LUK 21

Sadaka wadda aka Saka

1 Yesu ya ɗaga kai ya ga waɗansu masu arziki suna saka sadakarsu a baitulmalin Haikali.

2 Sai ya ga wata gajiyayyiya da mijinta ya mutu ta saka rabin kobo biyu a ciki.

3 Sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, abin da gajiyayyiya gwauruwan nan ta saka a ciki, ya fi na sauran duka.

4 Domin duk waɗannan sun bayar daga yalwarsu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk kuɗinta na abinci.”

Yesu Ya Faɗi irin Rushewar da za ta Sami Haikali

5 Waɗansu suna zancen Haikali, da yadda aka ƙawata shi da duwatsun alfarma da keɓaɓɓun kayan sadaka, sai ya ce,

6 “In don waɗannan abubuwa da kuke kallo ne, ai, lokaci yana zuwa da ba wani dutsen da za a bari a nan a kan ɗan’uwansa da ba a baje shi ba.”

Alamu da Tsanance-tsanance

7 Sai suka tambaye shi suka ce, “Malam, a yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa’ad da suke shirin aukuwa?”

8 Sai ya ce, “Ku kula fa kada a ɓad da ku. Don mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa su ne ni, suna kuma cewa, ‘Lokaci ya yi kusa.’ To, kada ku bi su.

9 In kuma kun ji labarin yaƙe-yaƙe da hargitsi, kada ku firgita. Lalle ne wannan ya fara aukuwa, amma ƙarshen tukuna.”

10 Sa’an nan ya ce musu, “Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki ya tasar wa mulki.

11 Za a yi raurawar ƙasa manya manya, da kuma yunwa, da annoba a wurare dabam dabam. Za a kuma yi al’amura masu bantsoro da manyan alamu daga sama.

12 Amma kafin wannan duka, za su kama ku, su tsananta muku. Za su miƙa ku ga majami’u da kurkuku, su kuma kai ku a gaban sarakuna da mahukunta saboda sunana.

13 Wannan zai zama muku hanyar ba da shaida.

14 Saboda haka, sai ku ƙudura a ranku, a kan ba za ku damu da yadda za ku mai da jawabi ba.

15 Domin ni ne zan ba ku ikon hurci, da kuma hikima wadda duk abokan adawarku, ba za su iya shanyewa ko musawa ba.

16 Ko da iyayenku ma da ‘yan’uwanku, da danginku, da abokanku, sai sun bāshe ku, su kuma sa a kashe waɗansunku.

17 Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana.

18 Amma ba gashin kanku ko ɗaya da zai yi ciwo.

19 Jurewarku ce za ta fisshe ku.”

Yesu ya Faɗi irin Ribɗewa da za ta Sami Urushalima

20 “Sa’ad da kuka ga rundunonin yaƙi sun kewaye Urushalima, sa’an nan ku tabbata ana kusan ribɗe ta.

21 Sa’an nan waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, su gudu su shiga duwatsu, na birni su fice, na ƙauye kuma kada su shiga birni.

22 Saboda lokacin sakamako ne, don a cika duk abin da yake rubuce.

23 Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci! Don matsanancin ƙunci zai saukar wa ƙasar, da kuma fushin Allah ga jama’an nan.

24 Za a kashe waɗansu da kaifin takobi, a kuma kakkama waɗansu a kai su bauta zuwa ƙasashen al’ummai duka. Al’ummai kuma za su tattake Urushalima, har ya zuwa cikar zamaninsu.”

Komowar Ɗan Mutum

25 “Za a kuma ga alamu a rana, da wata, da taurari, a duniya kuma al’ummai su matsu ƙwarai, suna shan damuwa saboda ƙugin teku da na raƙuman ruwa.

26 Mutane za su suma don tsoro, da kuma fargaban al’amuran da suke aukuwa ga duniya, don za a girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.

27 A sa’an nan ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin gajimare da iko da ɗaukaka mai yawa.

28 Sa’ad da waɗannan al’amura suka fara aukuwa, sai ku ɗaga kai ku dubi sama, domin fansarku ta yi kusa.”

Aya a kan Itacen Ɓaure

29 Sai ya ba su wani misali, ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa,

30 da zarar sun fara toho, kuna gani, ku da kanku kun san damuna ta yi kusa ke nan.

31 Haka kuma sa’ad da kuka ga waɗannan al’amura suna aukuwa, ku sani Mulkin Allah ya gabato.

32 Hakika, ina gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba, sai duk abubuwan nan sun auku.

33 Sararin sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”

Gargaɗi a Zauna a Faɗake

34 “Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har ba labari ranan nan ta mamaye ku kamar tarko.

35 Don haka, za ta auka wa mazaunan duniya duk, kowa da kowa.

36 Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu’a ku sami ikon tsere wa dukan waɗannan al’amura da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”

37 Kullum da rana yakan koyar a Haikali, da dare kuma yakan fita ya kwana a dutsen da ake ce da shi Dutsen Zaitun.

38 Da sassafe kuma dukan mutane sukan zo wurinsa a Haikali su saurare shi.