IRM 40

Irmiya da waɗanda Suka Ragu Sun Zauna tare da Gedaliya

1 Ubangiji ya yi magana da Irmiya bayan da Nebuzaradan shugaban matsara ya sake shi daga Rama, sa’ad da ya yi masa ƙuƙumi tare da waɗanda aka kwaso daga Urushalima da Yahuza, za su Babila.

2 Shugaban matsara ya ware Irmiya, sa’an nan ya ce masa, “Ubangiji Allahnka ne ya hurta wannan masifa a kan wurin nan.

3 Ga shi kuwa, ya yi kamar yadda ya faɗa, domin kun yi wa Ubangiji zunubi, ba ku yi biyayya da muryarsa ba, don haka wannan masifa ta auko muku.

4 Yau na kwance ƙuƙumin da yake a wuyanka, idan ka ga ya fi maka kyau, ka zo mu tafi tare zuwa Babila, to, sai ka zo, zan lura da kai da kyau, amma idan ba ka ga haka ya yi maka daidai ba, to, kada ka bi ni. Ga dukan ƙasa shimfiɗe a gabanka, ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.”

5 Amma Irmiya bai tafi ba, sai Nebuzaradan ya ce masa, “Ka koma wurin Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan, wanda Sarkin Babila ya sa ya zama mai mulkin garuruwan Yahuza, ka zauna tare da shi da mutanen, ko kuwa ka tafi duk inda ka ga ya fi maka kyau.” Sai ya ba Irmiya abinci da kyauta, sa’an nan ya sallame shi.

6 Irmiya kuwa ya tafi wurin Gedaliya ɗan Ahikam, a Mizfa, ya zauna tare da shi da mutanen da suka ragu a ƙasar.

7 Sa’ad da shugabannin sojoji waɗanda suke a karkarar Yahudiya tare da mutanensu, suka ji labari Sarkin Babila ya sa Gedaliya ɗan Ahikam ya zama mai mulkin ƙasar, a kan matalauta, wato mata da maza, da yara na ƙasar, waɗanda ba a kwashe su zuwa bautar talala a Babila ba,

8 sai shugabannin, wato Isma’ilu ɗan Netaniya, da Yohenan da Jonatan, ‘ya’yan Kareya, da Seraiya ɗan Tanhumet, da ‘ya’yan Efai, mutumin Netofa, da Yazaniya ɗan mutumin Ma’aka suka tafi tare da mutanensu zuwa wurin Gedaliya a Mizfa.

9 Gedaliya ɗan Ahikam, jikan shafan ya rantse musu da mutanensu, ya ce, “Kada ku ji tsoron bauta wa Kaldiyawa, ku yi zamanku a ƙasar, ku bauta wa Sarkin Babila, za ku kuwa zauna lafiya.

10 Amma ni zan zauna a Mizfa, in zama wakilinku a wurin Kaldiyawa waɗanda za su zo wurinmu. Ku tattara inabi, da ‘ya’yan itatuwa na kaka, da man zaitun, ku tanada su a gidajenku, ku zauna a garuruwan da kuka ci.”

11 Haka kuma Yahudawan da suke a Mowab, da Ammon, da Edom, da kuma sauran ƙasashe suka ji, cewa Sarkin Babila ya bar waɗansu mutane a Yahuza, ya kuma shugabantar da Gedaliya ɗan Ahikam, jikan Shafan a kansu,

12 sai dukan Yahudawa suka koma daga inda aka kora su zuwa ƙasar Yahuza. Suka zo wurin Gedaliya a Mizfa. Suka tattara ruwan inabi da ‘ya’yan itatuwa na kaka da yawa.

Maƙarƙashiyar Isma’ilu gāba da Gedaliya

13 Yohenan ɗan Kareya kuwa, tare da dukan shugabannin sojojin da suke cikin sansani a karkara, suka zo wurin Gedaliya a Mizfa.

14 Suka ce masa, “Ko ka sani Ba’alis Sarkin Ammonawa ya aiko Isma’ilu ɗan Netaniya ya kashe ka?” Amma Gedaliya ɗan Ahikam, bai gaskata su ba.

15 Sai Yohenan ɗan Kareya ya yi magana da Gedaliya a Mizfa a asirce ya ce, “Ka bar ni in tafi in kashe Isma’ilu ɗan Netaniya, ba wanda zai sani. Don me shi zai kashe ka, ya watsa dukan Yahudawan da suke tare da kai, har sauran Yahudawan da suka ragu su halaka.”

16 Amma Gedaliya ɗan Ahikam ya ce wa Yohenan ɗan Kareya, “Kada ka kuskura ka yi wannan abu, gama ƙarya ce kake yi wa Isma’ilu.”