ISH 47

Hukunci a kan Babila

1 Ubangiji ya ce,

“Babila, ki sauko daga kan gadon sarautarki,

Ki zauna a ƙasa cikin ƙura.

Dā ke budurwa ce, birnin da ba a yi nasara da shi ba!

Amma ba sauran taushi da kuma rashin ƙarfi!

Ke baiwa ce yanzu!

2 Ki juya dutsen niƙa, ki niƙa gari!

Ki kware lulluɓi! Ki tuɓe kyawawan tufafinki!

3 Mutane za su gan ki a ƙasƙance, a kunyace kuma,

A tuɓe ki tsirara kamar yarinyar da take baiwa.

Zan ɗauki fansa, ba kuwa wanda zai hana ni.”

4 Allah Mai Tsarki na Isra’ila ya fanshe mu,

Sunansa Ubangiji Mai Runduna ne!

5 Ubangiji ya ce wa Babila,

“Ki zauna shiru a cikin duhu,

Ba za su ƙara kiranki sarauniyar al’ummai ba!

6 Na yi fushi da mutanena,

Na maishe su kamar su ba nawa ba ne.

Na sa su a ƙarƙashin ikonki,

Ba ki kuwa yi musu jinƙai ba,

Har da tsofaffi ma kin ba su wuya.

7 Kina tsammani za ki yi ta zama sarauniya kullayaumin,

Ba ki ɗauki waɗannan al’amura a zuci ba,

Ko ki yi tunanin yadda za su ƙare.

8 “Ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi,

Ke da kike tsammani kina zaune lami lafiya.

Kin ɗauka kina da girma kamar Allah,

Har kina ganin ba wani kamarki.

Kina tsammani ba za ki taɓa zama gwauruwa ba,

Ko ki sha hasarar ‘ya’yanki.

9 Amma ba da jimawa ba, a rana ɗaya

Dukan waɗannan al’amura za su faru.

Kome sihirin da za ki yi,

Za ki rasa ‘ya’yanki, ki kuwa zama gwauruwa.

10 “Kin amince da kanki cikin muguntarki,

Kina tsammani ba wanda yake ganinki.

Hikimarki da saninki suka sa kika ɓata,

Kika kuwa ce da kanki, ‘Ni ce Allah,

Ba mai kama da ni!’

11 Duk da haka bala’i zai auko miki,

Ba ɗaya daga cikin sihirinki da zai tsai da shi ba,

Lalacewa za ta auko a kanki farat ɗaya,

Lalacewar da ba ki taɓa ko mafarkinta ba!

12 Ki riƙe dukan sihirinki, da makarunki, da layunki,

Kina amfani da su tun kina ƙarama.

Watakila za su yi miki wani taimako,

Watakila kya iya tsoratar da abokan gāba.

13 Kome shawarar da kika samu ba ki da ƙarfi.

Bari mashawartanki su fito su cece ki,

Waɗancan mutane masu binciken taurari

Waɗanda suka zana taswirar sammai,

Su kuma faɗa miki

Dukan abin da zai faru da yake wata wata.

14 “Za su zama kamar budu,

Wuta kuwa za ta ƙone su ƙurmus!

Ba ma za su ko iya ceton kansu ba.

Harshen wuta zai fi ƙarfinsu,

Ba wutar da za su zauna, su ji ɗumi!

15 Nan ne inda shawararsu za ta kai ki,

Waɗannan masanan taurari da kika yi ta neman shawararsu dukan kwanakin ranki.

Dukansu za su bar ki, kowa ya tafi inda ya nufa,

Ba wanda zai ragu da zai cece ki.”