ISH 53

1 Wane ne zai gaskata abin da muka ji yanzu?

Wane ne zai iya ganin ikon Ubangiji cikin wannan?

2 Nufin Ubangiji ne bawansa ya yi girma

Kamar dashe wanda yake kafa saiwarsa a ƙeƙasasshiyar ƙasa.

Ba shi da wani maƙami ko kyan ganin

Da zai sa mu kula da shi.

Ba wani abin da zai sa mu so shi,

Ba kuwa abin da zai ja mu zuwa gare shi.

3 Muka raina shi, muka ƙi shi,

Ya daure da wahala da raɗaɗi.

Ba wanda ya ko dube shi.

Muka yi banza da shi kamar shi ba kome ba ne.

4 Amma ya daure da wahala wadda a ainihi tamu ce,

Raɗaɗin da ya kamata mu ne za mu sha shi.

Mu kuwa muna tsammani wahalarsa

Hukunci ne Allah yake yi masa.

5 Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu,

Aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata.

Hukuncin da ya sha ya ‘yantar da mu,

Dūkan da aka yi ta yi masa, ya sa muka warke.

6 Dukanmu muna kama da tumakin da suka ɓata,

Ko wannenmu ya kama hanyarsa.

Sai Ubangiji ya sa hukunci ya auko a kansa,

Hukuncin da ya wajaba a kanmu.

7 Aka ƙware shi ba tausayi,

Amma ya karɓa da tawali’u,

Bai ko ce uffan ba.

Kamar ɗan rago wanda ake shirin yankawa,

Kamar tunkiya wadda ake shirin yi wa sausaya,

Bai ko ce uffan ba.

8 Aka kama shi, aka yanke masa shari’a,

Aka tafi da shi domin a kashe shi,

Ba wanda ya kula da ƙaddararsa.

Aka kashe shi saboda zunubin mutanenmu.

9 Aka yi jana’izarsa tare da maguye.

Aka binne shi tare da masu arziki

Ko da yake bai taɓa yin laifin kome, ko ƙarya ba.

10 Ubangiji ya ce,

“Nufina ne ya sha wahala,

Mutuwar kuwa hadaya ce domin ta kawo gafara,

Saboda haka zai ga zuriyarsa,

Zai yi tsawon rai,

Ta wurinsa nufina zai cika.

11 Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna,

Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce,

Shi ne bawana, adali,

Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa,

Ya sa su zama mutanena amintattu.

12 Saboda haka zan ba shi matsayi mai girma,

Matsayi a cikin manyan mutane masu iko.

Da yardarsa ya ba da ransa

Ya ɗauki rabon masu laifi.

Ya maye gurbin masu zunubi da yawa,

Ya kuwa sha hukuncin da ya cancanci masu zunubi.

Ya yi roƙo dominsu.”