ISH 22

Annabci a kan Kwarin Wahayi

1 Wannan shi ne jawabi a kan kwarin wahayi.

Me yake faruwa? Me ya sa jama’ar birni duka suke biki a kan rufin gidaje?

2 Birnin duka ya ruguntsume, cike da hayaniya da tashin hankali.

Mutanenku da suka mutu ba su mutu suna yaƙi ba.

3 Dukan shugabanninku sun gudu, an kuwa kama su tun kafin su harba ko kibiya ɗaya. Dukanku da aka iske tare, aka kama ku, ko da yake kuka gudu da nisa.

4 Ni dai ƙyale ni kurum, in yi ta kuka mai zafi. Kada ka yi ƙoƙarin ta’azantar da ni, saboda yawancin mutanena sun mutu.

5 Wannan shi ne lokacin gigicewa, da shan ɗibga, da ruɗewa a cikin kwarin wahayi, Ubangiji Allah Mai Runduna shi ya aukar mana da shi. An ragargaza garukan birninmu har ƙasa, ana jin amsar kuwwar koke-kokenmu na neman taimako a cikin tsaunuka.

6 Sojojin ƙasar Elam sun zo kan dawakai suna rataye da kwari da baka. Sojojin ƙasar Kir sun shirya garkuwoyinsu.

7 Kwarurukansu masu dausayi na ƙasar Yahuza suna cike da karusai, sojoji kuma a kan dawakai suna tsattsaye a ƙofofin Urushalima.

8 Dukan kagaran Yahuza sun rushe.

Sa’ad da wannan ya faru kun kwaso makamai daga cikin taskar makamai.

9-10 Kun ga wuraren da suke bukatar gyara a garukan Urushalima. Ku ƙidaye dukan gidaje da suke cikin Urushalima, kuka rushe waɗansu gidaje don ku sami duwatsun da za ku gyara garukan Urushalima. Don ku tanada ruwa a cikin birnin,

11 kun gina matarar ruwa a jikin garuka don ta tare ruwan da yake gangarowa daga tsohon tafki. Amma ba ku kula da Allah ba, wanda ya shirya wannan tuntuni, wanda kuma ya sa wannan ya kasance.

12 Ubangiji Mai Runduna yana kiranku ku yi kuka, ku yi makoki, ku aske kawunanku, ku sa tsummoki.

13 A maimakon haka sai kuka yi dariya, kuka yi biki. Kuka yanka tumaki da shanu don ku ci, kuka sha ruwan inabi. Kuka ce, “Gara mu ci mu sha! Gobe za mu mutu.”

14 Ubangiji Mai Runduna ya ce mini, “Ko kusa ba za a gafarta musu wannan mugunta ba muddin ransu. Ni, Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

Eliyakim Zai Gāji Shebna

15 Ubangiji Mai Runduna ya faɗa mini in tafi wurin Shebna, mai hidimar iyalin gidan sarki, in ce masa,

16 “Kana tsammani kai wane ne? Wa ya ba ka ‘yancin sassaƙa wa kanka kabari a jikin duwatsu?

17 Yana yiwuwa kai wani abu ne, amma Ubangiji zai ɗauke ka, ya jefar.

18 Zai dunƙule ka kamar ƙwallo ya jefa ka a cikin ƙasar da ta fi girma. A can za ka mutu a kusa da karusan da kake fāriya da su. Abin kunya kake a gidan maigidanka!

19 Ubangiji zai fisshe ka daga maƙaminka, ya ƙasƙantar da kai daga babban matsayinka!”

20 Ubangiji ya ce wa Shebna, “Idan haka ya faru zan aika wa bawana Eliyakim ɗan Hilkiya.

21 Zan sa masa tufafin sarautarka, in ɗaura masa ɗamara, in kuma ba shi dukan ikon da kake da shi. Zai zama kamar uba ga jama’ar Urushalima da na Yahuza.

22 Zan sa shi ya zama sarki mai cikakken iko, na zuriyar Dawuda. Mabuɗan fāda suna hannunsa, abin da ya buɗe, ba mai ikon rufewa. Abin da ya rufe kuwa ba mai ikon buɗewa.

23 Zan kafa shi da ƙarfi a wurin kamar turke, zai kuwa zama sanadin daraja ga dukan iyalinsa.

24 “Amma dukan ‘yan’uwansa da masu dogara gare shi za su zama nawaya a gare shi. Za su rataya gare shi kamar tukwane da ƙoren da aka sa a ragaya!

25 Sa’ad da wannan ya faru ragayar da aka ɗaura tam za ta tsinke ta fāɗo. Wannan shi ne ƙarshen kowane abin da aka sa a cikin ragayar ke nan. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”