LUK 4

Shaiɗan Ya Gwada Yesu

1 Yesu kuma cike da Ruhu Mai Tsarki sai ya dawo daga Kogin Urdun. Ruhu na iza shi zuwa jeji,

2 har kwana arba’in, Iblis yana gwada shi. A kwanakin nan bai ci kome ba. Da suka ƙare kuwa ya ji yunwa.

3 Iblis ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, ka umarci dutsen nan ya zama gurasa,”

4 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba.’ ”

5 Sai Iblis ya kai shi wani wuri a bisa, ya nunnuna masa dukkan mulkokin duniya a ƙyiftawar ido.

6 Iblis ya ce masa, “Kai zan bai wa ikon duk waɗannan, da ɗaukakarsu, don ni aka danƙa wa, nakan kuma bayar ga duk wanda na ga dama.

7 In kuwa za ka yi mini sujada, duk su zama naka.”

8 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake cewa,

‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada,

Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”

9 Sai kuma ya kai shi Urushalima, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali, ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, to, dira ƙasa daga nan,

10 don a rubuce yake cewa,

‘Zai yi wa mala’ikunsa umarni game da kai, su kiyaye ka,’

11 da kuma

‘Za su tallafe ka,

Don kada ka yi tuntuɓe da dutse.’ ”

12 Sai Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai kuwa an ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”

13 Bayan da Iblis ya gama irin dukan gwaje-gwajensa, ya rabu da shi ɗan lokaci tukuna.

Yesu Ya Fara Hidima a Galili

14 Yesu ya koma ƙasar Galili, ikon Ruhu yana tare da shi. Labarinsa ya bazu a dukan kewayen.

15 Ya yi ta koyarwa a majami’unsu, duk ana girmama shi.

An Ƙi Yesu a Nazarat

16 Ya zo Nazarat inda aka rene shi. Ya shiga majami’a a ran Asabar kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe domin ya yi karatu.

17 Aka miƙa masa Littafin Annabi Ishaya, ya buɗe littafin, ya sami inda aka rubuta cewa,

18 “Ruhun Ubangiji yana tare da ni,

Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara.

Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru,

In kuma buɗe wa makafi ido,

In kuma ‘yanta waɗanda suke a danne,

19 In yi shelar zamanin samun karɓuwa ga Ubangiji.”

20 Ya rufe littafin ya mayar wa mai hidima, ya zauna. Duk waɗanda suke cikin majami’a suka zuba masa ido.

21 Sai ya fara ce musu, “Yau Nassin nan ya cika a kunnenku.”

22 Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe, wannan ba ɗan Yusufu ba ne?”

23 Yesu ya ce musu, “Lalle za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka.’ Za ku kuma ce mini, ‘Duk abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, ka yi a nan garinku mana.’ ”

24 Ya ce kuma, “Hakika, ina gaya muku, ba annabin da yake yardajje a garinsu.

25 Amma gaskiya nake gaya muku, a zamanin Iliya akwai mata gwauraye da yawa a Isra’ila, wato a lokacin da aka hana ruwan sama har shekara uku da wata shida, sa’ad da babbar yunwa ta game dukan ƙasar.

26 Duk da haka ba a aiki Iliya gun ko ɗaya daga cikinsu ba, sai ga wata mace kaɗai a Zarifat ta ƙasar Sidon wadda mijinta ya mutu.

27 A zamanin Annabi Elisha kuma akwai kutare da yawa a Isra’ila, ba kuwa ɗayansu da aka tsarkake sai Na’aman, mutumin Suriya, kaɗai.”

28 Da suka ji haka, duk waɗanda suke a majami’a suka husata ƙwarai.

29 Sai suka tashi suka fitar da shi bayan gari, har suka kai shi goshin dutsen da aka gina garinsu a kai, don su jefa shi ƙasa.

30 Amma ya ratsa ta tsakiyarsu, ya yi tafiyarsa.

Mai Baƙin Aljan

31 Sai ya tafi Kafarnahum, wani gari a ƙasar Galili, yana koya musu ran Asabar.

32 Suka yi mamakin koyarwarsa domin magana tasa da hakikancewa take.

33 A majami’ar kuwa akwai wani mutum mai baƙin aljan. Sai ya ta da murya da ƙarfi ya ce,

34 “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne ka hallaka mu? Na san ko wane ne kai, Mai Tsarkin nan ne kai na Allah.”

35 Sai Yesu ya kwaɓe shi ya ce, “Shiru! Rabu da shi!” Bayan da aljanin ya fyaɗa shi ƙasa a tsakiyarsu, ya rabu da shi, bai kuwa cuce shi ba.

36 Sai mamaki ya kama su duka, suna ce wa juna, “Wannan wace irin magana ce? Ga shi, da tabbatarwa, da gabagaɗi kuma yake umartar baƙaƙen aljannu, suna kuwa fita.”

37 Labarinsa duk ya bazu ko’ina a kewayen ƙasar.

Yesu Ya Warkar da Surukar Bitrus

38 Sai ya tashi daga majami’a, ya shiga gidan Bitrus. Surukar Bitrus kuwa tana fama da mugun zazzaɓi, sai suka roƙe shi saboda ita.

39 Sai ya tsaya a kanta, ya tsawata wa zazzaɓin, ya kuwa sake ta. Nan take ta tashi ta yi musu hidima.

Yesu Ya Warkar da Mutane da yawa da Maraice

40 A daidai fāɗuwar rana, duk waɗanda suke da marasa lafiya, masu cuta iri iri, suka kakkawo su wurinsa. Sai ya ɗaɗɗora wa kowannensu hannu, ya warkar da su.

41 Aljannu kuma suka fita daga mutane da yawa, suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya tsawata musu, ya hana su magana, don sun sani shi ne Almasihu.

Yesu Ya Tafi Yin Wa’azi

42 Da gari ya waye ya fita, ya tafi wani wurin inda ba kowa. Sai taro masu yawa suka yi ta nemansa, suka je wurinsa. Sonsu ne su tsaishe shi, don kada ya tashi daga gare su,

43 amma ya ce musu, “Lalle ne in yi wa sauran garuruwa bisharar Mulkin Allah, domin saboda wannan nufi ne aka aiko ni.”

44 Sai ya yi ta yin wa’azi a majami’un ƙasar Galili.