ISH 12

Waƙar Godiya

1 Rana tana zuwa sa’ad da jama’a za su raira waƙa, su ce,

“Ina yabonka ya Ubangiji! A dā ka yi fushi da ni,

Amma yanzu kana yi mini ta’aziyya, ba za ka ƙara yin fushi da ni ba.

2 Allah ne Mai Cetona,

Zan dogara gare shi, ba zan ji tsoro ba.

Ubangiji ne yake ba ni iko da ƙarfi,

Shi ne Mai Cetona.”

3 Kamar yadda ruwan daɗi yake sa mai jin ƙishirwa farin ciki,

Haka nan jama’ar Allah suke farin ciki sa’ad da ya cece su.

4 A wannan rana jama’a za su raira waƙa, su ce,

“Ku yi wa Ubangiji godiya! Ku nemi taimako a gare shi!

Ku faɗa wa dukan sauran al’umma abin da ya aikata!

Ku faɗa musu irin girman da yake da shi!

5 Ku raira waƙa ga Ubangiji, saboda manyan ayyuka da ya aikata.

Bari dukan duniya ta ji labarin.

6 Bari dukan waɗanda suke zaune a Sihiyona su yi sowa su raira waƙa!

Gama Mai Tsarki, Allah na Isra’ila, mai girma ne,

Yana zaune tare da mutanensa.”