ISH 38

Ciwon Sarki Hezekiya da Warkewarsa

1 A lokacin nan sai sarki Hezekiya ya kamu da rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya je wurinsa domin ya gaishe shi, ya ce masa, “Ubangiji ya ce ka kintsa kome daidai, gama ba za ka warke ba. Ka yi shirin mutuwa.”

2 Hezekiya kuwa ya juya wajen bango ya yi addu’a, ya ce,

3 “Ya Ubangiji, ka tuna, na bauta maka da aminci da biyayya, na kuma yi ƙoƙarin aikata abin da kake so in yi.” Sai ya fara kuka mai zafi.

4 Sa’an nan Ubangiji ya umarci Ishaya,

5 cewa ya koma wurin Hezekiya ya faɗa masa, “Ni, Ubangiji Allah na kakanka Dawuda, na ji addu’arka, na kuma ga hawayenka, zan bar ka ka ƙara shekara goma sha biyar nan gaba.

6 Zan cece ka, da wannan birni na Urushalima, daga Sarkin Assuriya, zan ci gaba da kiyaye birnin.”

7 Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ubangiji zai nuna maka alama da za ta tabbatar maka zai cika alkawarinsa.

8 Ubangiji zai komar da inuwa baya da taki goma, bisa ga ma’aunin rana na sarki Ahaz.” Inuwa kuwa ta koma da baya daga fuskar rana har mataki goma.

9 Bayan da Hezekiya ya warke daga rashin lafiyarsa, sai ya rubuta wannan waƙar yabo.

10 Na zaci a gaɓar ƙarfina

Zan tafi lahira,

Ba zan ƙara rayuwa ba.

11 Na zaci ba zan ƙara ganin Ubangiji ba

A wannan duniya ta masu rai,

Ko kuwa in ga wani mutum mai rai.

12 An datse raina, ya ƙare,

Kamar alfarwar da aka kwance,

Kamar saƙar da aka yanke,

Na zaci Allah zai kashe ni.

13 Dare farai na yi ta kuka saboda azaba,

Sai ka ce zaki yake kakkarya ƙasusuwana.

Na zaci Allah zai kashe ni.

14 Muryata ƙarama ce, ba kuma ƙarfi,

Na kuwa yi kuka kamar kurciya,

Idanuna sun gaji saboda duban sama.

Ya Ubangiji, ka cece ni daga dukan wannan wahala.

15 Me zan iya faɗa? Ubangiji ne ya yi wannan.

Ina da ɓacin zuciya, ba na iya barci.

16 Ya Ubangiji, zan bi ka, kai kaɗai.

Ka warkar da ni, ka bar ni da rai.

17 Ɓacin zuciyata zai juya ya zama salama.

Ka ceci raina daga dukan hatsari,

Ka gafarta dukan zunubaina.

18 Ba wanda yake yabonka a lahira,

Matattu ba za su iya dogara ga amincinka ba.

19 Masu rai ne suke yabonka,

Kamar yadda nake yabonka yanzu.

Iyaye za su faɗa wa ‘ya’yansu irin amincinka.

20 Ya Ubangiji, ka riga ka warkar da ni!

Za mu kaɗa garayu mu kuma raira waƙar yabo,

Za mu raira yabo cikin Haikalinka muddin ranmu.

21 Haka ya faru bayan da Ishaya ya faɗa wa sarki ya sa curin da aka yi da ‘ya’yan ɓaure a kan marurun, ya kuwa warke.

22 Sarki Hezekiya ya riga ya yi tambaya ya ce, “Me zai zama alama ta cewa zan iya zuwa Haikali?”