila ba, bai kuma ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyansa ba, zan hukunta wa wannan al’umma da takobi, da yunwa, da annoba, har in hallaka ta, ta hannun Nebukadnezzar, ni Ubangiji na faɗa.

9 Saboda haka kada ku saurari annabawanku, da masu duba, da masu mafarkai, da matsubbata, ko masu sihiri waɗanda suka ce muku ba za ku bauta wa Sarkin Babila ba.

10 Suna yi muku annabcin ƙarya ne, za su kuwa sa a kai ku wata ƙasa nesa da ƙasarku. Zan kore ku, za ku kuwa lalace.

11 Amma duk al’ummar da za ta ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanta, ta kuma bauta masa, zan bar ta a ƙasarta, ta yi noman ƙasarta, ta zauna a ciki, ni Ubangiji na faɗa.’ ”

12 Sai na faɗa wa Zadakiya Sarkin Yahuza wannan magana cewa, “Ka ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyanka, ka bauta masa, shi da mutanensa, don ka rayu!

13 Don me kai da mutanenka za ku mutu ta takobi, da yunwa, da annoba, kamar yadda Ubangiji ya yi magana a kan kowace al’umma da ta ƙi ta bauta wa Sarkin Babila?

14 Kada ka kasa kunne ga maganar annabawan da suke ce maka, ‘Ba za ku bauta wa Sarkin Babila ba.’ Annabcin ƙarya suke yi muku.

15 Gama Ubangiji ya ce shi bai aike su ba, annabcin ƙarya suke yi muku da sunansa, don ya kore ku, ku halaka, ku da annabawan da suke yi muku annabci.”

16 Sa’an nan na faɗa wa firistoci da jama’a cewa, “In ji Ubangiji, kada ku kasa kunne ga abin da annabawanku suke muku annabci cewa, ‘Ba da daɗewa ba za a komo da kayan Haikalin Ubangiji daga Babila.’ Ƙarya ce suke yi muku.

17 Kada ku ji su, amma ku bauta wa Sarkin Babila don ku rayu! Don me birnin nan zai zama kufai?

18 Idan su annabawa ne, idan kuwa Ubangiji yana magana da su, to, bari su roƙi Ubangiji Mai Runduna kada a tafi Babila da kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima.

19 Gama Ubangiji Mai Runduna ya faɗi zancen ginshiƙai, da babbar kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,

20 wato waɗanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila bai kwashe ba a lokacin da ya tafi da Yekoniya ɗan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, da dukan dattawan Yahuza da na Urushalima zuwa bauta a Babila.

21 “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra’ila, ya faɗa a kan kayayyakin da suka ragu a Haikalin Ubangiji, da a fādar Sarkin Yahuza, da a Urushalima,

22 ‘Za a kwashe su a kai Babila, a can za su kasance har lokacin da zan sāke kulawa da su. Sa’an nan ne zan komo da su, in maishe su a wannan wuri.’ ”