ISH 30

Rashin Amfanin Dogara ga Masar

1 Ubangiji ya yi magana, ya ce, “Waɗanda suke mulkin Yahuza sun shiga uku, domin sun tayar mini. Suna aiki da shirye-shiryen da ba ni ne na yi ba, suka sa hannu a kan yarjejeniya gāba da nufina. Suna ta aikata zunubi a kan zunubi.

2 Suna tafiya Masar neman taimako, ba su shawarce ni ba. Suna so Masar ta kāre su, saboda haka suka sa dogararsu ga Sarkin Masar.

3 Amma sarkin zai rasa ikon taimakonsu, kāriyar da Masar za ta yi musu ƙarshenta masifa.

4 Ko da yake jakadunsu sun riga sun isa Zowan da Hanes, biranen Masar,

5 duk da haka jama’ar Yahuza za su yi da na sani, da suka dogara ga al’ummar da ba abar dogara ba ce, al’ummar da ba ta daɗa musu kome a lokacin da suke sa zuciya ga taimako ba.”

6 Wannan shi ne jawabin da Allah ya yi a kan dabbobin da suke kudancin hamada, “Jakadu sun yi tafiya a ƙasa mai hatsari, inda zakoki suke, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke. Suna labta wa jakunansu da raƙumansu kayayyaki masu tsada da za su kai gaisuwa ga al’ummar da ba za ta taimake su da kome ba.

7 Taimakon da Masar za ta yi marar amfani ne. Don haka na yi mata laƙabi, ‘Macijin da ba ya yin kome.’ ”

Jama’a Marar Biyayya

8 Allah ya faɗa mini in rubuta a littafi yadda mutane suke, saboda ya zama tabbatacciyar shaida a kansu.

9 A kullum suna tayar wa Allah, a kullum ƙarya suke yi, a kullum suna ƙin kasa kunne ga koyarwar Allah.

10 Sukan faɗa wa annabawa su yi shiru. Sukan ce, “Kada ku yi mana magana a kan abin da yake daidai. Ku faɗa mana abin da muke so mu ji ne kawai. Bari mu ci gaba da ruɗewarmu.

11 Tashi daga nan, kada ku toshe mana hanya. Ba ma so mu ji kome game da Allah Mai Tsarki na Isra’ila.”

12 Amma wannan shi ne abin da Allah Mai Tsarki na Isra’ila ya ce, “Kun yi banza da abin da nake faɗa muku, kuna dogara ga aikin kamakarya da yin zamba.

13 Kun yi laifi. Kuna kamar bango wanda ya tsage daga bisa har ƙasa. Za ku fāɗi ba zato ba tsammani.

14 Za a ragargaza ku kamar tukunyar yumɓu, da mummunar ragargazawa har da ba za a sami ‘yar katangar da za a ɗauki garwashin wuta ba, ko a ɗebo ruwa daga randa.”

15 Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra’ila, ya ce wa jama’a, “Ku komo gare ni a natse, ku dogara gare ni. Sa’an nan za ku zama ƙarfafa ku zauna lafiya.” Amma ba ku yarda ba!

16 A maimakon haka sai kuka shirya ku tsere wa maƙiyanku a kan dawakai masu gudu. Daidai ne, tilas ku tsere! Tsammani kuke saurin gudun dawakanku ya isa, amma waɗanda za su fafare ku sun fi ku gudu!

17 Dubunku za su gudu da ganin abokin gābanku ɗaya, abokan gāba biyar sun isa su sa dukanku ku gudu. Ba abin da zai ragu daga cikin rundunar sojojinku, sai sandan tutarku kaɗai da take kan tudu.

18 Duk da haka dai, Ubangiji yana jira ya yi muku alheri. A shirye yake ya yi muku jinƙai, domin a kullum yana aikata abin da yake daidai. Ta wurin dogara ga Ubangiji ake samun farin ciki.

Ubangiji Zai Sa wa Jama’arsa Albarka

19 Ku jama’ar da suke zaune a Urushalima ba za ku ƙara yin kuka ba. Ubangiji mai juyayi ne, sa’ad da kuka yi kuka gare shi neman taimako, zai amsa muku.

20 Ubangiji zai sa ku ku sha wahala, amma shi kansa zai kasance tare da ku, ya koya muku, ba za ku ƙara wahalar nemansa ba.

21 Idan kuka kauce daga hanya zuwa dama ko hagu, za ku ji muryarsa a bayanku yana cewa, “Ga hanyan nan, ku bi ta.”

22 Za ku kwashe gumakanku waɗanda aka dalaye da azurfa, da waɗanda aka rufe da zinariya, ku jefar da su kamar abin ƙyama, kuna ihu, kuna cewa, “Ku ɓace mana da gani!”

23 Duk lokacin da kuka shuka amfanin gonakinku, Ubangiji zai aiko da ruwan sama ya sa su girma, zai ba ku kaka mai albarka, shanunku kuma za su sami makiyaya wadatacciya.

24 Takarkaranku da jakunanku da suke huɗar gonakinku za su ci harawa mafi kyau duka.

25 A wannan rana sa’ad da aka kame kagaran abokan gābanku, aka kashe jama’arsu, rafuffukan ruwa za su malalo daga kowane tsauni da kowane tudu.

26 Wata zai yi haske kamar rana, hasken rana zai riɓanya har sau bakwai kamar a tattara hasken rana na kwana bakwai a maishe shi ɗaya! Dukan wannan zai faru sa’ad da Ubangiji zai ɗaure raunukan da ya yi musu, ya warkar da su.

Allah zai Hukunta Assuriya

27 Ana iya ganin ikon Allah da ɗaukakarsa daga nesa! Wuta da hayaƙi suna nuna fushinsa. Ya yi magana, maganarsa tana ƙuna kamar wuta.

28 Ya aika da iska a gabansa kamar rigyawa wadda take kwashe kome, ta tafi da shi. Yakan gwada al’ummai ya kai su hallaka, yakan sa dukan shirye-shiryensu na mugunta su ƙare.

29 Amma ku, jama’ar Allah, za ku yi farin ciki, ku raira waƙa kamar yadda kukan yi a daren tsattsarkan idi. Za ku yi murna kamar waɗanda suke tafiya suna bushe-bushe a hanyarsu ta zuwa Haikalin Ubangiji Mai Tsarki, Mai Ceton Isra’ila.

30 Ubangiji zai bar kowane mutum ya ji maɗaukakiyar muryarsa, ya kuma ji ƙarfin fushinsa. Za a ga harsunan wuta, gizagizai za su ɓarke, za a yi ƙanƙara, da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.

31 Assuriyawa za su firgita sa’ad da suka ji muryar Allah, suka kuma ji irin zafin hukuncinsa.

32 Sa’ad da Ubangiji ya miƙa sandan hukuncinsa ya yi ta bugun Assuriyawa, jama’arsa kuwa za su yi ta kaɗa ganguna da garayu, su yi murna!

33 An riga an shirya wurin ƙonawa don Sarkin Assuriya. An tsiba itace cike da wurin. Kamar kibritu, numfashin Ubangiji zai cinna masa wuta.