K. MAG 22

1 Idan ya zama dole ne ka zaɓa tsakanin kyakkyawan suna ko dukiya, to, ka zaɓi kyakkyawan suna, tagomashi kuma ya fi azurfa da zinariya.

2 Ba bambanci tsakanin mawadaci da matalauci, gama Ubangiji ne ya halicce su duka.

3 Mutum mai hankali, in ya ga wahala tana zuwa yakan kauce mata, amma shashasha yakan kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.

4 Kana da tsoron Ubangiji, ka yi tawali’u, za ka arzuta, ka ɗaukaka, ka sami tsawon rai.

5 Idan kana ƙaunar ranka ka nisanci tarkunan da aka kafa a hanya don su kama mugaye.

6 Ka koya wa yaro yadda zai yi zamansa, zai kuwa tuna da ita dukan kwanakinsa.

7 Matalauta su ne bayin attajirai, bawa ne kai ga wanda ka ci bashi a gare shi.

8 In ka shuka rashin gaskiya masifa ce za ta tsiro, wato hukunci mai tsanani wanda zai hallakar da kai.

9 Ka zama mai hannu sake, ka riƙa ba matalauta abincinka, za a sa maka albarka saboda haka.

10 Ka rabu da mutum mai fāriya, mai gardama, mafaɗaci, hatsaniya za ta ƙare.

11 In ka yi ladabi za ka zama aminin sarki, gama yana ƙaunar amintaccen mutum.

12 Ubangiji yana lura ya ga an riƙe gaskiya sosai ta wurin ƙin yarda da maganganun ƙarya.

13 Malalaci yakan yi zamansa a gida, yakan ce, “Zaki zai kama ni in na fita waje.”

14 Zina tarko ce, takan kama waɗannan waɗanda Ubangiji yake fushi da su.

15 Halin yara ne su yi wauta da waɗansu abubuwa na rashin kula, amma tsumagiya za ta koya musu abin da ya fi kyau.

16 Idan attajirai kake yi wa kyauta, kana kuma zaluntar matalauta don ka arzuta, kai kanka za ka talauce.

Umarnai da Dokoki

17 Ka kasa kunne zan koya maka abin da masu hikima suka faɗa, yi nazari a kan koyarwarsu.

18 Za ka yi murna in ka tuna da su, ka iya faɗarsu.

19 Ina so ka dogara ga Ubangiji, don haka zan faɗa maka su yanzu.

20 Na rubuta maka karin magana, suna ƙunshe da ilimi da kyakkyawar shawara.

21 Zan koya maka ainihin gaskiya, domin sa’ad da aka aike ka ka nemo ta, za ka iya kawo amsa daidai.

22 Kada ka ƙwari matalauci don ka fi shi, kada ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari’a.

23 Ubangiji zai yi magana dominsu a kan shari’ar da suke yi, ya nemi ran duk wanda yake neman rayukansu.

24 Kada ka yi abuta da mutane masu zafin fushi, ko masu zafin rai.

25 Mai yiwuwa ne ka koyi irin ɗabi’unsu, har ka kasa sākewa.

26 Kada ka yi alkawarin ɗaukar wa wani lamuni,

27 gama idan ka kāsa biya har gadonka ma za su ɗauke.

28 Kada ka kawar da shidar kan iyaka wadda kakanninka suka kafa.

29 Ka nuna mini mutumin da yake aiki mai kyau, ni kuwa in nuna maka mutumin da ya fi duka, wanda ya cancanci ya zauna tare da sarakuna.