MAK 2

Hukuncin Ubangiji a kan Urushalima

1 Ubangiji ya duhunta Sihiyona saboda fushinsa!

Daga Sama kuma ya jefar da darajar Isra’ila a ƙasa.

Bai kuma tuna da matashin sawayensa ba

A ranar fushinsa.

2 Dukan wuraren zaman Yakubu,

Ubangiji ya hallakar ba tausayi,

Da fushinsa kuma ya rurrushe kagaran Sihiyona.

Ya ƙasƙantar da mulki da masu mulkin.

3 Da zafin fushinsa, ya karya ƙarfin Isra’ila,

Ya kuma bar yi musu taimako

A lokacin da abokan gāba suka zo.

Kamar harshen wuta, ya ƙone dukan abin da yake na Yakubu.

4 Ya ja bakansa kamar abokan gāba,

Ya kuma nuna ikonsa kamar maƙiyi.

Ya hallaka dukan abin da yake da bansha’awa.

A alfarwar Sihiyona, ya zubo da hasalarsa kamar wuta.

5 Ubangiji ya zama kamar maƙiyi, ya hallaka Isra’ila.

Ya hallaka fādodinta duka,

Ya mai da kagaranta kango.

Ya aukar wa Yahuza da makoki da baƙin ciki mai yawa.

6 Ya rushe Haikalinsa kamar bukka cikin gona,

Ya mai da wurin yin ƙayyadaddun idodinsa kufai.

Ubangiji ya sa ƙayyadadden idi da kiyaye Asabar

Su ƙare a Sihiyona,

Da zafin fushinsa kuma ya wofinta sarki da firist.

7 Ubangiji ya wulakanta bagadensa,

Ya kuma wofinta tsattsarkan Haikalinsa.

Ya ba da garun fādodinta a hannun abokan gāba,

Suka yi sowa a Haikalin Ubangiji

Kamar a ranar idi.

8 Ubangiji ya yi niyya

Ya mai da garun Sihiyona kufai,

Ya auna ta da igiyar awo,

Bai janye dantsensa daga hallaka ta ba.

Ya sa kagara da garu su zozaye, su lalace tare.

9 Ƙofofinta sun nutse ƙasa,

Ya lalatar, ya kakkarya ƙyamarenta,

An kai sarkinta da mahukuntanta cikin al’ummai,

Inda ba a bin dokokin annabawanta,

Ba su kuma samun wahayi daga wurin Ubangiji.

10 Dattawan Sihiyona suna zaune a ƙasa shiru,

Sun yi hurwa, suna saye da tufafin makoki.

‘Yan matan Urushalima kuma sun sunkuyar da kansu ƙasa.

11 Idanuna sun dushe saboda kuka,

Raina yana cikin damuwa.

Zuciyata ta karai saboda halakar mutanena,

Gama ‘yan yara da masu shan mama

Sun suma a titunan birnin.

12 Suna yi wa uwayensu kuka, suna cewa,

“Ina abinci da ruwan inabi?”

Suna suma kamar mutanen da aka yi wa rauni

A titunan birnin,

Suna mutuwa a ƙirjin uwayensu.

13 Me zan ce miki?

Da me zan kwatanta ki, ya Urushalima?

Da me zan misalta wahalarki

Don in ta’azantar da ke, ya Sihiyona?

Masifar da ta same ki tana da fāɗi kamar teku,

Wa zai iya warkar da ke?

14 Annabawanki sun gano miki wahayan ƙarya,

Ba su tone asirin muguntarki,

Har da za a komo da ke daga bauta ba.

Amma suka yi miki annabcin ƙarya na banza.

15 Dukan masu wucewa suna yin miki tafin raini.

Suna yi wa Urushalima tsāki,

Suna kaɗa mata kai, suna cewa,

“Ai, Urushalima ke nan,

Birnin nan da ake cewa mai cikakken jamali,

Wanda ya ƙayatar da dukan duniya?”

16 Maƙiyanki duka sun wage bakinsu gāba da ke,

Suna tsāki, suna cizon bakinsu,

Suna ihu, suna cewa, “Mun hallaka ta!

Ai, wannan ita ce ranar da muke fata!

Ga shi kuwa, ta zo, mun gan ta!”

17 Ubangiji ya aikata abin da ya yi niyya,

Ya cika maganarsa wadda ya faɗa tun dā,

Ya hallakar, ba tausayi,

Ya sa maƙiyi ya yi murna a kanki,

Ya ƙarfafa ƙarfin maƙiyanki.

18 Ya Sihiyona, ki yi kuka ga Ubangiji,

Bari hawayenki su gudana dare da rana kamar ruwan rafi,

Kada ki huta, kada kuma idanunki su huta!

19 Ki tashi, ki ya ta kuka dukan dare,

Ki bulbule abin da yake cikin zuciyarki

Kamar ruwa gaban Ubangiji.

Ki miƙa hannuwanki zuwa gare shi,

Saboda rayukan ‘ya’yanki,

Waɗanda suke suma da yunwa

A magamin kowane titi!

20 Ya Ubangiji, ka duba, ka gani!

Wane ne ka yi wa haka?

Mata za su cinye ‘ya’yansu da suke reno?

Ko kuwa za a kashe firist da annabi

A cikin Haikalin Ubangiji?

21 Yara da tsofaffi suna kwance cikin ƙurar tituna,

An kashe ‘ya’yana, ‘yan mata da samari, da takobi.

Ka kashe su a ranar fushinka, ba tausayi.

22 Ka gayyato mini tsoro

Kamar yadda akan gayyato taro a ranar idi.

A ranar fushin Ubangiji

Ba wanda ya tsere, ko wanda ya tsira.

‘Ya’yan da na yi renonsu, na goye su,

Maƙiyina ya hallaka su.