IRM 38

An Fitar da Irmiya daga Rijiya Marar Ruwa

1 Shefatiya ɗan Mattan, da Gedaliya ɗan Fashur, da Yehukal ɗan Shelemiya, da Fashur ɗan Malkiya, suka ji maganar da Irmiya yake faɗa wa dukan mutane cewa,

2 “Ubangiji ya ce wanda ya zauna a wannan birni zai mutu da takobi, da yunwa, da annoba, amma wanda ya fita ya je wurin Kaldiyawa zai rayu, zai sami ransa kamar ganimar yaƙi.

3 Gama Ubangiji ya ce, hakika za a ba da wannan birni a hannun rundunar sojojin Sarkin Babila su ci shi.”

4 Sarakunan suka ce wa sarki, “A kashe mutumin nan, gama yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran jama’a duka ta wurin irin maganganun da yake faɗa musu. Gama wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan jama’a sai dai wahala yake nemar musu.”

5 Sarki Zadakiya ya ce, “Ai, ga shi nan a hannunku, gama sarki ba zai yi abin da ba ku so ba.”

6 Sai suka ɗauki Irmiya suka saka shi a rijiyar Malkiya ɗan sarki, wadda take gidan waƙafi. Suka zurara Irmiya a ciki da igiya. Ba ruwa a rijiyar, sai dai lāka, Irmiya ya nutse cikin lākar.

7 Ebed-melek, bābā, mutumin Habasha, wanda yake a gidan sarki, ya ji labari sun saka Irmiya a rijiya. A lokacin nan, sarki yana zaune a Ƙofar Biliyaminu.

8 Sai Ebed-melek ya fita, ya tafi gaban sarki, ya ce masa,

9 “Ya maigirma sarki, waɗannan mutane sun yi mugun abu da suka saka annabi Irmiya cikin fijiya, Zai mutu can da yunwa, gama ba sauran abinci a birnin.”

10 Sa’an nan sarki ya umarci Ebedmelek, mutumin Habasha, ya tafi da mutum talatin su tsamo annabi Irmiya daga cikin rijiyar kafin ya mutu.

11 Sai Ebed-melek ya tafi da mutanen, ya kuma tafi gidan sarki, a ɗakin ajiya, ya kwaso tsummoki da tsofaffin tufafi, ya zurara wa Irmiya a rijiyar.

12 Ebedmelek, mutumin Habasha, ya ce wa Irmiya ya sa tsummokin da tsofaffin tufafin a hammatarsa, ya zarga igiya, Irmiya kuwa ya yi yadda aka ce masa.

13 Suka jawo Irmiya da igiyoyi, suka fito da shi daga rijiya. Irmiya kuwa ya zauna a gidan waƙafi.

Zadakiya Ya Nemi Shawarar Irmiya

14 Sarki Zadakiya ya aika a kirawo annabi Irmiya. Ya tafi ya sadu da Irmiya a ƙofa ta uku ta Haikalin Ubangiji. Sarki kuwa ya ce wa Irmiya, “Zan yi maka tambaya, kada kuwa ka ɓoye mini kome.”

15 Irmiya kuwa ya ce wa Zadakiya, “Idan na faɗa maka gaskiya za ka kashe ni, idan kuma na ba ka shawara, ba za ka karɓi shawarata ba.”

16 Sarki Zadakiya ya rantse wa Irmiya a ɓoye, ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda yake ba mu rai, ba zan kashe ka ko in bashe ka a hannun waɗannan mutane da suke neman ranka ba.”

17 Irmiya ya ce wa Zadakiya, “Haka Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra’ila ya ce, idan ka miƙa wuya ga sarakunan Sarkin Babila, za ka tsira, ba kuwa za a ƙone birnin da wuta ba, kai da gidanka za ku tsira.

18 Amma idan ba ka miƙa wuya ga sarakunan Sarkin Babila ba, to, za a ba da wannan birni a hannun Kaldiyawa, za su ƙone shi da wuta. Kai kuma ba za ka tsira daga hannunsu ba.”

19 Sarki Zadakiya ya ce wa Irmiya, “Ina jin tsoron Yahudawa waɗanda suka gudu zuwa wurin Kaldiyawa. Kila a bashe ni a hannunsu, su ci mutuncina.”

20 Irmiya kuwa ya ce masa, “Ba za a bashe ka gare su ba. Kai dai ka yi biyayya da maganar Ubangiji wadda nake faɗa maka yanzu. Yin haka zai fi maka amfani, za ka tsira.

21 Amma idan ka ƙi miƙa wuya, to, ga abin da Ubangiji ya nuna mini a wahayi.

22 Ga shi, dukan matan da suka ragu a gidan Sarkin Yahuza, za a kai su wurin sarakunan Sarkin Babila, suna cewa,

‘Aminanka sun ruɗe ka,

Sun rinjaye ka.

Yanzu sun ga ƙafafunka sun nutse

cikin laka,

Sai suka rabu da kai.’

23 “Dukan matanka da ‘ya’yanka za a kai su wurin Kaldiyawa, kai kanka kuma ba za ka tsere musu ba, amma Sarkin Babila zai kama ka, birnin kuma za a ƙone shi da wuta.”

24 Sai Zadakiya ya ce wa Irmiya, “Kada ka bar wani ya san wannan magana, kai kuwa ba za a kashe ka ba.

25 Idan sarakuna suka ji, wai na yi magana da kai, in suka zo wurinka, suka ce, ‘Ka faɗa mana abin da ka faɗa wa sarki da abin da sarki ya faɗa maka, kada ka ɓoye mana kome mu kuwa ba za mu kashe ka ba.’

26 Sai ka ce musu, ‘Na roƙi sarki da ladabi don kada ya mai da ni a gidan Jonatan, don kada in mutu a can.’ ”

27 Dukan sarakuna suka tafi wurin Irmiya suka tambaye shi. Shi kuwa ya amsa musu yadda sarki ya umarce shi. Sai suka daina magana da shi, tun da yake ba wanda ya ji maganar da ya yi da sarki.

28 Irmiya kuwa ya yi zamansa a gidan waƙafi har ranar da aka ci Urushalima da yaƙi.