K. MAG 21

1 Ubangiji ne yake mallakar tunanin sarki a sawwaƙe kamar yadda yake yi da ruwan rafi.

2 Ko da a ce dukan abin da kake yi daidai ne, ka tuna fa Ubangiji ya san manufarka.

3 Ubangiji ya fi so ka yi abin da yake daidai, mai kyau kuma, fiye da ka miƙa masa hadayu.

4 Girmankai da fāriya suke bi da mugaye, wannan kuwa zunubi ne.

5 Yin shiri a tsanaki zai kai ka ga biyan bukatarka, idan kuwa ka cika gaggawa ba za ka sami abin da zai ishe ka ba.

6 Dukiyar da aka tara ta hanyar rashin gaskiya takan ƙare nan da nan, takan kuma kai ga mutuwa.

7 Mugaye, tasu ta ƙare saboda muguntarsu, gama sun ƙi yin abin da yake daidai.

8 Mutane masu laifi sukan bi ta karkatacciyar hanya, marasa laifi kuwa suna aikata abin da yake daidai.

9 Gara zama a saƙo da zama a gida ɗaya tare da mace mai mita.

10 Mugaye sun zaƙu su aikata mugunta, ba su yi wa kowa jinƙai.

11 Sa’ad da aka hukunta mai girmankai, ko marar tunani yakan koyi wani abu, mutum mai hikima yakan koyi abin da ake koya masa.

12 Adali ya san tunanin mugaye, yakan kuwa zama sanadin lalacewarsu.

13 Idan ka ƙi jin kukan matalauci, naka kukan da kake yi na neman taimako, ba za a ji ba.

14 Kyauta a asirce takan kwantar da zuciyar wanda yake fushi da kai.

15 Sa’ad da aka yi adalci mutanen kirki sukan yi murna, amma mugaye sukan yi baƙin ciki.

16 Mutuwa tana jiran wanda ya ƙi bin hanyar hankali.

17 Sa kai cikin nishaɗi, wato shan ruwan inabi, da cin abinci mai tsada, ba zai bar ka ka tara dukiya ba.

18 Wahalar da mugaye suke so su jawo wa mutanen kirki, za ta koma kansu.

19 Gara ka zauna a hamada, da ka zauna tare da mace mai mita, mai yawan kai ƙara.

20 Mutane masu hikima suna zaune da wadata da nishaɗi, amma wawaye da zarar sun sami kuɗi sukan kashe su nan da nan.

21 Ka yi alheri ka yi aminci, za ka yi tsawon rai waɗansu kuma za su girmama ka, su yi maka abin da yake daidai.

22 Sarkin yaƙi mai wayo yakan ci birnin da jarumawa suke tsaro, ya rushe garun da suke taƙama da shi.

23 Idan ba ka so ka shiga wahala, ka lura da abin da kake faɗa.

24 Ba kalmar da ta fi “fāɗin rai” dacewa ga mutum mai girmankai, mai fāriya marar tunani.

25 Malalacin mutumin da ya ƙi yin aiki, kansa yake kashewa.

26 Duk abin da yake tunani dukan yini, shi ne a kan abin da yake so ya samu. Amma adali ko ta ƙaƙa yakan bayar da hannu sake.

27 Ubangiji yana ƙin hadayar da mugaye suka miƙa masa, tun ba wadda suka miƙa ta da mugun nufi ba.

28 Ba a gaskata shaidar maƙaryaci, amma mutumin da yakan yi tunani a kan al’amura, akan karɓi tasa.

29 Adali ya tabbatar da kansa, haka ma mugun mutum yakan yi da’awa, cewa shi ma ya tabbatar da kansa.

30 Hikima, da haziƙanci, da basira, ba kome suke ba gāba da Ubangiji.

31 Kana iya shirya dawakai don zuwa yaƙi, amma nasara ta Ubangiji ce.