ISH 32

Sarki Mai Adalci

1 Wata rana za a yi wani sarki mai adalci, da kuma shugabannin ƙasa waɗanda za su yi mulki da gaskiya.

2 Ko wannensu zai zama kamar wurin fakewa daga iska da kuma wurin ɓuya saboda hadiri, za su zama kamar rafuffukan da suke gudu cikin hamada, kamar inuwar babban dutse a ƙeƙasasshiyar ƙasa.

3 Idanunsu da kunnuwansu za su kasance a buɗe domin sauraron jama’a.

4 Za su zama masu haƙuri sosai, za su yi kome da haziƙanci, za su kuma faɗi abin da suke nufi.

5 Ba wanda zai girmama wawayen mutane, ko kuma ya ce da mazambata suna da aminci.

6 Dakiki yakan yi maganar wauta ya kuma yi tunanin mugayen ayyukan da zai aikata. Abin da dakiki yakan aikata da abin da yakan faɗa, duk ɓatanci ne ga Allah, bai kuwa taɓa ciyar da masu jin yunwa ba, ko ya ba masu jin ƙishi ruwa su sha.

7 Mugu ne shi, yana kuwa yin mugayen abubuwa, yakan yi shiri don ya lalatar da matalauta da ƙarya, ya kuma hana su samun hakkinsu.

8 Amma mutum mai aminci yakan yi aikin aminci ya kuwa tsaya da ƙarfi a kan abin da yake daidai.

An Yi wa Matan Urushalima Faɗaka

9 Ku matan da kuke zaman jin daɗi, ba ku da damuwar kome, ku kasa kunne ga abin da nake faɗa.

10 Zai yiwu ku wadatu yanzu, amma baɗi war haka za ku fid da zuciya, gama ba inabin da za ku tattara.

11 Kuna ta zaman jin daɗi, ba abin da yake damunku, amma yanzu ku yi rawar jiki don tsoro! Ku tuɓe tufafinku ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.

12 Ku bugi ƙirjinku don baƙin ciki, gama an lalatar da gonaki masu dausayi da kuma gonakin inabi,

13 ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya ne suke girma a ƙasar jama’ata. Ku yi kuka domin dukan gidajen da mutane suke murna a cikinsu dā, domin kuma birnin da yake cike da jin daɗi a dā.

14 Har ma za a bar fādar, babban birnin sarauta kuma za a gudu a bar shi gaba ɗaya. Gidaje kuma da kagaran da take tsaronsu za su zama rusassu har abada. A can jakunan jeji za su yi ta zarya, tumaki kuma za su sami wurin kiwo.

15 Amma Allah zai ƙara aiko mana da Ruhunsa. Ƙasar da ta zama marar amfani za ta komo mai dausayi, gonaki kuma za su ba da amfani mai yawa.

16 A ko’ina a ƙasar za a aikata adalci da gaskiya.

17 Gama kowa zai yi abin da yake daidai, za a sami salama da zaman lafiya har abada.

18 Gidajen jama’ar Allah za su zama da salama da zaman lafiya, ba abin da zai dame su.

19 (Amma ƙanƙara za ta faɗo a jeji, za a kuma rurrushe birni.)

20 Kowa zai yi murna da ruwan sama mai yawa domin amfanin gona, da kuma lafiyayyiyar makiyaya domin jakuna da shanu.