ISH 18

Annabci a kan Habasha

1 A hayin kogunan Habasha akwai wata ƙasa inda ake jin amon fikafikai.

2 Daga waccan ƙasar wakilai sukan gangaro daga Kogin Nilu a cikin jiragen ruwa da aka yi da iwa. Ku koma gida, ku manzanni masu gaggawa! Ku kai saƙo ƙasarku, can a mafarin Kogin Nilu, zuwa ga al’ummarku mai ƙarfi mai iko, zuwa ga dogayen mutanenku masu sulɓin jiki, waɗanda ake jin tsoronsu ko’ina a duniya.

3 Kowane mutum da yake a duniya ya kasa kunne, kowannen da yake zaune a duniya, ya duba tutar, alama da za a ɗaga sama a ƙwanƙolin duwatsu, ya kasa kunne ga busar ƙaho!

4 Ubangiji ya ce mini “Zan duba daga samaniya a hankali kamar yadda raɓa take saukowa a natse da gumin dare a lokacin girbi, hasken rana kuma a yini.

5 Kafin a tattara ‘ya’yan inabi, sa’ad da furanni duka suka karkaɗe, ‘ya’yan inabi suna ta nuna, haka magabta za su hallaka Habasha a sawwaƙe kamar yadda ake faffalle rassan kurangar inabi da wuƙa.

6 Za a bar gawawwakin sojojinsu a fili domin tsuntsaye da namomin jeji su zama abincin tsuntsaye da bazara, abincin namomin jeji kuma a lokacin sanyi.”

7 A wannan lokaci Ubangiji Mai Runduna zai karɓi hadayu daga wannan ƙasa, a mafarin Kogin Nilu, wato wannan ƙaƙƙarfar al’umma mai iko, waɗannan dogayen mutane masu sulɓin jiki, waɗanda ake jin tsoronsu ko’ina a duniya. Za su zo Dutsen Sihiyona, inda ake yi wa Ubangiji Mai Runduna sujada.