LUK 6

Almajirai suna Zagar Alkama a Ran Asabar

1 Wata rana ran Asabar, yana ratsa gonakin alkama, sai almajiransa suka zāgi alkamar, suna murtsukewa suna ci.

2 Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Don me kuke yin abin da bai halatta a yi ba a ran Asabar?”

3 Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba sa’ad da ya ji yunwa, shi da abokan tafiyarsa?

4 Yadda ya shiga masujadar Allah, ya ɗauki keɓaɓɓiyar gurasan nan ya ci, har ma ya ba abokan tafiyarsa, wadda ba ta halatta kowa ya ci ba, sai firistoci kaɗai?”

5 Sai ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”

Mai Shanyayyen Hannu

6 A wata Asabar kuma ya shiga majami’a, yana koyarwa. Akwai kuwa wani mutum a ciki wanda hannunsa na dama ya shanye.

7 Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka yi haƙwansa su ga ko yā warkar a ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa.

8 Shi kuwa ya san tunaninsu. Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Taso, ka tsaya nan tsakiya.” Sai ya tashi, ya tsaya a wurin.

9 Yesu ya ce musu, “Ina yi muku tambaya. Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko mugunta? A ceci rai, ko a hallaka shi?”

10 Sai ya duddube su duke, ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Ya miƙa, hannunsa kuwa sai ya koma lafiyayye.

11 Sai suka husata ƙwarai, suka yi shawarar abin da za su yi wa Yesu.

Yesu Ya Zaɓi Almajirai Sha Biyu

12 A kwanakin nan Yesu ya fita ya hau dutse domin yin addu’a. Dare farai yana addu’a ga Allah.

13 Da gari ya waye ya kira almajiransa, ya zaɓi goma sha biyu a cikinsu, ya ce da su manzanni.

14 Su ne Bitrus, da ɗan’uwansa Andarawas, da Yakubu, da Yahaya, da Filibus, da Bartalamawas,

15 da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Saminu, wanda ake ce da shi Zaloti,

16 da Yahuza ɗan Yakubu, da kuma Yahuza Iskariyoti, wanda ya zama maci amana.

Yesu Ya Hidimta wa Mutane Masu Yawa

17 Sai ya gangaro tare da su, ya tsaya a wani sarari. Ga kuwa babban taro masu binsa, da kuma taro masu yawan gaske daga duk ƙasar Yahudiya da Urushalima, da kuma yankin ƙasar Taya da Sidon da yake bakin bahar, waɗanda suka zo su saurare shi, a kuma warkar da cuce-cucensu.

18 Waɗanda kuma baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, aka warkar da su.

19 Duk taron suka nema su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.

Albarka da La’ana

20 Sai ya ɗaga kai, ya dubi almajiransa, ya ce,

“Albarka tā tabbata gare ku, ku matalauta, domin Mulkin Allah naku ne.

21 “Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke mayunwata a yanzu, domin za a ƙosar da kuke.

“Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke kuka a yanzu domin za ku yi dariya.

22 “Albarka tā tabbata a gare ku sa’ad da mutane suka ƙi ku, suka kuma ware ku, suka zage ku, suka yi ƙyamar sunanku saboda Ɗan Mutum.

23 Ku yi farin ciki a wannan rana, ku yi tsalle don murna, domin ga shi, sakamakonku mai yawa ne a Sama. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawa.

24 “Amma kaitonku, ku masu arziki domin kun riga kun sami taku ta’aziyya.

25 “Kaitonku, ku da kuke ƙosassu a yanzu, don za ku ji yunwa. “Kaitonku, ku masu dariya a yanzu, don za ku yi baƙin ciki, ku yi kuka.

26 “Kaitonku in kowa na yabonku. Haka kakanninsu ma suka yi wa annabawan ƙarya.”

Ƙaunar Magabta

27 “Amma ina gaya muku, ku masu sauraro, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa maƙiyanku alheri.

28 Ku sa wa masu zaginku albarka. Masu wulakanta ku kuma, ku yi musu addu’a.

29 Wanda ya mare ka a kunci ɗaya, juya masa ɗaya kuncin kuma. Wanda ya ƙwace maka mayafi, kada ka hana masa taguwarka ma.

30 Duk wanda ya roƙe ka, ka ba shi. Wanda kuma ya ƙwace maka kaya, kada ka neme shi.

31 Yadda kuke so mutane su yi muku, to, ku yi musu haka.

32 In masoyanku kawai kuke ƙauna wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma suna ƙaunar masoyansu.

33 In kuma sai waɗanda suke muku alheri kawai kuke yi wa alheri, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma haka suke yi.

34 In kuma sai ga waɗanda kuke tsammani za su biya ku ne kuke ba da rance, wane lada ne da ku? Ai, ko masu zunubi ma, sukan ba masu zunubi rance, don a biya su daidai.

35 Amma ku ƙaunaci magabtanku, kuna yi musu alheri. Ku ba da rance, kada kuwa ku tsammaci biya. Ladanku kuma zai yi yawa, za ku kuma zama ‘ya’yan Maɗaukaki, domin shi mai alheri ne ga masu butulci da kuma mugaye.

36 Ku kasance masu tausayi kamar yadda Ubanku yake mai tausayi.”

Kada ku Ɗora wa Kowa Laifi

37 “Kada ku ɗora wa kowa laifi, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yi wa kowa mugun zato, ku ma ba za a yi muku ba. Ku yafe, ku ma sai a yafe muku.

38 Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har ya yi tozo, har yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.”

39 Ya kuma ba su wani misali ya ce, “Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Ashe, dukansu biyu ba sai su fāɗa a rami ba?

40 Almajiri ba ya fin malaminsa. Amma kowa aka karantar da shi sosai, sai ya zama kamar malaminsa.

41 Don me kake duban ɗan hakin da yake a idon ɗan’uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba?

42 Ƙaƙa kuma za ka iya ce wa ɗan’uwanka, ‘Ya ɗan’uwana, bari in cire maka ɗan hakin da yake a idonka,’ alhali kuwa kai kanka ba ka ga gungumen da yake a naka ido ba? Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake a idonka tukuna sa’an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin da yake a idon ɗan’uwanka.”

Akan Gane Itace ta ‘Ya’yansa

43 “Ba kyakkyawan itace da yake haifar munanan ‘ya’ya, ba kuma mummunan itace da yake haifar kyawawan ‘ya’ya.

44 Domin kowane itace da irin ‘ya’yansa ake saninsa. Ai, ba a ɗiban ɓaure a jikin ƙaya, ko kuwa inabi a jikin sarƙaƙƙiya.

45 Mutumin kirki kam ta kyakkyawar taskar zuciyarsa yakan yi abin kirki, mugu kuwa ta mummunar taskar zuciyarsa yakan yi mugun abu. Ai, abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.”

Kafa Harsashin Gini Iri Biyu

46 “Don me kuke kirana, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ba kwa kuwa yin abin da na faɗa muku?

47 Duk mai zuwa wurina, yake jin maganata, yake kuma aikata ta, zan nuna muku kwatancinsa.

48 Kamar mutum yake mai gina gida, wanda ya yi haƙa mai zurfi, har ya sa harsashin ginin a kan fā. Da aka yi rigyawa, sai ruwan kogi ya bugi gidan, amma bai iya girgiza shi ba, saboda an gina shi da aminci.

49 Amma wanda ya ji maganata, bai kuwa aikata ba, kamar mutum yake wanda ya gina gida a kan turɓaya, ba harsashi. Ruwan kogi ya buge shi, nan da nan ya rushe. Wannan gida ya yi mummunar ragargajewa!”