ISH 56

Sakamakon Cikar Alkawarin Ubangiji

1 Ga jawabin da Ubangiji ya yi, “Ku kiyaye gaskiya ku yi adalci, gama cetona yana zuwa nan da nan, za a kuwa bayyana adalcina.

2 Mai albarka ne mutumin da yake aikata wannan, da ɗan adam da yake riƙe da shi kam, wanda yake kiyaye ranar Asabar, bai kuwa ƙazantar da ita ba, wanda kuma ya tsame hannunsa daga aikata kowace irin mugunta.”

3 Kada baƙon da ya hada kansa da mutanen Ubangiji ya ce, hakika Ubangiji zai ware shi daga jama’arsa.

Kada kuma baban ya ce shi busasshen itace ne.

4 Ga abin da Ubangiji ya ce, wa mutanen nan, “Ku babani waɗanda kuka kiyaye Asabar ɗina, ku da kuka zaɓi abubuwan da suka gamshe ni, kuka kuwa cika alkawarina da aminci,

5 zan ba ku matuni da suna a Haikalina da cikin garukana, da sun fi na ‘ya’ya mata da maza. Zan ba ku tabbataccen suna wanda ba za a raba ku da shi ba.”

6 Ubangiji ya ce wa baƙin da suka bi shi, don su yi masa hidima, suna ƙaunar sunansa, sun kuma zama bayinsa, dukan wanda yake kiyaye ranar Asabar, bai kuwa ɓata ta ba, ya kuma cika alkawarinsa da aminci,

7 “Zan kai ku tsattsarkan dutsena, in sa ku yi murna a masujadata. Hadayunku na ƙonawa da sadakokinku za su zama abin karɓa a bagadena. Za a kira Haikalina wurin yin addu’a na dukan jama’a.”

8 Haka Ubangiji Allah, shi wanda ya tattara Isra’ilawa korarru, ya faɗa, ya ce, “Zan ƙara tattaro waɗansu, bayan waɗanda na riga na tattara.”

Kā da Tsafin Isra’ila

9 Dukanku namomin jeji ku zo ku ci, dukanku namomin jeji.

10 Matsaransa makafi ne, dukansu marasa ilimi ne. Dukansu kamar karnuka ne bebaye, ba su iya haushi ba, suna kwance suna ta mafarki, suna jin daɗin rurumi!

11 Suna kama da karnuka masu zarin ci, ba su taɓa samun abin da ya ishe su ba. Makiyayan nan kuma ba haziƙai ba ne, dukansu, kowa ya nufi inda ya ga dama. Kowa yana ta nemar wa kansa riba.

12 Sukan ce, “Zo mu samo ruwan inabi, bari mu cika cikinmu da barasa. Gobe ma kamar yau za ta zama, har ma fiye da haka.”