ISH 15

Annabci a kan Mowab

1 Wannan shi ne jawabi a kan Mowab.

Biranen Ar da Kir, an hallaka su dare ɗaya, ƙasar ta yi tsit, ba kowa.

2 Mutanen Dibon sun hau kan tuddai don su yi kuka a matsafarsu. Mutanen Mowab suna kuka da baƙin ciki saboda biranen Nebo da Medeba, sun aske kawunansu da gyammansu saboda baƙin ciki.

3 Mutane a tituna sun sa tsummoki a jikinsu, suka taru a filayen taruwa na birni da a kan rufin ɗakuna, sai makoki suke suna ta kuka.

4 Mutanen Heshbon da na Eleyale suka yi kuka da ƙarfi, har ana iya jin kukansu daga Yahaza. Har mayaƙa ma sun yi rawar jiki, zuciyarsu ta karai.

5 Zuciyata ta yi kuka ainun saboda Mowab! Mutane sun gudu zuwa cikin garin Zowar. Waɗansu sun haura zuwa Luhit, suna tafe suna kuka, waɗansu sun tsere zuwa Horonayim, suna hargowa saboda baƙin ciki.

6 Rafin Nimra ya ƙafe, ciyawar da take gefensa ta bushe, ba sauran wani ɗanyen abu.

7 Mutane sun haye kwarin Larabawa, suna ƙoƙari su tsere da dukan abin da suka mallaka.

8 A ko’ina a kan iyakokin Mowab, sai ƙugin kukansu ake ji. Ana kuwa ji daga garuruwan Eglayim da Biyer-elim.

9 A garin Dibon, kogin ya yi ja wur da jini, Allah kuwa ya tanada wa mutanen wurin abin da ya fi wannan muni. Hakika za a yi wa duk wanda ya ragu a Mowab mummunan kisa.